Wace irin al’umma ce a Najeriya?

“Ba a sonmu, ba ma son kanmu, ba ma son mai sonmu, mun fi son mara sonmu, kamar an yi mana sammu???”Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya rubuta wa Shugaban kasa Jonathan wasika mai shafi 18, da ta bayyana zargin da yake yi wa Dokta Jonathan akan abin da yake faruwa, tun kafin su faru.Muna da […]

Wace irin al’umma ce a Najeriya?
Wace irin al’umma ce a Najeriya?

“Ba a sonmu, ba ma son kanmu, ba ma son mai sonmu, mun fi son mara sonmu, kamar an yi mana sammu???”
Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya rubuta wa Shugaban kasa Jonathan wasika mai shafi 18, da ta bayyana zargin da yake yi wa Dokta Jonathan akan abin da yake faruwa, tun kafin su faru.
Muna da tsofaffin shugabannin kasar nan su bakwai masu rai, har da shi  kansa Obasanjo, amma ba su dauki wani mataki akai ba, ga ‘yan majalisun tarayya masu ikon tsige shugaban kasa, ga malaman Jami’a da na addini da mawadata da sarakuna duk sun gani. Har yanzu ba su dauki wani mataki akai ba. Ga tsohon shugaban babban bankin Najeriya (CBN), Maimartaba Sarkin Kano,Muhammad Sunusi ll da ya bankado satar $49.8bn ya gagara sasantawa har aka fara dawo da wasu, saura $20bn. Maimakon a kama barayi a hukuntasu sai aka dakatar da shi, da ya bankado satar.
Yayin da kwamitin Faruk M. Lawal na majalisar tarayya da ya bankado satar #2.7tril na tallafin mai, aka bashi toshiyar baki ta $600,000. har yanzu yana majalisar ba a ko dakatar da shi ba, ba a kwato mana kudin namu ba. An mai da mu Arewawaye, saboda irin wawayen cikinmu, ‘yan Allah ya baku musamu, ba sa rokon Allah ya ba su, sai makiyan Allah, saboda mutuwar zuciya da bata. Sai ga shi a Ranar 15/7/2014 Jonathan da jam’iyyar PDP sun tsige Gwamnan Adamawa, Murtala Nyako na jam’iyyar APC, sannan shi ma takwaransa na Jihar Nassarawa sun kunno masa wuta.  To haka za a zuba ido tabbas? Abin Allah Ya kiyaye, ana kokarin mayar da Najeriya kamar kasar Kamaru, mabiya daban, mai mulki daban. Wadannan kadanne daga abubuwan da suka faru, ban da wadanda za su iya faruwa nan gaba. Allah ya tsaremu.
Duk wanda yayi imani shi dan Najeriya ne mai hakki a duk abin da Allah ya azurta Najeriya dashi, mai hankali, mara kwadayi, ya fito a hadu a gurfanar da Jonathan gaban shari’a, akai shi kotun duniya kafin zabe mai zuwa, na 2015. kamar inda tsohon Shugaba Rochard Nidon shi ne shugaban kasar Amurka na 37, ya yi murabus daga mukaminsa ne saboda majalisar dokoki ta shirya tsige shi, sakamakon umarnin da ya bayar na kai wa ofishin jam’iyyar adawa farmaki.
A karkashin dimokuradiyya babu inda a ka yarda shugaban kkasa ya yi amfani da kujerarsa domin cimma muradun kashin da kansa.
A na tsige irin wannan shugaban ne nan take. Idan kuwa ba a tsige shi ba, to gwamnatin ta zama ta kama-karya, ko da kuwa farar hula ne ke mulkar ta. Anya kuwa Shugaba Jonathan ya san da hakan. Jonathan ya yi amfani da ofishinsa ya aikata wadancan abubuwan, a ciki har da fada da gwamnonin jam’iyyun adawa, sannan uwa uba Shugaba Jonathan ne ya sauke Mai Shari’a Ayo Salami daga mukamin shugaban kotun daukaka kara, ba don komai ba sai saboda zai yi hukuncin da zai yi wa ’yan adawa dadi a kan zaben shugaban kasa.
*…Shin haka za mu kasance, mu ci gaba da zama ana yi mana mulki kama karya? ‘Yan Najeriya mu farko mu ceto kasar mu tunda dai
wadanda ke da ikon sauke sun zama ’yan amshin shata yanzu ko wadannan abubuwa ya kamata talakawa farar hula. Sai dai idan ba da gaske ake ba. Abin da ke faruwa a Najeriya lamari ne da ke bukatar aikin agaji na gaggawa; don haka shugaban kasa ne ya kamata ya tunkari gabaransa. Bai dace ya damka wa wani ragamar tafiyar da sha’anin tsaro a irin wannan lokaci ba. Wannan fa tamkar batu ne irin na asibiti. A lokacin da babu gagarumar matsala, likitoci suna iya wakilta jami’an jinya da sauran masu taimaka wa likitoci, ta hanyar ba su umarni. Amma a lokacin da a ke bukatar taimakon gaggawa, likitan ne da kansa yake shiga dakin tiyata ya dauki wukar fida. To, a nan ma wannan ne lokacin da ya kamata babban kwamandan askarawan Najeriya ya sanya kaki.
In ban da lallacewar shugabanci ana ta kashe-kashe a wasu yankuna na kasa a ce shugaba yaki zuwa, sannan aka sace ’yan matan makarantar sakandare sama da 200, shugaba bai gana da iyayen yaran ba, sai da wata matashiya ta taso daga Pakistan (Malala), ta ga shugaban kasa don lallacewa, sannan ya gana da su, wai yaji haushi, to su ba su ji haushi ba, sai kai da babu yarka a ciki? Allah ya kyauta. Ashe babu dadi. A kullum ’yan Najeriya da yawa ne ke mutuwa, amma abin takaici, shi ne, wadanda ke da alhakin maganta matsalar ba su san inda suka sa gaba ba. Anas Saminu ya rubuto makalarsa daga Kano.07033882307.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya