Wadanne matasa ne za su amfana da tallafi, har yaushe?
Yanzu dai ta tabbata gwamnatin tarayya ta jam`iyyar APC, ta amince daga watan Janairun sabuwar shekara mai zuwa in Allah Ya kaimu za ta fara rabon tallafin Naira dubu biyar-biyar ga wasu matasan kasar nan miliyan 25, da ba su da ayyukan yi, a zaman cika alkawarin yakin neman zaben da dan takarar neman shugabancin […]
Yanzu dai ta tabbata gwamnatin tarayya ta jam`iyyar APC, ta amince daga watan Janairun sabuwar shekara mai zuwa in Allah Ya kaimu za ta fara rabon tallafin Naira dubu biyar-biyar ga wasu matasan kasar nan miliyan 25, da ba su da ayyukan yi, a zaman cika alkawarin yakin neman zaben da dan takarar neman shugabancin kasa a jam`iyyar, kuma a yau shugaban kasar nan, Muhammadu Buhari ya yi wa matasan. Makasudin yin wannan alkawari da yunkurin cika shin bai rasa nasaba da irin halin rashin ayyukan yi da akasarin matasan kasar nan suke ciki, rashin ayyukan da suke kawo zaman kashe wando tsakanin matasan da ma fadawa cikin ayyukan ta`addanci, irin su rikice-rikicen `yan tada kayar baya da fashi da makami da garkuwa da mutane don neman kudin fansa da fasa bututu don satar man fetur da dangogin ayyukan ta`addanci da suka zama ruwan dare a cikin kasa.
Duk da jam`iyyar ta APC, alkawari ta yi na za ta bayar da wadannan kudi a zaman tallafi, amma bayar da kudin ba su tabbata ba sai da babbar jam`iyyar adawa ta PDP, ta rinka kiraye-kirayen lallai sai gwamnatin APC ta yunkura ta cika alkawarin da ta dauka din. Ba wai daga jam`iyyar adawa ta PDP aka rinka samu wannan matsin lamba ba, hatta daga cikin jam`iyyar ta APC, wasu daga cikin jiga-jiganta da suka hada da uwargidan shugaban kasa Hajiya A`isha Buhari, ita ma ta bi sawu cikin kiran jam`iyyar tasu ta APC da ta gaggauta cika wannan alkawari.
Ba da tallafin kudi irin wannan, ba wani sabon labari ba ne a kasashen da suka ci gaba ga marasa ayyukan yi ko marasa galihu ko gajiyayyu da makamantansu, tallafi irin wannan da kasashen da suka ci gaban sukan yi, yana da ka`idoji da sharudda. Alal misali, wanda ba ya da aiki, da zarar ya samu aiki za a zare sunansa, sannan shi ma ya ci gaba da tallafa wa wasu daga irin kudin harajin da zai rinka biyan hukuma a zamansa na ma`aikaci. Dadin-dadawa, babu wani batu na la`akari da ra`ayin siyasar mabukacin ba, illa dai kawai mabukaci ne da ya rasa madafar a rayuwa, don gudun shi kansa ko shi da iyalinsa su fada cikin wani mawuyacin halin rayuwa. To, hukumomi suke daukar nauyinsa, har ranar da ya samu aiki da taimakon hukumomi, ko kuma har ranar da ya ka koma ga Mahaliccinsa, idan ba wanda zai iya yin aiki ba ne har abada.
Akasarin kasashen duniya da suka ci gaba da suke wannan shiri na ba da tallafin kudi ga marasa galihunsu za ka tarar tuni suka tsallake siradin kalubalen rashin abubuwan more jin dadin rayuwa ga mutanensu, irin su wutar lantarki ko rashin ingantattun hanyoyin kiwon lafiya da ilmi, balle ruwan sha, ko man fetur. Babban abin la`akari kamar yadda na fadi a sama, duk wanda ya wadata ba ya kara sha`awar a ce sunansa na cikin masu samun tallafin. Don haka batun wanda zai amfana da wanda yake bai cancanta, bai zama wata matsala ga mahukuntan irin wadancan kasashe, suna yin komai a kan gaskiya da gaskiya.
