Wadanda aka kwaso daga Afirka ta Tsakiya sun bayyana taskun da suka shiga
Yan Najeriya mazauna kasar Afirka ta Tsakiya da Gwamnatin Tarayya ta dawo da su sun bayyana irin taskun da suka shiga lokacin da rikicin kasar ya barke.Mutanen wadanda mafi yawansu mata ne da yara, sun ce mazajensu sun sadaukar da ransu wajen ganin sun kubuta da ransu inda aka kashe wasu daga cikinsu a lokacin […]

Yan Najeriya mazauna kasar Afirka ta Tsakiya da Gwamnatin Tarayya ta dawo da su sun bayyana irin taskun da suka shiga lokacin da rikicin kasar ya barke.
Mutanen wadanda mafi yawansu mata ne da yara, sun ce mazajensu sun sadaukar da ransu wajen ganin sun kubuta da ransu inda aka kashe wasu daga cikinsu a lokacin da ’yan tawayen Anti-Balaka, suka yi wa unguwannin Miskin da Sankilo da kuma Afo da Musulmi suka fi yawa kofar rago.
Malam Adamu Ibrahim wani dan asalin Jihar Bauchi da ya auri wata Bahaushiya haihuwar birnin Bangui, ya ce lokacin da ’yan Anti-Balaka suka isa unguwarsu ta Sankilo, ya je masallaci Sallar Magariba, da ya dawo gida sai ya samu an kone masa gida da na makwabta, kuma bai iske matarsa ba, har ya dawo Najeriya. “Mun bi sawu amma sai wani akwatin bindiga muka gani dauke da tuta da kudin Faransa da sauran alamu da ke nuna Faransa ce ta ba su shi,” inji shi.
Hajiya Fadimatu Yahaya ’yar asalin Jihar Borno da ta yi aure a kasar shekara da suka gabata, ta ce lokacin da ’yan tawayen Anti-Balaka suka shiga unguwarsu ta Miskin, mai unguwar ya yi kwalala inda maza suka fito suka yi musu garkuwa, sannan aka dauke mata a cikin mota zuwa ofishin Jakadancin Najeriya.
Ta yi zargin cewa sojojin Faransa na karbe makaman ’yan tawayen Saleka da ake ganin suna mara wa tsohon Shugaban kasar baya, a yayin da take kara karfafa na Anti-Balaka.
Maryam Bukar Talba, ’yar asalin Kano da aka haifa a can, ta ce an kashe mahaifinta da ’yan uwanta hudu, kuma ofishin Jakadancin Najeriya a kasar bai ba su ko ruwa ba bare shimfida, haka suka yi ta zaman takura har lokacin da Allah Ya yi dawowarsu.
Wata mai suna Halima Mohammed mai kimanin shekara 45 ta ce kafin rasuwar mahaifinta ya gaya mata shi mutumin Gezawa ne a Jihar Kano. “Mahaifina dan asalin garin Gezawa ne sai dai ban taba zuwa Najeriya ba, yanzu zan je can na nemi ‘yan uwan mahaifina,” inji ta.
Wani matashi mai suna Umar Hassan ya ce shi dai fatansa ya ga karshen yakin ya koma. “Duk da cewa da kyar muka sha, amma kullum addu’a nake yi Allah Ya kawo karshen yakin da ake yi a Bangui na koma, saboda yadda nake ganin Najeriya ba zan iya zama a nan ba saboda yanayin rayuwar akwai tsada ba kamar can ba” inji shi.
A cikin ’yan gudun hijirar akwai jariri mai kimanin wata daya da haihuwa wanda a yanzu haka kakarsa take rikonsa sakamakon kashe mahaifiyarsa da aka yi a lokacin yakin. Kakar jaririn, mai suna Maryam Ali ta shaida wa Aminiya cewa, “A lokacin da ‘yata ta ji zuwan ’yan tawayen gidansu sai ta nemi mijinta ya gudu. Kuma kafin su shigo dakinta ne ta yi sauri ta sanya jaririn a cikin kwando ta rufe shi da tsummokara. Sannan ta kira ni a waya ta shaida min abin da ke faruwa, ta gaya min inda ta boye jaririn. Sai dai lokacin da muka zo gidan tare da sojoji sai muka iske an yanka ta gunduwa-gunduwa,” inji ta.
Kimanin ‘yan asalin Jihar Kano 400 da yakin kasar Afirka ta Tsakiya ya rutsa da su suka sauka a Hukumar Hisba ta Jihar Kano a ranar Talatar makon jiya, bayan da Hukumar Bayar da Agaji ta Jihar Kano (SEMA) ta kwaso su daga Abuja.
Babban Sakataren Hukumar SEMA ta Jihar Kano Aliyu Bashir ya ce hukumarsu tana kokarin sada ’yan gudun hijirar fiye da 400 da danginsu. “Muna ba su duk taimako, idan mun gama tace su za mu hada su da ’yan uwansu. Yaran da ba mu samu iyayensu ba, za mu kai su gidan marayu, har zuwa lokacin da danginsu za su zo neman su,” inji shi.