Wadanda suka rasu a girgizar kasar Turkiyya da Syria za su kai 20,000 —Jami’an lafiya
WHO na fargabar mutanen da girgizar kasa ta kashe za su karu
Jami’an lafiya sun bayyana fargaba cewa za a iya samun mutum 20,00o da suka rasu a girgizar kasar da ta auku a kasashen Turkiyya da makwabciyarta Syria.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana fargabarta cewa alkaluman mutanen da suka rasu a girgizar kasar na iya karuwa a kan 4,890 da hukumomin kasashen suka sanar.
- Za a fara tseren duniya na farko a Najeriya a watan Afrilu
- NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Magance Matsalolin Harkar Kudi Ta Intanet
Kawo yanzu mutum 4,890 hukumomin kasashen suka tabbatar da rasuwarsu, baya ga rushewar gine-gine 5,600.
A safiyar Talata, hukumar agaji da jinkai ta Turkiyya (AFAD) ta ce mutum 3,381 suka rasu a kasar wanda ya kara adadin mamatan zuwa 4,890.
“Mun dauka tashin alkiyama ce ta zo; ba mu taba ganin abu irin haka ba,” in ji wata matashiyar ’yar jarida, Melisa Salman, mai shekara.
Duk da tsananin hunturu, masu aikin ceto sun kwana sun wayi garin Talata suna amfani da hannayensu wajen hako mutane da kuma gawarwakin da suka makale a baraguzan benaye da sauran gine-ginen da suka rushe a girgizar kasar ta ranar Litinin a.
Kasahehen duniya dai sun kasu da girgizar kasar mai karfin 7.8 da kuma irin barnar da ta yi, inda suke rige-rigen yin ta’aziyya da kuma kai tallafi ga kasashen biyu.
A halin da ake ciki, ana ci gaba da aikin ceto a sassan kasashen Turkiyya inda dubban daruruwan ’yan Syria ke zaman gudun hijira, baya ga wanda ake yi a can Syria.
A halin yanzu, ana fama da tsananin hunturu inda sanyi ya kai maki kasa da 0 na ma’unin yanayi, lamarin da ya sa kasashe ke kara tausayawa da kuma alkawarin bayar da agaji ga kasashen biyu.
Turkiyya na daga cikin kasashen da ke yawan samun girgizar kasa, inda a 1939 aka samu mai karfin maki 7.8 wanda ya yi ajalin muutm 33,000 a yankin Gabashin Lardin Erzincan.
A 1999 aka samu mai karfin maki 7.4 a yankin Duzce, wanda ya kashe mutum sama da 17,000.
Masana sun sha yin gargadi cewa girgizar kasa na iya aukuwa a birnin Santabul, babban birnin kasar da ke da mazauna sama da miliyan 16 da ke zaune a gidaje da ke matsaloli a yanayin gininsu.