Wadda ke damfara da sunan matar gwamnan Katsina ta shiga hannu

Mata da mijin na amfani da sunan matar gwamnan Katsina wajen damfara masu canjin kuɗi.

Wadda ke damfara da sunan matar gwamnan Katsina ta shiga hannu

Hukumar EFCC ta kama wata mata da mijinta bisa zargin yin sojan gona da sunan mai ɗakin Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Fatima Dikko Radda, wajen damfarar kuɗi Naira miliyan 197.75.

An gurfanar da su a gaban babbar kotun Jihar Kaduna, tare da wasu mutum biyu da ake zargi suna taimaka musu wajen aikata laifin.

EFCC ta ce mutanen huɗu sun haɗa kai wajen amfani da sunan Hajiya Fatima Dikko Radda don samun canjin dala daga wani mai sana’ar canji.

Matar ta gabatar da kanta a matsayin Fatima Dikko Radda, tana buƙatar a yi mata canjin dala.

Mijinta kuma ya samar da layukan waya da aka yi wa rajista da sunan Fatima Dikko Radda, domin a rikita tunanin mai amfani da manhajar ‘True Caller’.

Bayan matar ta nemi a yi mata canjin dala, sai suka turawa mai canjin lambar asusun banki da zai tura kuɗin kafin ta aika masa da dalar.

Da farko, ta karɓi Naira miliyan 89 daga hannun wani mutum mai suna Aminu Usman, da nufin za ta tura masa dala 53,300.

Daga baya kuma, ta sake karɓar Naira miliyan 108, tana mai cewa za ta tura masa dala 118,000.

EFCC na ci gaba da bincike kan lamarin.