Koda yake wannan shi ne karon farko da gwmnatin tarayya a cikin wannan mulkin na dimokuradiyya da aka kai yau shekaru kusan 17, ta yunkura da sunan za ta fara biyan kudin tallafi ga wasu matasa miliyan 25, amma dama gwamnatocin jihohi irin su Imo da Kebbi da Sakkwato da Nassarawa da Zamfara da Jigawa tuni suke biyan kudin tallafi da suka kama daga N7,000 zuwa abin da ya yi sama duk wata ga wasu nakasassu, sai dai kuma kash! Ba lallai ba ne nakasassun da suka cancanta din su mahukuntan wadancan jihohi suke ba kudin tallafin, kuma ba a la`akari da ra`ayin siyasa.
Yanzu, bari mu duba kudin tallafin da gwamnatin tarayyar ta ce za ta fara rabawa ga matasan kamar yadda Ministan Al`amurran Wasanni da Matasa, Barista Solomon Dlong ya tabbatar a kwanakin baya. Aniyar babban burin da gwamnatin tarayya take so wannan shiri ya cimmawa a tsakanin matasan kasar nan dai, bai wuce yadda za ta rage yawan zaman kashe wandon a tsakanin matasan, wanda kan haddasa yin amfani da su wajen aikata ayyukan ta`addanci da makamantan miyagun ayyuka, kamar yadda na ambata a sama.
Kafin in yi magana a kan yawan makudan kudin da wannan shiri zai rinka lakumewa, walau a wata ko a shekara, ya kamata in yi tambaya ga Minista Barista Dalong a kan irin matakan da zai yi amfani da su wajen zabo wadannan matasa miliyan 25? Abin da ya sa na yi wannan tambaya, bai wuce irin kididdigar da ake bayarwa ba, na cewa kashi 60 cikin 100, na yawan mutanen kasar nan miliyan 170, wato miliyan 102, ke nan matasa ne, wadanda kusan rabin su, wato miliyan 51, ba su da ayyukan yi, walau wadanda suka yi karatun boko, ko wadanda ba su yi ba. Mai karatu ka ga a nan akwai bukatar kamanta gaskiya da adalci, wajen tabbatar da cewa masu tsananin bukatar tallafin kadai za su amfana da shi, ba masu uwa a gindin murhun wannan gwamnatin ba, kamar yadda aka saba a kasar nan wajen rabon duk wani abu na gwamnati, sai ka tarar ana kara wa mai karfi karfi, talakawa kuwa suna ta ci gaba da rayuwa a cikin bakar wahala.
Shirin tallafin Naira dubu biyar-biyar (N5,000), shiri ne a bisa kididdiga zai rika lakume Naira Biliyan 125, duk wata, yayin da ashekara zai rika lashe Naira tiriliyan 1.5 a shekaru hudu na wa`adin zangon farko na wannan gwamntin zai lashe kusan Naira tiriliyan 6. Idan aka duba yawan wadannan kudi wasu na da ra`ayin cewa makudai ne, wasu kuma na cewa ba su takakara suka karya ba ga gwamnatin tarayya da a karon farko cikin tarihin kasar nan gwamnatin APC ta ba da shelar za ta yi kasafin kudin N tiriliyan 8 a shekara mai zuwa, 2016, kusan ninki biyu na wannan shekarar ta 2015, da APC din ta gada daga gwamnatin PDP.
Masu iya magana kan ce, ‘da ka ba mutum kifi gara ka koya masa yadda zai kama kifin,’ masu wannan ra`ayi suna ganin tun da dai yanzu a bayyane take tattalin arzikin kasar nan kusan ya dogara ne kacokan akan kudin shiga daga man fetur, man fetur din da yanzu farashinsa ya fadi kasa warwas, babu kuma alamar zai farfado, to kamata ya yi gwamnatin tarayyar ta mayar da hankali wajen kashe dan dari da kwabon da ta ka samu wajen ganin ta farfado da ayyukan noma da kiwo da kuma ganin ingantuwar wutar lantarki, fannoni biyun da su kadai za su iya jibantar matsalolin rashin ayyukan yi da musamman matasan kasar nan suke fama da shi, maimakon rabon tallafin kudaden da ba za su kashewa matasan kishirwarsu ba, ta talauci.