Wa zai sayi amfanin gona a farashin gwamnati?

Yau sama da makonni biyu ke nan da Ma`aikatar Ayyukan Gona da Raya Karkara ta tarayya ta buga wata sanarwa a wasu Jaridun kasar nan, inda ta bayyana farashin wasu kayayyakin amfanin gona, makamantan hatsi da rogo, a zaman farashi mafi kankanta da ya kamata a saye su a kakar bana. Sanarwar ta ce, ‘Ma`aikatar, […]

Wa zai sayi amfanin gona a farashin gwamnati?
Wa zai sayi amfanin gona a farashin gwamnati?

Yau sama da makonni biyu ke nan da Ma`aikatar Ayyukan Gona da Raya Karkara ta tarayya ta buga wata sanarwa a wasu Jaridun kasar nan, inda ta bayyana farashin wasu kayayyakin amfanin gona, makamantan hatsi da rogo, a zaman farashi mafi kankanta da ya kamata a saye su a kakar bana. Sanarwar ta ce, ‘Ma`aikatar, bisa ga ajandarta ta inganta fannin ayyukan gona ya sanya ta yanke wannan farashin kamar haka:-
  Masara N55,000; Dawa N66,000; Gero N71,000; Waken Soya N100,000; Shinkafa sanfarera N65,000; Garin Kwaki N104,000, sai Ingantaccen Garin Rogo (irin wanda za a iya hadawa a yi burodi) N103,000. Dukkan wadannan farashi suna magana ne akan kowane tan daya na amfanin gonar, ko mu ce buhu goma, kowane mai nauyi kilo 100, tunda kilo 1,000 ke yin tan. Daga karshe sanarwar da Babbar Sakatariyar Ma`aikatar Misis Ibukun Odusote, ta sanyawa hannu, inda ta karkare da cewa an fadi wannan farashi ne a zaman karfafa wa manoman gwiwa, don haka sai ta yi fatan za su yi amfani da wannan dama wajen cin gajiyarta, sai dai kuma sanarwar ba ta bayyana wa zai sayi rarar amfanin gonar, ko ina-da-ina manoman za su kai amfanin gonarsu, don haka manoman suke ganin wannan sanarwa tamfar farfagandar da suka dade suna fama da ita daga Ma`aikatar akan inganta fannin ayyukan gona na kasar nan.
Ba ko shakka tallata wancan sanarwa a irin wannan lokaci wani abu ne da ka iya faranta ran musamman kananan manoma, bisa ga abubuwa biyu, ko abin da ya wuce haka. Na farko sanarwar ta zo adaidai lokacin da aka fara girbin wasu daga cikin kayayyakin amfanin gonar, kamar su masara da shinkafa da gero da rogo, hakan ka iya saita karamin manomi akan zai ci riba ko a`a.
Na biyu, samun hakan a irin wannan lokaci zai iya raba manoman da `yan ciko, wadanda kan sayi amfanin gonar da kaka akan farashin da manomi bai iya mayar da ko da abin da ya kashe ba, amma saboda yana bukatar kudi, ya sanya ala tilas ya kai amfanin gonarsa kasuwa ya sayar, ba tare da tunanin ya yi noman don riba ba, da dai sauran matsaloli na kananan manoma da suke da burin ganin shigowar kaka, musamma a daminar da ake ganin za ta yi harshe.
Yanzu babban kalubalen da ke gaban gwamnatin tarayya da ita kanta ma`aikatar gona ta tarayya bai wuce fayyace wa manoman ba yadda wannan sabon tsarin farashin amfanin gona zai yi aiki. Ma`ana, kamar yadda wasu manoman suka fara tambaya: Ina za su kai amfanin gonar tasu a saya bisa ga wancan farashi? Gwamnatin tarayya ce za ta shigo kasuwa kai tsaye ta sayi rarar amfanin gonar? Ko ta hannun gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi cinikin zai rinka fadawa? Bankunan kasuwanci ko na raya ayyukan gona za su saya? Ko attajirai da kungiyoyin jam`iyyun gama kai da kamfanoni da masana`antu masu sarrafa amfani gona za su shigo kasuwannani su sayi rarar amfanin gonar? Dukkan wadannan tammbayoyi da makamantansu suna matukar bukatar amsa daga Ministan Ayyukan Gona da Raya karkara na tarayya, tunda sanarwar ba ta fayyace haka ba, kamar yadda na fadi tun farkon wannan makala.
  Cikin biyu dole ka samu daya, ko dai ka kira bayyana farashin a zaman ganganci ko kuma aniyar da manoman kasar nan suka san gwamnatin tarayya da ita na kullum duk matakan da take dauka akan ayyukan gona, ba tana yi ba ne da aniyar kawo gyara ba, sai don ta karya fannin. Don kuwa koda a kasashen da suka ci gaba da gwamnatocinsu suke sanya farashin amfanin gona duk shekara, sukan yi haka ne, bisa ga ingantaccen tsarin da suke da shi na bayar da tallafi akan daukacin kayan amfanin gona, irin su taraktocin noma da iri da magani kwari da na ciyawa da takin zamani da bashi mai rahusa da tanadar kasuwa mai farashi kyakykyawa ga manomansu, amma mu nan batun ba haka yake ba.
Koda mai karatu ba manomi ba ne, ya sha jin irin yadda kungiyoyin manoman kasar nan da manoma daidaiku na kusan dukkan jihohin kasar nan kamar su Binuwai da Kano da Sakkwato da Katsina da Zamfara da Kaduna da Kabbi da sauransu a kowace shekara suke kokawa akan rashin samun wadatattu, kuma ingantattun iri da takin zamani da maganin kwari da ciyawa da tarantocin noma da bashi, da ma ita kanta kasuwar da za su sayar da amfanin gonarsu akan kari. Kamar yadda manoman shinkafa da alkama da tumatar da sauran amfanin gona na wadancan jihohi suka dade suna kokawa, duk kuwa da irin alkawarin roman bakan da Ma`aikatar Ayyukan gona da raya karkara da kamfanoni da masana`antun da suke sarrafa  amfani gona sukan yi masu na su noma irin wadancan amfani gona za su zo da kaka su saya, amma kakar na yi ba za su gansu ba.
Ina ga lokaci ya yi da Ministan Ayyukan gona na tarayya, Dokta Adewumi Adesina ya sake wata dibarar don kuwa a yanzu dai dukkan matakan da yake cewa suna dauka da aniyar farfado da ayyukan gona manoma ba su gani a kasa ba, Don haka ya zama wajibi ya gyara tsarin farfado da ayyukan gonar na GES, shirin da akarkashinsa ake raba wa manoman da suka yi rijista buhunnan takin zamani bi-biyu ta wayar hannu, takin da ba ya zuwa wajen wadanda Allah Ya sa suka samu, sai bayan bukatarsa ta wannan daminar ko noman rani ta wuce. Haka labarin yake akan iri da magunguna da saurn kayayyakin amfanin gona, bare kuma ka yi batun samun bashin kudi ko taraktocin  noma
   Gwamnatocin jihohi da na kananan hukumomi,  musamman na jihohin Arewa inda ake da kasar noma mai yalwa da yabanya mai kyau, su ma ya kamata su rungumi aikin gona gadan-gadan, don kuwa tuni masana sun sanar cewa noman nan dai shi ne makomar kasar nan da al`ummar ta, don kuwa man fetur da ake takama da shi zai kare. karewa ma da karau da me aka kafa harsashin tattalin arzikin kasar nan? Ai kowa ya sani da aikin gona ne.
                                                 

MARTANI AKAN MAkALAR MAKON JIYA
   A makalar makon jiha na samu martini daga Malam Sule Musa Dutse, wani tsohon dan Jarida da ya yi ritaya daga Gwamnatin Jihar Jigawa, a matsyinin Babban Jami`in yada labara a Ma`aikatar yada labaran jihar.
Alhaji Ado Saleh Kankiya. Na ga rubutunka akan Jigawa, kuma duk abubuwan da ka rubuta gaskiya ne. Ina shaida maka kafin kirkiro jihar shugabannin kananan Hukumomi uku daga 1979 zuwa 1989, su suka kassara Dutse, wajen hana `yan Dutse gina filayen Sabon garin Dutse da Alhaji Basiru Muhammadu Sanusi Galadiman Dutse ya raba, har da talakawa. A shirye Nike in kara maka bayani, har da sunayensu .
Sule Musa Dutse 08060743251