Wadansu manyan Arewa ba sa kaunar Buhari – Rabaran Maina

Rabaran Joshua Ray Maina shi ne shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) reshen Jihar Bauchi a tattaunawarsu da wakilinmu ya ce nan da watanni biyu kungiyar zata kai gudunmawar kayayyakin abinci jihar Borno domin tallafawa wadanda suke cikin mawuyacin hali a jihar ta Borno: Ko akwai wani shiri da kuke yi don tallafa wa mutanen […]

Wadansu manyan Arewa ba sa kaunar Buhari – Rabaran Maina
Wadansu manyan Arewa ba sa kaunar Buhari – Rabaran Maina

Rabaran Joshua Ray Maina shi ne shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) reshen Jihar Bauchi a tattaunawarsu da wakilinmu ya ce nan da watanni biyu kungiyar zata kai gudunmawar kayayyakin abinci jihar Borno domin tallafawa wadanda suke cikin mawuyacin hali a jihar ta Borno:

Ko akwai wani shiri da kuke yi don tallafa wa mutanen da tashin hankalin Boko Haram ya fi shafa?
Har zuwa wannan lokaci da muke zantawa da kai al’umma suna ci gaba da kawo mana gudunmawar kayan abinci da kudi domin tallafa wa mutanen Jihar Borno da sauransu. Nan ba da jimawa ba tawagar kungiyar (CAN) reshen Jihar Bauchi za mu tashi zuwa Jihar Borno domin kai musu kayayyakin tallafi. Daga cikin kayayyakin da za mu kai musu akwai shinkafa da man girki da suturu da makamantansu.
Wannan gudunmawar da za mu kai ba Kiristoci ba ne kadai za su amfana har da Musulmi ’yan uwanmu za su amfana. Daga nan kuma za mu kai wani tallafin ga mutanen garin mubi da ke cikin wani mawuyacin hali. Idan Allah Ya sa muka samu kudi kafin lokacin wadanda suke fama da rashin lafiya za mu ba su wani abu domin su sayi magani. Kuma za a gudanar da wannan aiki ne a karkashin jagorancin shugabannin gudanarwa na kungiyar (CAN) na Jihar Bauchi.

Mene ne ra’ayinka game da sulhun da gwamnati take yi da kungiyar Boko Haram?
Ya kamata ka fahimci cewa siyasa ta shiga cikin wannan batu na kungiyar Boko Haram kuma ina tabbatar maka cewa ’yan siyasa ne suke ruruta wutar fitinar Boko Haram domin cimma muradunsu. Da dan Jam’iyyar PDP da dan Jam’iyyar APC dukkansu bakinsu daya ne, da yawa daga cikin ’yan Jam’iyyar APC sun fito ne daga PDP wannan shi ne maganar gaskiya. Wai shin me ya sa babu rikicin Boko Haram a Jihar Sakkwato ne saboda haka kullum ina fada cewa ba mu da dattawa a Arewa da za su fito su fadi gaskiya komai dacinta.

Mene ne ra’ayinka game da ’yan takarar shugabancin kasa na Jam’iyyar APC?
Ko mutum ya yarda ko kada ya yarda addini ya shiga cikin siyasar Najeriya, daya daga cikin matsalolinmu shi ne dole a bambanta siyasa da addini. Kuma ya kamata ka fahimci cewa Janar Buhari a lokacin mulkinsa mutane sun sha bakar wahala, Buhari ya daure sarakuna kuma babu wanda ya tsira a lokacin mulkinsa. Amma a fahimtata zan iya cewa talakawa ne kawai suke kaunarsa masu kudin Arewa ko Musulmi ko Kirista ba sa kaunar Buhari. Kiristocin Najeriya ba su da wata matsala da Buhari babbar matsalarsa ita ce mutanen Arewa, manyan Arewa ne. A nawa ra’ayin ya kamata Buhari ya hakura da tsayawa takara ya jawo wani matashi ya mara masa baya, domin ita ce hanya daya tilo da ta kamata a bi a tawa fahimtar. Akwai wadanda suke ganin idan ba su ba, sai dai a fasa kowa ya rasa a dandalin siyasar Najeriya wannan kuma kuskure ne.
Don haka Janar Muhammadu Buhari ya janye takararsa domin akwai gwamnoni da sarakunan gargajiya da ba sa kaunarsa da manyan ’yan kasuwa, a baki suna sonsa amma a zuciyarsu ba sa kaunarsa ko kadan. Idan Buhari ya yi nasara azzalumai za su sha wahala amma talaka rayuwarsa za ta inganta.
Idan kuma ka dubi Atiku Abubakar ya yi Mataimakin Shugaban kasa na tsawon shekara takwas babu abin da ya tsinana wa jiharsa ta Adamawa hanyar garinsu ya gagara sa baki a gyara hanyar Adamawa ita ce hanya mafi muni a Najeriya, kauyenmu da ba kwalta ya fi hanyar Yola kyau. Aikin da tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu ya yi ya fi aikin da Atiku ya yi a matsayinsa na Mataimakin Shugaban kasa.
Sannan babbar matsalar da Shugaba Jonathan yake fuskanta a cikin gwamnatinsa ita ce bai san Najeriya ba.Ya san tsarin mutanen Kudancin kasar nan amma bai san tsarin ’yan Arewa ba.

A karshe mene ne sakonka ga ’yan Najeriya?
Kamar yadda na fada maka a baya har gobe ba na tare da masu cewa gwamnati ce take ruruta wutar fitinar Boko Haram. Babban sakona ga al’umma shi ne ya kamata idan mutum zai yi magana ya yi adalci ga kowa. Kuma duk wanda yake ganin abubuwan da nake fada ba gaskiya ne yana da ikon maida martani.