Wadansu daga cikin ‘yan gudun hijran

Dokta Yakubu Mai Gida Kachako, shi ne mataimakin Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano.  Kuma Shugaban Cibiyar Binciken Magungunan  Musulunci da Fadakarwa ta Kachako wadda take birnin Kano. Har ila yau, yana tare da sashen nazarin magunguna na Jami’ar Bayero ta Kano a bangaren kwamitin bincike a kan magungunan kasar Hausa.  A wannan tattaunawar da […]

Wadansu daga cikin ‘yan gudun hijran

Dokta Yakubu Mai Gida Kachako, shi ne mataimakin Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano.  Kuma Shugaban Cibiyar Binciken Magungunan  Musulunci da Fadakarwa ta Kachako wadda take birnin Kano. Har ila yau, yana tare da sashen nazarin magunguna na Jami’ar Bayero ta Kano a bangaren kwamitin bincike a kan magungunan kasar Hausa.  A wannan tattaunawar da ya yi da Aminiya kwanakin baya a Kaduna, ya yi tsokaci kan yadda za a kawar da matsalar shaye-shayen abubuwan da ke sanya maye a cikin al’umma. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Me ye girman matsalar shaye-shayen kayan maye a halin yanzu?
Dokta Yakubu: To ai yanzu matsalar shaye-shaye ta zama ruwan dare game duniya. Ba wata al’umma a duniya da za ka ce ba a shaye-shaye a cikinta. Bincike ya tabbatar da cewa ba wanda zai ce ma ga lokacin da aka fara shan miyadun kwayoyi a duniya, ba wanda ya san lokacin. Domin ana cewa a iya abin da aka sani na kusa-kusa, an fara shaye-shaye kwayoyi kimanin shekara dubu biyar da suka wuce kafin haihuwar Annabi Isa (AS). Domin haka kowace kasa tana kokari iya nata yadda za ta shawo kan matsalar. Sai kowa ya shigo ciki, malamai su shigo ciki, ’yan kasuwa su shigo ciki, wanda yake kowane addini ma ba ya son shaye-shaye. Idan ka duba addinin Kirista yaki yake da shi, addinin Musulunci shi ma yaki yake da matsalar. Kuma sannan al’ummar mu da Hausawa da wadanda ba Hausawa ba da kowace kabila, ba wanda ya bari. Saboda haka ashe cuta ce ta addabi kowa a duniya. Tana bukatar sai kowa ya zo ya ba da gudummuwarsa. Yanzu wani abu da zai ba ka mamaki mace a gidanta ba a barta ba, yarinya a gida a gaban iyayenta an koya mata shaye-shaye. Yara ’yan makarantar firamare da sakandare suna shaye-shaye. Su za su zama shugabanni gobe. Matsalar ita ce duk san da aka ce jami’in tsaro, wanda zai kula da lafiyar masu hankali, ya sha abin da zai gusar masa da hankali, to ka ga akwai babban tashin hankali.

Aminiya: Wace gudunmuwa iyaye za su iya bayarwa wajen yaki da matsalar?
Dokta Yakubu: Abu na farko shi ne ta fuskar tarbiyya. Su dage wajen tarbiyyar ’ya’yansu, wato su bai wa ’ya’yansu tarbiyyar da ta dace da shari’a. Ita mahaifiyar ta guji cin haram, mijinta ya guji cin haram shi ma. Domin an ce duk mutumin da ya ci haram loma guda, sai ya yi kwana 40 yana addu’a Allah bai karbi addu’arsa ba. Kuma matukar mutum zai ci haram ya samar da cikin dansa ko ’yarsa, ko uwar ta yi abu na rashin da’a lokacin goyon ciki, to sai abin da za a haifa ya gada. Ka ga ke nan akwai bukatar natsuwa da zaman lafiya da gudun abin da zai kawo lalacewar tarbiyya. Sannan idan aure za a yi, tun daga zabar mace, a zabi macen da take da tarbiyya kuma ta fito daga gidan tarbiyya. Sannan a yi neman auren bisa ka’ida ta addini, wanda ba za a kula juna ba, ba za a nuna abin nan ba. Sannan idan an yi auren wajen kusantar juna a tabbatar an yi hakan bisa ka’idar shari’a.  Wajibi ne sai an bi wadannan .
Sannan a wajen nakuda, zuwan yaro duniya shi ma a kula sosai. A lokacin da da yake zuwa duniya wani irin yanayi ne ake shiga. Aljanu suna zuwa karbar haihuwa saboda haka abin da ake so a kori aljanu ya zama mala’iku ne a wurin.

