Wadanda suka kamu da Coronavirus a Najeriya sun zama 89

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta sanar da karin mutum takwas da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya. Wannan ya sa adadin mutanen da zuwa yanzu aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 89. An samu karin mutane bakwai a jihar Legas, hakan ya sa Legas ke da adadin […]

Wadanda suka kamu da Coronavirus a Najeriya sun zama 89

Kwalba dauke da Sanfurin gwajin Coronavirus

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta sanar da karin mutum takwas da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya.

Wannan ya sa adadin mutanen da zuwa yanzu aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 89.

An samu karin mutane bakwai a jihar Legas, hakan ya sa Legas ke da adadin mutum 59 da suka kamu da cutar a Najeriya kuma su ke da mafi yawan masu cutar a kasar. Sai kuma guda a Jihar Benuwe.

Hakan ya sa adadin mutanen da suka kamu da cutar a Najeriya ya kai 89.

Jerin jihohin Najeriya da cutar Coronavirus ta bulla  da kuma yawan mutanen da cutar ta kama:

Legas- 59

Abuja- 14

Ogun- 3

Enugu- 2

Ekiti- 1

Oyo- 3

Edo- 2

Bauchi- 2

Osun-1

Rivers-1

Benuwe- 1