Wahala da yunwa suka sa mu tattaki daga Katsina zuwa Bauchi – Almajirai

Wadansu kananan yara almajirai ’yan shekara 5 zuwa 10 da aka kai su makarantar allo a garin Sabuwa da ke Jihar Katsina daga karamar Hukumar Alkaleri a Jihar Bauchi, sun ce wahala da yunwa ne suka tilasta su yin tattaki daga Katsina zuwa Bauchi don komawa garinsu. Almajiran wadanda dukansu Fulani ne da suka ce […]

Wahala da yunwa suka sa mu tattaki daga Katsina zuwa Bauchi – Almajirai

Wadansu kananan yara almajirai ’yan shekara 5 zuwa 10 da aka kai su makarantar allo a garin Sabuwa da ke Jihar Katsina daga karamar Hukumar Alkaleri a Jihar Bauchi, sun ce wahala da yunwa ne suka tilasta su yin tattaki daga Katsina zuwa Bauchi don komawa garinsu.

Almajiran wadanda dukansu Fulani ne da suka ce sun shafe kwanaki 6, suna wannan tattaki da kafa da niyyar komawa garinsu, an tsince su ne a kauyen Kwabi da ke karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi.  

Da yake zantawa da wakilinmu, daya daga cikin yaran mai suna Sani Usman ya ce sun fito ne daga karamar Hukumar Alkaleri da ke Jihar Bauchi, kuma kawunsu ne ya kai su wurin wani malami don yin almajiranci a garin Sabuwa da ke Jihar Katsina.

 Sani Usman ya ce sakamakon yunwa da wahala da kuma duka da malaminsu yake yi musu ne suka gudo.  “Da kafa muka taho daga Katsina za mu koma gida, mun yi kwanaki 6 muna wannan tafiya da kafa. Shi ne wadansu suka tsince mu suka kawo mu nan Sakatariyar karamar Hukumar Toro,” inji Sani Usman.  

 Da yake zantawa da wakilinmu kan al’amarin, Daraktan Sashin Ilimi da Walwalar Jama’a na karamar Hukumar Toro, Malam Ibrahim Yaro Gumau ya bayyana takaicinsa kan yadda irin wadannan abubuwa suke faruwa a yanzu.

Ya ce kusan duk mako suna samun irin wadannan yara da ake tsintowa ana kawo musu a karamar hukumarsu.

Ibrahim Yaro ya ce har yanzu mutanenmu suna daukar kananan yara da ba su san komai ba, suna kai su makarantar allo da sunan yin karatua can nesa. Kuma da dama ba karatun suke yi ba, ana sanya su ayyukan wahala ne kuma su ne suke neman abincin da za su ci.  

Ya ce sakamakon tsintar yarar sun kira jami’an karamar Hukumar Alkaleri, sun shaida musu kuma za su tura musu takarda domin su binciko iyayensu domin su zo su zauna da su kamar yadda suke yi.  “Muna kira ga jama’a su guji tura ’ya’yansu kanana da ba su da wayo zuwa makaranta a nesa da su. Domin yanzu yara ko a gidajen iyayensu, za su iya yin karatun Alkur’ani har su sauke,” inji Daraktan