Aminiya: Ta wace hanya za a kori aljanun?
Dokta Yakubu:  Ta hanyar karanta ayoyin Al-kur’ani.  Lokacin da Fatima diyar Manzon Allah (SAW) ta zo haihuwa, sai ya tashi wasu mata biyu, ya ce ku je ku taimake ta. Da suka shiga dakin sai suka fara karanta Fatiha, suka karanta ayoyi da suke cikin Suratul A’raf, aya ta 54 zuwa ta 56, suka karanta Falaki da Nasi shi ke nan. Sai malamai suka ce ashe wannan ayoyin su ake so a karanta a dakin mai haihuwa.  Su ne ake so mace mai nakuda ta ji, ko ta karanta da kanta ko mijinta ya karanta mata. Ko kuma mai karbar haihuwar ta karanta,  ko ma’aikatar karbar haihuwar su karanta. Ko da a kaset, ko a waya aka sanya ya wadatar. Abin da aka fi so ke nan.  
Bayan haka, a bayar da kyakkyawar yanayi na zuwan da duniya. Idan ya zo ya fara jin ambaton Allah a kunnensa. Domin ya zo a cikin hadisin Buhari, babu dan  da za a haifa ya zo duniya face Shaidan ya shafe shi. A wata ruwaya sai aka ce, sai Shaidan ya cika masa dan yatsa a kubinsa. Sai aka ce amma ban da Maryam da  danta Annabi Isa (AS), su kadai ne Shaidan bai iya samu ya yi musu wannan ba. Sai malamai suka ce mai ya sa bai samu dama ba, aka ce lokacin da Shaidan ya zo zai soke shi bayan ta haife shi, sai ta dauke shi ta sanya shi a cikin mayafi ta lullube shi. Tana lullube shi da ya zo sai ya soke wannan mayafin, maimakon ya soke jikin yaron.  To shi ya sa, malamai suka ce daga an haifi jinjiri ana yanke masa cibiya a yi maza-maza a lullube shi.
Har ila yau, a kula lokacin da mace take nakuda kada a rika yin yawan surutu da maganganu wadanda suke marasa kyau. Saboda wani yanayi ne mai ban mamaki. Bugu da kari, yana da kyau a lura da zamanta lokacin da za ta haihun, ana so ta haihu a durkushe idan da hali. Saboda siffarta ta ba da Allahu.  Ka ga ta haihu a cikin sunan Allah ke nan.  Ana so a tsara masa tarbiyya, a kula da kiwon lafiyarsa.  A duba launin fatarsa, idan lafiyarsa lau, za a ganta ta yi launin rawaya. Daga nan sai yi masa huduba a kunnensa na dama da dai sauran tanade-tanaden da shari’a ta yi.  Har ila yau, an so idan za ta shayar da yaron ta yi alwala.

Aminiya:  Wace gudunmuwa gwamnati za ta bayar wajen magance matsalar shaye-shayen?
Dokta Yakubu:  Na farko dai ta bulo da hanyoyin samar da ayyukan yi. A gina cibiyoyin gyara tarbiyyar matasan da suka fada cikin matsalar.  Kamar yadda gwamnatin Jihar Kano ta samar da wannan.  A ce wata makaranta ce ta mashaya da aka yi, a samar da magunguna da abinci da kulawa da komai. Har ila yau, a tabbatar da an koya musu wata sana’a kafin su fito. To za ka ga an rage yawan masu shaye-shaye da yawa.

Aminiya: Kamar bangaren malamai fa?
Dokta Yakubu: Su ma malamai su  ci gaba da fadakar da dalibai. A fito da abubuwa a fili da nuna musu illolin hakan. Misali akwai wani taron lacca da muka yi a Kano, sai da na sanya aka nemo mini kaza da kuma giya. Da aka yanka kazar, sai na  aka dauko hantarta aka sanya a cikin giyar, aka rufe. Bayan dan wani lokaci, sai hantar ta zuke giyar, ta dawo fara sal bayan ta kumbura. Sai na ce a duba a gani wannan fa rana guda ke nan, ya zai kasance idan mutum ya kwashe shekaru yana shaye-shayen. Matsalar ta shafi kowa dole sai kowa ya taimaka wajen yaki da matsalar.

Aminiya: Ko ka taba rubuta wani littafi dangane da wannan matsalar?
Dokta Yabubu:  Akwai guda mai suna: Illolin Kayan Sa Maye Ga Rayuwar Matasa.