WAEC ta saki sakamakon jarabawar 2025
Jimillar ɗalibai 1,973,253 daga makarantu 23,554 da aka amince da su ne suka zauna jarabawar bana.
Hukumar da ke shirya jarabawa kammala karatun sakandire a Afrika ta Yamma (WAEC), ta saki sakamakon jarabawar SSCE na shekarar 2025.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Litinin, 4 ga Agustan 2025, tana mai cewa dukkan ɗaliban da suka zauna jarabawar yanzu za su iya duba sakamakon nasu a shafinta na intanet.
- Za a mayar da gidan yarin da ya haura shekara 100 zuwa gidan tarihi a Kano
- An sace jariri sabuwar haihuwa a asibitin Ekiti
“WAEC na farin cikin sanar da ɗalibai da suka rubuta jarabawar WASSCE a shekarar 2025 cewa an saki sakamakon a hukumance yau Litinin, 4 ga watan Agusta,” in ji sanarwar.
WAEC ta buƙaci ɗalibai da su shiga shafin duba sakamako na hukuma a (http://waecdirect.org) ko (http://waecdirect.org) domin duba sakamakon su ta amfani da bayanan jarabawa da lambobin tantance sakamako wato result checker pins.
A nasa bangaren, shugaban ofishin WAEC na Nijeriya, Amos Dangut, ya bayyana cewa an samu raguwar kashi 33.8 cikin ɗari na sakamako masu kyau idan aka kwatanta da na shekarar 2024.
Da yake zantawa da manema labarai a birnin Legas, Dangut ya ce kashi 72.12 cikin ɗari na ɗaliban da suka samu makin credit ko fiye a aƙalla darussa biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi — adadi ne da ya yi kasa da na bara da kusan kashi 34 cikin ɗari.
“A ƙididdigar da muka yi tsakanin sakamakon jarabawar 2024 da na 2025, mun lura cewa an samu raguwar kashi 33.8 cikin ɗari a yawan ɗaliban da suka samu makin credit ko fiye a aƙalla darussa biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi,” in ji shi.
Aminiya ta rawaito cewa wannan dai na zuwa ne bayan ɗalibai da iyaye da su kansu makarantun sakandare a faɗin ƙasar sun shafe makonni suna dakon fitowar sakamakon jarabawar na bana.
Jimillar ɗalibai 1,973,253 daga makarantu 23,554 da aka amince da su ne suka zauna jarabawar bana.