Wacce ta yi takarar kujerar Shugabancin Faransa na da alaka da Putin – Bincike
A baya dai ta sha musanta hakan
Kwamitin Majalisar Dokokin Faransa ya gano jam’iyyar National Rally mai ra’ayin mazan jiya ta Marine Le Pen na da kusanci ta kut-da kut da gwamnatin Rasha.
Binciken, a cewar Sashen Hausa na Rediyon Faransa (RFI), ya kuma gano cewa Le Pen ta saukaka yada manofofin Kremlin.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 37 a kauyukan Sakkwato
- Ma’aikatan Lantarki za su shiga yajin aiki saboda cire tallafin man fetur
Marine Le Pen da jam’iyyarta ta RN sun sha musanta zargin alaka da Vladamir Putin, to sai dai rahoton kwamitin bincike na majalisar dokoki da ‘yan jarida suka samu tun kafin wallafa shi ya bankado fiye da abin da ake zargi tun farko.
Bayan kwashe sama da watanni shida na bincike kan korafe-korafe sama da 50, kwamitin majalisar ya gano cewa jam’iyyar National Rally (RN) wadda a da ake kira National Front, ta kasance tashar sadarwa ga gwamnatin, tare da goyon baya ga Moscow a mamayar da ta yi wa yankin Crimea.
Rahoton binciken da ake shirin wallafa a mako mai zuwa, a ranar Alhamis ya samu amincewa da kuri’u 11 kan biyar, matakin da ya fusata shugaban binciken kuma mai gabatar da kara, dan majalisar RN Jean-Philippe Tanguy, wanda ya yi watsi da tsarin da aka bi. (RFI Hausa)