Wai me Obasanjo ke nufi ne?
Watanni biyu ke nan da ‘yan kwanaki tun lokacin da ‘yan ta’adda suka wafce ‘yanmatan Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Chibok a Jihar Barno, kuma har yanzu suna can a hannunsu, cikin bakar Ukuba da takaici da bakin cikin da bai misaltuwa. An yi kwarmato har bakuna sun yi kumfa, an kakkaga hakarkari har aka kai […]
Watanni biyu ke nan da ‘yan kwanaki tun lokacin da ‘yan ta’adda suka wafce ‘yanmatan Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Chibok a Jihar Barno, kuma har yanzu suna can a hannunsu, cikin bakar Ukuba da takaici da bakin cikin da bai misaltuwa. An yi kwarmato har bakuna sun yi kumfa, an kakkaga hakarkari har aka kai ruwa rana, an yi soki-burutsu da nuna yatsun zargi ga jami’an tsaron da suka kasa yin katabus wajen kare rayuka da dukiyar jama’an shiyyar Arewa-maso-Gabas, an kuma ga wallen gwamnati da shugabanninta don rashin tabuka komai wajen kwato wadannan ‘yanmata da kuma kasa magance tabarbarewar al’amari irin haka.
Duniya ta tausayawa jama’an Jihar Barno da kuma iyayen yaran da wannan masifar ta afkawa, kasashen da ake gani sun kware a harkokin tsaro da kuma leken asiri sun nuna matukar damuwa game da haka, har suka ce za su bayar da dukkan taimako da gudummawar da Gwamnatin Shugaba Goodluck za ta nema don zakulo wadancan ‘yanmatan, su kuma dauki matakan magance ta’addancin kungiyar da ake kira Boko Haram.
A yanzu wata guda ke nan bayan an amincewa Turawa da yin haka, amma babu wani kwakkwaran abin da suka aikata da zai kwantar da hankalin jama’a, ya kuma nuna cewa da gaske suke yi game da neman inda ‘yanmatan suke. Sun kawo jiragen da ba su da matuka, sun murda taurarinsu na sararin samaniya suna kallon yankin Barno, sun yi kwana-da-kwanaki suna ta shawagi da karakaina a kauyuka da manyan garuruwan da ke cikin Jihar Barno da kuma wadanda ke kan iyakar kasar Najeriya da Kamaru da Nijar da Chadi, amma har yanzu ko gyalen yarinya guda ba su hango ba. Hasali ma jama’a kuka suke da wadannan Turawa, domin a ganinsu, ko kuma a ce a saninsu, ba batun nemo wadancan ‘yanmatan ne suka sanya a gaba ba, a’a sun dukufa ne wajen ci gaba da leken asiri da kuma kokarin gano cikakkun bayanai game da dimbin arzikin da ke bizne a wannan yankin, da kuma tsara dabarun yadda za su tozarta jinsin wasu mutanen kasar nan da abin da suka yi imani da shi.
A takaice dai ana iya cewa gwamnatin Najeriya ta fara mancewa da batun wadancan ‘yanmatan, domin kuwa tun can farko ba ta damu da halin da miliyoyin mutanen shiyyar Arewa-maso-gabas suke ciki ba. An batar da dubban miliyoyin Nairori don jami’an tsaro su ji dadin murkushe ta’addanci, amma hakan bai hana dubban miliyoyin dukiyar jama’an asarar dukiya da rayukansu ba kullu yaumin. Duk da dokar ta bacin da ake ta kafawa har yanzu babu lokacin da za a kawo karshen wannan mummunar masifar.
A kwanaki babban hafsan askarawan kasar nan ya ce gwamnati ta gano inda ‘yanmatan nan suke, amma ba zai fada ba don gudun kada garin neman kiba a jajibo rama, kuma kafin hankulan jama’a su kwanta bayan tunzurin da suka yi saboda furucin wancan babban kwamandan, sai kuma ga tsohon shugaban kasa na wata magana mai ban haushi, kuma cike da takaici: wai ko da ma za a gano ‘yanmatan nan to rabin su ne kadai za su dawo, domin an mayar da wasunsu sadakai, kuma sai idan sun yi cikin shege ne, ko kuma sun haihu za a koro su zuwa ga iyayensu. To wai shin me Obasanjo yake nufi da wannan furucin? Ba shakka wadannan kalamai ba irin na dattijon arziki ne ba, domin kuwa Cif Obasanjo bai nuna damuwa da halin matsin da ‘yanmatan ke ciki ba, shi kokarinsa shi ne ya mayar da al’amarinsu na siyasa don biyan wasu bukatunsa. Yanzu dai ana iya zargin cewa Cif Olusegun Obasanjo na da masaniya game da inda ‘yanmatan nan suke tun da ya san cewa rabinsu ne kawai za su iya komowa. Idan aka tutsiye shi, aka kuma takura masa zai fadi inda sauran suke, wadanda ya ce za a koro idan sun yi ciki ko sun haihu.
An dade ana zargin cewa Obasanjo dan koren Amurka ne, wanda ke tona asirin kasarsa gare su don su ji dadin ci gaba da tatuke arzikinta, suna kuma kuntata wa jama’arsa. Watakila dai bakinsu daya ne da Amurka game da alkawarin da suka yi na gano wadancan ‘yanmatan. Kamar yadda wasu ‘yan majalisar dokokin kasar Amurka guda hudu suka fayyace wa manema labarai a wata ganawa da suka yi da su a Unity Fountain da ke Abuja, kasarsu ta fara yunkurawa don tunkarar ‘yan kungiyar Boko Haram da niyyar kwato ‘yanmatan, kuma tun da Obasanjo ya san halin da ‘yanmatan ke ciki ai ba abin da ya hana shi yi wa Amurkawan jagora don a ceto su, domin kuwa an ce da dan gari ake cin gari.
Tun ba yau ne ba Olusegun Obasanjo ke tutiyar yana da wata alaka ta musamman da kungiyar Boko Haram, har ma ya taba ziyartarsu a garin Maiduguri, al’amarin da ya janyo rasuwar daya daga cikin mutanen marigayi Muhammad Yusuf. A yanzu kuma ga shi nan yana ikirarin sanin inda ‘yanmatan suke, yana kuma bugun kirji, yana cewa idan har an amince masa zai taimaka wajen kwato ‘yanmatan domin ya san yadda zai tunkari ‘yan Boko Haram game da haka. To da walakin, goro a miya.