WAFU B: Yadda Najeriya ta lallasa Burkina Faso a wasan karshe

Tun bayan minti takwas da fara wasan na ranar Juma’a Najeriya ta fara ragargazar Burkina Faso

WAFU B: Yadda Najeriya ta lallasa Burkina Faso a wasan karshe

Kungiyar Kwallon Kafa ta Golden Eaglets ta lashe Gasar WAFU B na matasa ’yan Shekara 17, bayan ta lallasa Young Stallions na Kasar Burkina Faso a wasan karshe.

Golden Eaglets sun lashe gasar ce bayan sun yi wa Young Stallions ci 2-1 a wasan karshe da suka gwabza a filin wasa na Cape Coast da ke kasar Ghana.

Hakan na zuwa ne ba jimawa bayan kungiyar ta lashe gasar ’yan kasa da shekara 20, inda ta doke Jamhuriyar Benin a wasan karshe da suka buga a Jamhuriyar Nijar.

Tun bayan minti takwas da fara wasan na ranar Juma’a Najeriya ta fara ragargazar Burkina Faso, inda dan wasan gabanta, Abubakar Abdullahi, ya kai musu wani mummunan hari, amma suka sha da kyar.

A minti na 22 da fara wasan ne Emmanuel Micheal ya tura wa dan wasan gaban wani kwallo, shi kuma ya huce haushinsa, inda ya zura kwallon farko a wasan a ragar Burkina Faso.

Abubakar Abdullahi ya kuma yi kokarin kara wa Young Stallions wani kwallo, amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba.

Bayan minti bakwai da hakan ne dan wasan Burkina Faso, Abdulramane Ouedraogo, ya farke ta hanyar cin Najeriya da ka; A haka aka tafi hutun rabin lokaci, ana kunnen doki.

Minti biyu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Abdullahi ya kara zura wa Burkina Faso Kwallo, ya kuma ci gaba da kai musu farmaki.

Bayan minti 12 da zura kwallon ya kara kai wata raraka a ragar Young Stallions, amma bai cim ma nasara ba.

Kafin a tashi daga wasan Burkina Faso ta nemi zura kwallo a ragar Najeriya, amma mai tsaron ragar, Richard Odoh, ya tare.

Haka kuma a minti na 67, Ebube Okeke ya kai hari ragar Burki Faso, amma kwallon ta daki turke ta yi waje.

Haka dai aka tashi wasan, Najeriya 2, Burkina Faso 1, wanda ya ba wa Golden Eaglets damar zama zakarun Gasar ta WAFU B a wannan karon.

A karshen wasan an zabi golan Najeirya, Richard Odoh, a matsayin wanda ya fi nuna bajinta a wasan.

Sau biyar Najeriya na lashe gasar matasa ’yan kasa da shekara 17 a matakin duniya.

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa

Ƙungiya ta buƙaci rage harajin cinikayya saboda ƙuncin rayuwa