Wadanda ke barin Kwankwasiyya burinsu su zama kamar ni – Rabi’u Kwankwaso 

Tun bayan da Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya samu a zaben 2019 ranar Litinin ake samun cacar baki tsakanin Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma Gwamna Ganduje. Ba wannan kadai ba, idan za a iya tunawa a jiya Alhamis ne Ganduje ya karbi tsohon shugaban jam’iyyar PDP […]

Wadanda ke barin Kwankwasiyya burinsu su zama kamar ni – Rabi’u Kwankwaso 

Tun bayan da Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya samu a zaben 2019 ranar Litinin ake samun cacar baki tsakanin Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma Gwamna Ganduje.

Ba wannan kadai ba, idan za a iya tunawa a jiya Alhamis ne Ganduje ya karbi tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Kano kuma jigo a darikar Kwankwasiyya, Rabi’u Sulaiman Bichi bayan ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki a jihar.

Yayin bikin karbar tasa, Gwamna Ganduje ya fadi abubuwa da dama a kan jagoran Kwankwasiyya wato tsohon gwamna kuma tsohon mai gidansa Rabi’u Kwankwaso, ciki har da cewa “Kwankwaso yana jin cewa babu wanda ya iya komai sai shi”.

A martanin da ya mayar a wata hira da wasu gidajen rediyo a Kano, Rabi’u Kwankwaso ya ce ai duk wadanda ma suke barin tafiyarsa ta siyasa burinsu shi ne “su zama kamar Rabi’u Kwankwaso”.

”Idan mafadin magana wawa ne ai majiyinta ba wawa ba ne,” in ji Kwankwaso, ya kara da cewa shi ne ya taimake su kuma “kila ma a kyautatawa daga iyayensu sai ni”.

A jawabinsa na ranar Alhamis, Gwamna Ganduje ya zargi Rabi’u Kwankwaso da cewa “ya kankane komai babu wanda yake taimakawa, hatta yawon kamfe da muka yi bai bayar da ko kwandalarsa ba”.

A martaninsa, shi kuma tsohon gwamnan cewa ya yi: “Ni burina a rayuwa duk wanda yake tare da ni tun daga kan dan aike si ne in daga shi ya zama babba (Chief Exectuive Officer).”

A karshe Kwankwaso ya nanata cewa ba shi ne ya haddasa rikicin da yake tsakaninsa da Ganduje ba sannan ya ce yana ci gaba da yin hakuri a matsayinsa na shugaba.