Wadaka da walawala
Kamfanin yamadidin duniya na Reuter, mai rututun labarai, ya yi tsokacin kan karfin tattalin dukiyar Haurobiya da jaddawalin kiyasi ya tabbatar da cewa ya sha gaban na Kudancin Ifrikiyya. Wadannan alkalumma na nuni da yadda hamshakai da jiga-jigan Haurobiya ke wadaka, su kuyma karke da yi wa gama-garin al’umma walwala. Dominn a nazarin karfin tattalin […]
Kamfanin yamadidin duniya na Reuter, mai rututun labarai, ya yi tsokacin kan karfin tattalin dukiyar Haurobiya da jaddawalin kiyasi ya tabbatar da cewa ya sha gaban na Kudancin Ifrikiyya. Wadannan alkalumma na nuni da yadda hamshakai da jiga-jigan Haurobiya ke wadaka, su kuyma karke da yi wa gama-garin al’umma walwala. Dominn a nazarin karfin tattalin dukiyar Haurobiya, Kamfanin rututuin labarai ya wassafa cewa akwai shakku, tunda akan yi la’akari da girman alala, wadda za ta ioya magance wa al’umma matsin lambar ’yar Gusau.
A farfajiyar wannan makaranta ta Dodorido da ke cikin Amintattar jaridar kasar Haurobiya, mun taba yin darasi kan “Tsimi da ta’adi, ga lukudi ga lakume kudi. Kai idan ba a ari faden Malam Mantau ba, za a fasko cewa, mun taba yin tsokaci kan “Kanwar kudi: Sinadarin buga Hauro.” Mun yi “Turmin dakan Hauro, inda muka fasko jirgin ‘Kwamandan Kalallamen Hauro,” tare da daukacin ’yan walawala da hana Haurobiyawa walawa.
Babban abin da nike son nusar da daukacin masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a wannan farfajiya, Shi ne, kasar Kudancin Ifrikiyya na karfin magawata dubu tsayuwa bisa kafa daya da zagaye na hasken lantarki, amma Haurobiya na burga da karfin magawata dubu kofar hanci. Kash! Allah wada naka ya lalace!
kasar Kudancin Ifrikiyya na cincirindon al’umma kusan malala gashin tunkiya babban lauje da zagaye; ita kuwa Haurobiya tana da dandazon mutane malala gashin tunkiya kimanin sili da kwanciyar magirbi da zagaye. Kuma yawan Haurobiyawa masu walagigi a kan tituna da laulayin gadin layi da zaman dirshan wajen kashe fatari, sun zarta na kudancin Ifrikiyya. Don haka karfin dukiyar Haurobiya da ake yamadidi da ita, cewa, ta kai Dalar Amurkawa gashin Balama Babban lauje da sili da zagaye, ni ina ganin ta yiwu ma ya zarta haka, duk da cewa manyan masana a fannin tsimi da tanadi sun soki lamirin jaddawali, bisa la’akari da cewa, ‘rayuwar gama-garin mutane ta gauraye da haure-haure da hauragiya, kuma mafi yawa na fama da talalar talauci.
Ni dai a matsayina na Babban direban alin wannan farfajiya, ina gajnin cewa, abin ya hana dukiyar Haurobiya yin tasirin kyautata rayuwar al’umma, shi ne, kwashi-kwaraf da dukiya, ta yadda ’yan tsirari ke wadaka, amma gama-garin al’umma an karke da yi musu walawala.
Lallai mu kara shirin nada dambe da jajircewa wajen asakala da jam’iyya mai danboto da sanda jirge, musamman a daidai lokacin da muke fama da tsaka mai wuya, inda Babban-rawa da shekararren mutumin Jihar Tumbin-giwa ke yunkurin cefanar da Arewatawa; uwa-uba, ga tsoho rasa kunya beran tanka ‘Tanko Ya-kasa.’ Tun kafin wadannan miyagu su karbi awalaja, ya kamata mu tabbatar da sun kwashi tutunsu a hannu. Da zarar mun yunkura, mun fatataki miyagun dawa, tabbas wata rana idan Kamfanin rututun labari ya tashi yin watsattsake kan al’amuran da ke wakana a kasar Haurobiya, zai rika nuna wa al’ummar duniya irin dabarun Harobiyawa na hana ’yan tsirari wadaka, har ta kai ga daukacin al’umma ta samu walwala.
Sakonnin makaranta
Martanin : Makekekiyar makiyayar Fullo
Mallam Dorido, barka da war haka. A gaskiya irin rubuce rubucen da kake yi da kuma irin akida ta tsana ga kabila da addini da kake yadawa ba tsari bane ko kadan. Ana kokarin hadan kan alumma amma kokari kake yi wajen wargaza ta. Gaskiya, akidar ka muguwa ce kuma ba irin ta ci gaba bace ba.
Gaskiya, ka yi tunanin zuci kamar mai hankali, ka daina irin wannan yade-yaden da ba za ta haifar da Al-kairi ba. Na gode. Bisssalam
Dabid Egbele Dabid Egbele [email protected] 08039382104
Tambaya
Assalamu alaikum. Shin an gayyaci Babban direban alli na makaranta zuwa taron sama wa Haurobiyawa makoma? Ko kuwa sai ‘yan bayan kango, da diyan amshin Mahadi mai dogon zamani? Duk dan dugwi dugwin da ya hana inna ai barci dai, masana yaren hau-hau wurin hawan sa, ba tare da sa-in-sa ba su ka ce; shi ma ba ya runtsa ba. Daga Ashiru danazumi Gwarzo.
Ta’aziyya
Innalillahi wa inna ilaihir Raji’un. Allah Ya yi wa mahaifiyar mataimakin Shugaban daliban Makarantar Dodorido na kasa, Abdullahi I. Abba rasuwa. Muna yi masa ta’aziyyata, Allah Ya rahamsheta, Ya kuma kyauta namu karshen. Ga lambar kurtun maganarsa: 08034182979 ga masu son yi masa ta’aziyya. Daga Bashir Ya’u (Uncle Bash).