Wadume: Kotu ta dage sauraron shari’ar ta’addanci

Shari’ar Hamisu Bala, wanda aka fi sani da Wadume, da ake zargi da garkuwa da mutane da kisan kai ta samu tsaiko saboda rashin zaman alkali mai sauraron shari’ar. Antoni Janar na Tarayya ya shigar da karar Wadume da wasu mutum shida bisa zargin aikata laifuka 13 da suka danganci garkuwa da mutane da kisan […]

Wadume: Kotu ta dage sauraron shari’ar ta’addanci

Wadume: Kotu da dage sauraron shari’ar kisa

Shari’ar Hamisu Bala, wanda aka fi sani da Wadume, da ake zargi da garkuwa da mutane da kisan kai ta samu tsaiko saboda rashin zaman alkali mai sauraron shari’ar.

Antoni Janar na Tarayya ya shigar da karar Wadume da wasu mutum shida bisa zargin aikata laifuka 13 da suka danganci garkuwa da mutane da kisan kai da ta’addanci da kuma mallakar haramtattun makamai.

An dage shari’ar Wadume da mutum shidan ne zuwa ranar 13 ga watan Yuli a gaban Mai Shari’a Binta Nyako a Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja.

Wadanda ake karar da lauyoyinsu sun halarci zaman kotun ranar Talata kafin daga bisani aka sanar cewa mai Sharia’a Binta Nyako ba za ta samu yi ba.

Sauran wadanda ake karar sun hada da Isfekta wanda jami’i ne a Hedikwatar ‘yan sanda a Karamar Hukumar Ibi ta Jihar Taraba.

Sauran su ne Auwalu Bala (Omo Razor) da Uba Bala (Uba Belu) da Bashir Waziri (Baba runs) da Zubairu Abdullahi (Basho) da Hafizu Bala (Maiwalda) da kuma Rayyanu Abdul.

A zaman kotun na baya, Mai Shari’a Binta Nyako ta yi watsi da bukatar wadanda ake karar na samun beli. Maimakon haka ta bukaci a hanzarta sauraron shari’ar.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno