Wadanda suka kamu da Coronavirus a Najeriya sun kai 46

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta sanar da karin mutum biyu da suka kamu da cutar Coronavirus a safiyar yau Laraba, hakan ya sa aka samu adadin mutane 46 da suka kamu da cutar. An samu karin mutanen biyu ne a jihohin Legas da Osun. Hukumar NCDC ta fitar da sanarwar ne da […]

Wadanda suka kamu da Coronavirus a Najeriya sun kai 46

Ma’aunin cutar Kurona

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta sanar da karin mutum biyu da suka kamu da cutar Coronavirus a safiyar yau Laraba, hakan ya sa aka samu adadin mutane 46 da suka kamu da cutar.

An samu karin mutanen biyu ne a jihohin Legas da Osun.

Hukumar NCDC ta fitar da sanarwar ne da misalin karfe 07:00 na safiyar Laraba, inda suka tabbatar da mutum 46 suka kamu da cutar, biyu da suka kamu da cutar sun warke daya kuma ya rasu.