Wai me ke damun Dokta Ahmad Gumi ne? (2)
Dokta ya ce: “A wancan karon na mulkinsa na farko, akwai malaman da suka yi masa nasiha game da yadda yake tafiyar da mulkinsa, domin shi ne wajibin malami ba tare da jin tsoron kowa ba sai Allah.” Abin tambaya a nan shi ne, wadanne malamai ne wadannan? A gaya mana sunayensu kuma dalilin me […]
Dokta ya ce: “A wancan karon na mulkinsa na farko, akwai malaman da suka yi masa nasiha game da yadda yake tafiyar da mulkinsa, domin shi ne wajibin malami ba tare da jin tsoron kowa ba sai Allah.” Abin tambaya a nan shi ne, wadanne malamai ne wadannan? A gaya mana sunayensu kuma dalilin me suka yi masa nasiha? Mu dai mun san Buhari a mulkinsa ya yi yaki ne da cin hanci da rashawa kuma ya kame masu kudi da suka ciwo bashi da sunan kasa suka ki biya. Abin mamaki shi ne, Dokta na tare da Buhari a 2003 har zuwa gabanin zaben 2007 kuma binciken da na yi ya tabbatar mun da cewa har a Saudiyya ya nemi taimako don agaza wa takarar Jonathan, matsayinsa na Musulmi. Shin bai san da hakan ba ne ko mancewa ya yi?
Akwai kuma inda ya ce: “Wallahi idan ka yi imanin cewa musibar da muka fada cikinta babu mai gyara ta sai Buhari, ka yi shirka. Shin in kura tana maganin zawo ta yi wa kanta mana. Ba ku ganin yadda shi kansa Buhari ya kasa ba kansa mulkin kasar nan? Domin mulki na Allah ne, har ka ce: ‘Sai Buhari!’ To, a nan duk da karancin ilimina na san an tafka kuskure mummuna. Shirka ita ce laifi mafi girma a shari’ar Musulunci kuma mutum ba ya zama mai shirka har sai ya kudurci abin da ya furta. Furuci kadai ba ya saka mutum shirka sai da yakini, kamar yadda Malam Ja’afar ya bayyana cikin bayanansa kuma Musulunci ya yi umarni da ka fadi alheri ko ka yi shiru. Shin wadannan kalaman suna da alheri a wannan yanayin? Lallai tun da ’yan takara guda biyu ne kadai, duk wani mai hankali zai iya gane cewa wata manufa ce ta mika mutane ga Jonathan. Saboda haka ina kira ga Malam da ya daina wadannan maganganu, musamman a wannan lokaci mai tsanani.
Dokta ya ce: “Kuna son ku halaka kanku, ku halaka shi. Ku sa masa buri a zuciyarsa, maimakon ku bar shi a nuna masa yadda zai yi kaffarar kura-kuransa na baya, wadanda suna daga cikin sababin jefa mu cikin wannan musiba. Sai ga shi kun fito ’yan kanzagi, kuna son ku hana shi istigfari.”
A zahiri wadannan kalamai sun nuna rashin adalcinsa a fili, saboda ba wanda ya sanar da shi cewa Allah na fushi da Buhari, balle ya ce ya dakatar da al’amuransa na rayuwa, ya koma istigfari. Shi kansa Dokta idan aka duba bayanansa munana a kan sahabbai da kuma manyan malamai na addini, ai shi ya fi cancanta da ya je neman tuba da istigfari, tun da shi ya fi Buhari sanin hukunce-hukunce da kuma tsananin azabar Allah ga duk wanda ya kauce daga kan hanyar da Allah Ya dora shi.
Dokta Gumi ya ce: “Kun ga dai Boko Haram sun fi ku ikirari mai manufa, domin su sun labe da sunan Allah ne da sunnar manzon Allah (SAW). Amma ku ’yan-ga-ni-a-kashen mutum ne. To, wallahi ku yi hattara. Za a zo a yi amfani da ku, bayan an harzuka ku, a maida ku kamar ’yan ta’adda, ’yan Boko Haram masu tada fitina, masu tada zaune tsaye.”
Dokta Gumi kuma ya yi rubutu na neman kariya daga zantukan mutane, yana cewa shi bai zagi Buhari ba kuma bai hana kowa ya zabi Buhari ba. To, ina zancen halatta magudin zabe yake kuma shin wadannan bayanai na fifita ’yan Boko Harama kan masoya Buhari, me suke nufi?
Lallai ina ba Dokta Ahmad Abubakar Gumi shawarar cewa, addinin nan namu ne da mu da shi baki daya kuma babu wanda aka killace shi da fahimtar addini shi kadai, sannan idan yana da sabani na siyasa dole ya yi shi cikin hikima; domin al’umma sun farka daga jahilcin da yake tsammani kuma ilimi ya fara yaduwa da wayewar kai. Saboda haka duk wani malami da zai yi nasiha, ya inganta niyyarsa, ya kuma kauda son rai a cikin bayanansa. Da haka ne addini zai daukaka kuma Allah zai tabbatar mana da haduwar kai da kuma natsuwa da zaman lafiya.
Allah ta’ala Ya gafarta mana kura-kurenmu, amin!
Mun kammala