WAEC ta sanar da ranar fara jarrabawar WASSCE ta 2021
Za a fara jarrabawar ne ranar Litinin, 16 ga watan Agustan 2021.
Wasu dalibai na rubuta jarrabawa
Hukumar Shirya Jarrabawar ta Afirka ta Yamma (WAEC) ta sanar da ranar Litinin, 16 ga watan Agustan 2021 a matsayin ranar da za a fara rubuta jarrabawar kammala sakandire (WASSCE).
Babban jami’in hukumar a Najeriya, Mista Patrick Areghan ne ya sanar da haka a Legas ranar Talata.
- Kwalara ta kashe mutum 4, ta kama 48 a Gombe
- An kashe mutum 112, an sace 160 a Kaduna da Filato a wata daya – Rahoto
A cewar sanarwar, “La’akari da jadawalin da aka amince da shi na kasa da kasa, jarrabawar WASCCE ta shekarar 2021 a dukkan yankin da ake rubutata za ta gudana daga ranar Litinin 16 ga watan Agusta zuwa Juma’a, takwas ga watan Oktoban 2021.
“To sai dai a Najeriya, za a kammala jarrabawar ne ranar 30 ga watan Satumban 2021, bayan an shafe makonni bakwai kenan ana yinta,” inji sanarwar.
A baya dai, akan rubuta jarrabawar ne a tsakanin watannin Afrilu da Mayun kowacce shekara, in ban da a bana da aka sami tsaiko sakamakon yadda annobar COVID-19 ta kawo dagula lamura.