Wadda ta yi garkuwa da kanta ta shiga komar ’yan sanda
Dubun wata mata mai shekara 26 mai suna Ataghar Namdoo ya cika bayan da ta hada baki da saurayinta suka yi garkuwar bogi da ita don karbar kudi daga wajen uwar dakinta da take yi wa aiki. Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas DSP Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa jami’ansu sun kama wadda […]
Dubun wata mata mai shekara 26 mai suna Ataghar Namdoo ya cika bayan da ta hada baki da saurayinta suka yi garkuwar bogi da ita don karbar kudi daga wajen uwar dakinta da take yi wa aiki.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas DSP Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa jami’ansu sun kama wadda ake zargin da wani mai suna Okpe Dabid, inda ya ce matar ta hada baki da saurayinta da wani mutum suka dauki bidiyonta a daure, bakinta a rufe a wani daji a yankin Ajah, sannan wani matashi da ya rufe fuskarsa a bidiyon yana cewa sun yi garkuwa da matar ce inda suka bukaci a ba su Naira miliyan 10 ko su kashe ta, sannan suka yi barazanar far wa iyalan wanda matar ke yi wa aiki, kuma suka dauki bidiyo na biyu inda suka nuna sun shiga da ita cikin daji.
Ya ce bayan sun tura wa uwar dakin matar bidiyon sun yi ta kiranta suna yi mata barazana lamarin da ya sa ta sanar da ’yan sanda. “Nan take Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Legas, Hakeem Odumosu ya ba runduna ta musamman da ke yaki da garkuwa da mutane umarnin bincikar lamarin, inda aka gano cewa mutumin da ke cikin bidiyon rike da wuka da ya rufe fuskarsa saurayin matar ce mai suna Emanuel Inu. Binciken da jami’anmu suka yi ya kai ga gano matar tare da kama Okpe Dabid wanda ya ce shi soja ne kuma yanzu haka ana bincike a kansa. Dukkan wadanda ake zargin sun amsa laifinsu inda suka ce su ukun sun san juna da dadewa kuma dukkansu ’yan Jihar Binuwai ne, sun shirya haka ne domin karbar Naira miliyan 10 daga uwar dakin Ataghar Namdoo,” inji shi.
Bala Elkana ya ce jami’ansu na kokarin kamo saurayinta Emanuel Anu wanda ya tsere, ya ce a dokar Jihar Legas babban laifi ne mutum ya shirya yin garkuwar bogi da kansa kuma ina an same su da laifi za su iya shafe shekara 14 a gidan yari.