WADATA kASA DA ABINCI Jagora Ga Manoma Don Samar Da Abinci Ga kasa Yadda Najeriya za ta wadata kanta da shinkata – Dokta Okuku

Dokta Innocent Okuku shi ne Shugaban sashen kasuwanci na Kamfanin Sarrafa Sinadarai na Notore. A wannan hirar da aka yi da shi ya bayyana yadda Najeriya za ta wadata kanta da shinkafa, inda ya yi nuni da cewa dole a jajirce wajen nomanta a cikin gida, don haka yake ganin hana shigo da ita shi […]

WADATA kASA DA ABINCI Jagora Ga Manoma Don Samar Da Abinci Ga kasa Yadda Najeriya za ta wadata kanta da shinkata – Dokta Okuku
WADATA kASA DA ABINCI Jagora Ga Manoma Don Samar Da Abinci Ga kasa Yadda Najeriya za ta wadata kanta da shinkata – Dokta Okuku

Dokta Innocent Okuku shi ne Shugaban sashen kasuwanci na Kamfanin Sarrafa Sinadarai na Notore. A wannan hirar da aka yi da shi ya bayyana yadda Najeriya za ta wadata kanta da shinkafa, inda ya yi nuni da cewa dole a jajirce wajen nomanta a cikin gida, don haka yake ganin hana shigo da ita shi ne matakin farko da zai sanya a yi kwazon cimma wannan manufa. Ga yadda hirar ta kasance:

 

Shinkafa abinci ne da ake amfani da shi a nan. Ko me ya sa har yanzu muke shigo da shinkafar da muke ci?
A matsayin kasa, ba ma samar da isassar shinkafar da muke bukata. Saboda haka muke shigo da ita don cike gibin abin da muka rasa. kididdiga ta nuna cewa muna samar kimanin ton miliyan uku na shinkafa, alhali abin da muke ya kai ton miliyan biyar. A hakikanin gaskiya ma, alkaluman kididdigar da aka fitar na baya-bayan nan daga Ma’aikatar Gona ta Tarayya na nuni da cewa muna da gibin ton miliyan guda da dubu 900 na shinkafa. Shi yasa idan ana son cike wannan gibin, dole sai mun shigo da abin da zai maye gurbin abin da ya yi mana karanci. Kuma ga shi mun fi son shinkafa gyararra. Mafi yawan shinkafar da ake nomawa a gida ba mai tsawo ba ce ba.
Wacce irin dabara ake amfani da ita wajen noman shinkafa a kasar Thailand da sauran kasashen nahiyar Asiya, har ta kai sun zama masu fitar da shinkafa waje?
Akwai wadansu muhimman al’amura da ke tatttare da dabarsu ta noman shinkafa, har ta kai ga suna samar da fiye da bukatarsu. Na farko sun bayar da fifikon noman a irin yanayin muhallin da ya dace da noman shinkafa. Ko kuma a ce a wuraren da ruwa ke kwance, wanda ke taimaka wa noman shinkafa a kwari, ba za ka noma kowane irin hatsi ba; kawai ka mayar da hankali a kan shinkafa kawaio. Na biyunsu, shi ne, suna noman shinkafar ne a daukacin shekara (rani da damina). Bas a yin noman irin yadda muke yi a nan. Mun dogara ne kacokam ga saukar ruwan sama, sannan muna yin noman ne sau daya (a shekara). Lokacin damin takaitacce ne, inda bay a wuce watanni biyar a wasu wuraren. Shi ya sa muke yin asara a sauran watanni bakwai. Idan har za ka iya noma hatsi da za ka iya cin gajiyarsa a tsawon wata uku da rani, to za ka iya yin irin wannan noman sua uku a shekara ke nan.
Ta yaya za mu iya kai ga gaci, ba ma wadatuwa da shinkafar da muka noma ba, har ma mu rika fitar da ita waje?
Da farko dai mu yi la’akari da kwarewa, saboda akwai abin da ake kira ‘fifikon samun dama’ a wajen noman hatsi. Za ka iya samun wurin noma da ya dace da hatsi, sai ka mayar da wurin wajen noma irin wannan tsiron.
Najeriya na da damar yin noman shinkafa. Alal misali a bara kididdiga ta nuna cewa, Jihar Kebbbi ta samar da shinkafar da ta noman a kan hekta fiye da dubu 100. Wannan al’amari ne mai ban sha’awa. An kiyasta cewa fiye da ton miliyan daya na shinkafa aka samu a Jihar Kebbi a bara, ta hanyar shirin bayar da tallafin bashin noma na Babban Bankin Najeriya. Sannan akwai kimanin jihohi 11a kasar nan da ke da dimbin albarkatun wurin noman shinkafa. Sai ka dauki wadannan wurare da ke jihohin da za a iya noma shinkafa, a mayar da hankali kacokam kan noman shinkafa kurum. A rinka yinta damina da rani. Wannan na nuni da cewa akwai bukatar mu kara fadada noman raninmu. Idan muka noma shinkafa sau biyu a shekara, Najeriya za ta samu isasshiyar shinkafar da al’umma ke bukatar su ci. Dubi cewa an samu ton miliyan daya na shinkafa daga Kebbi a noman, kuma a samu ton miliyan biyu da damina, ka ga kana maganar ton miliyan uku ke nan daga jiha daya. Idan ka sarrafa ton miliyan uku, za ka iya samun shinkafar da aka sarrafa, aka alkinta (a buhu) kimanin ton miliyan biyu zuwa biyu da rabi. Ka ga ke nan an samar da rabin bukatar abin da zai ciyar da Najeriya. Akwai Adamawa da Taraba da Kano da Jigawa da Binuwai da Ebonyi da Kuros Ribas da Anambara da sauransu. Wadannan jihohi suna fadin kasar da za a iya noma shinkafa.
Ka ga ke nan idan har muka samar da abin da ake bukatar don noman shinkafa, za a samar da rubin abin da muke a shekara a wadannan jihohi, ta haka za mu shawo kan kalubalen gibin karancin shinkafa da ake fama da shi a Najeriya.
Wacce gudunmuwa gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu za su iya bayarwa wajen cimma wannan manufa?
Akwai dimbin gudunmuwar da gwamnati za ta iya bayarwa. A bayar da fifiko wajen noman shinkafa, ta hanyar tabbatar da cewa ana yin noman a daukacin shekara. A hana shigo da shinkafa, ta yadda za a kara himma wajen nomanta a cikin gida. Akwai sauran nau’ukan hatsi da za mu ba su muhimmanci kafin mu samar da shinkafar da za ta wadace. Alal misali, a samar da yanayin samun tallafin bashin kudi. Idan har za ka yi noma dole ka mallaki daukacin kayan aikin gona, wadanda za ka iya sayensu da kudi.
Mafi yawan manomanmu ba su da isassun kudin sayen wadannan kayan aiki.. Saboda haka akwai bukatar samar da kafar samun tallafin bashi gare su. Na biyu dokar muhalli dole ta ta’allaka wajen noma abinci a gida. Kuma manoma suna da karancin sanin yadda za su kula da tsirran da suka noma, saboda haka akwai bukatar gwamnati ta rinka tura musu malaman gona. Su kuwa kamfanoni masu zaman kansu, idan gwamnati ta samar da kyakkyawan yanayi, sai masu saka jari su shugi a dama da su, ta yadda za mu rinka noma fiye da abin da muke bukata.