Wadanda suka kashe matashi a Kaduna sun shiga hannu

’Yan Sanda a Jihar Kaduna sun kama matasa biyu da ake zargi da kashe wani matashi mai suna Aliyu Yusuf a makon shekaranjiya saboda budurwa. Ana zargin su ne da daba masa wuka a kafada a kofar makarantar Capital da ke titin Rabah a Malali, Kaduna, bayan sun samu sabani a kan wata budurwa mai […]

Wadanda suka kashe matashi a Kaduna sun shiga hannu
Wadanda suka kashe matashi a Kaduna sun shiga hannu

’Yan Sanda a Jihar Kaduna sun kama matasa biyu da ake zargi da kashe wani matashi mai suna Aliyu Yusuf a makon shekaranjiya saboda budurwa. Ana zargin su ne da daba masa wuka a kafada a kofar makarantar Capital da ke titin Rabah a Malali, Kaduna, bayan sun samu sabani a kan wata budurwa mai suna Lantana da ke Unguwar Badarawa.
Umar Abdullahi mai shekara 19 da ake zargi da daba wa marigayin wuka an kamo shi ne a Daura ta Jihar ýKatsina, kuma a lokacin ganawarsa da Aminiya a Hedikwatar ’Yan sandan Jihar Kaduna, ya ce ya daba wa Aliyu wuka ne lokacin da marigayin ya yi kokarin daba wa abokinsa wuka. “Mun je makarantar ce saboda shi da abokansa suna tsokanar abokinmu Yunusa wanda dan makarantar ne saboda suna neman budurwa daya, kuma mun je ne da nufin gargadinsu. Amma sai marigayin da abokansa suka fito da wukake, sai ya tunkari abokinaYunusa ya kai masa sara da ya kauce ni kuma sai na daba masa wuka a kafada. Gaskiya na yi kuskure, ina rokon iyayena da na marigayi Aliyu su yafe min domin ban ji dadin abin da na yi ba. A ce wai na kashe mutum saboda budurwa. Kuma ina kira ga ’yan uwana matasa mu rika tunani kafin daukar mataki saboda gudun yin da-na-sani,” inji shi.
Yunusa Umar ya ce lokacin da ya je gidan su Lantana ya gan ta da wayar hannu, bayan ya koma gida sai su marigayi Aliyu da abokansa suka zarge shi cewa wai yana yada labarin cewa Lantana ta saci waya. Har suka yi masa dukan tsiya shi kuma ya fada wa aboknsa. “Ban so wani ya mutu ba, kawai dai sun je da nufin a buge su ne kawai domin su daina tsokana ta,” inji shi.
Kakakin Rundunar DSP Zubairu Abubakar ya ce sun fara binciken lamarin kuma da zarar sun kammala za a tura wadanda ake zargin kotu.