WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar dalibai 91,225
Hukumar Shirya Jarrabawa ta Yammacin Afrika (WAEC) ta sanar da sakamakon jarrabawar shaidar samun takardar kammala makarantar sakandare (WASSCE) na dalibai dubu 91,225 da suka rubuta a shekarar 2019. Shugaban ofishin WAEC na Najeriya Mista Olu I. Adenipekun, ne ya sanar da hakan ga manema labarai yau Juma’a, inda ya ce dalibai dubu 97,080 ne […]
Hukumar Shirya Jarrabawa ta Yammacin Afrika (WAEC) ta sanar da sakamakon jarrabawar shaidar samun takardar kammala makarantar sakandare (WASSCE) na dalibai dubu 91,225 da suka rubuta a shekarar 2019.
Shugaban ofishin WAEC na Najeriya Mista Olu I. Adenipekun, ne ya sanar da hakan ga manema labarai yau Juma’a, inda ya ce dalibai dubu 97,080 ne suka yi rijistar jarrabawar WEAC, yayin da dalibai 94,884 ne suka samu damar rubuta jarrabawar.
A cikin dalibai 94,884 da suka rubuta jarrabawar, an fitar da sakamakon dalibai 91,225. Nan gaba kadan za a fitar da sakamakon dalibai 3,659.