Wacce ake zargi da safarar mutane na cigiyar jaririyarta a hannun ’yan sanda

Matar da ake zargi da safarar yara a jihar Ogun, ta roki ‘yan sanda da su ba ta damar ganin jaririyarta ‘yar watanni tara a duniya.

Wacce ake zargi da safarar mutane na cigiyar jaririyarta a hannun ’yan sanda

Hannun jaririya

Matar da ake zargi da safarar yara a jihar Ogun, ta roki ‘yan sanda da su ba ta damar ganin jaririyarta ‘yar watanni tara a duniya.

An rawaito cewa an cafke matar ne yayin da take kokarin safarar wasu yara guda biyu zuwa kasashen ketare.

Sai dai wadda ake zargin ta ce “Ban san me ya faru ‘yan sanda suka dauke min jaririyata ‘yar watanni tara ba. Ban san ina suka kai min ita ba. Ina fama da ciwon kai, da ciwon mama.

“Sun yi min karya, ban yi safarar yaran domin karuwanci ba. Mijina Bakanike ne a kasar Libya. Ban taba yin safarar mutane ba.

“Wanda yake jan ragamar lamarin nan, ya dauke min yarinya ta, kuma ban san inda suka kai ta ba.

“Ina rokon gwamnati ta taimaka min saboda na ga jaririyata, bana jin dadi.

“Iyayen yaran sun ce ba sa bukatar ci gaba da tuhuma ta, amma ban san me yasa ‘yan sanda suka ci gaba da tsare ni ba,” a cewarta.

Wadda ake zargin ta yi wannan jawabi ne yayin da take ganawa da manema labarai a ranar Litinin.

Sai dai jami’an ‘yan sandan jihar, sun ce an kai jaririyar gidan marayu na Abeokuta ne kafin lokacin da za a kammala bincike a kan ta.

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro