Wai mene ne dadin duniya?
A kullum na tsaya ina tunanin irin yadda muke ta hankoro da kai-kawo domin ganin mun biya bukatun rayuwa ko ta wace irin fuska, sai na ga tamkar muna aikin baban-giwa ne, domin dukkan abin da ka sa gaba, ka kuma samu, to da yana farko da kuma karshe.Dukkan irin abin da kake ta hakilon […]
A kullum na tsaya ina tunanin irin yadda muke ta hankoro da kai-kawo domin ganin mun biya bukatun rayuwa ko ta wace irin fuska, sai na ga tamkar muna aikin baban-giwa ne, domin dukkan abin da ka sa gaba, ka kuma samu, to da yana farko da kuma karshe.
Dukkan irin abin da kake ta hakilon tarawa ko don biyan taka bukata ko ta iyali ko wani abu makamamcin haka, sai na ga ci gaba da yalwata ce irin ta mai ginar rijiya.
In yau duk fadin duniyar nan ba ka da na biyu a tarin dukiya, to sai me? Wannan shi ne jin dadin duniya? Gidaje da mutum ya tara ko makudai da ke cikin banki ko kyawawan mata da mutum ya ajiye, a narka-narkan gidaje ko kuma yawan arzikin ’ya’ya da mutum ya samu, su ne alamun mutum ya samu abin jin dadin duniya?
Shin rashin matsaloli na rayuwa, komai ya yi wa mutum daidai, kana ci, kana sha, kana bushaha, wannan shi ne jin dadin rayuwar? Shin tufatar da kai daga siliki ko tufa da ta fi kowace tsada da burgewa, shi ne jin dadin rayuwar?
Don yau abin hawa na gani da fada ya zama abin kawa a gare ka, ka shiga wancan dankareriyar mota, ka hau doki na isa ko kuma kai ne da jiragen sama ko na ruwa, naka na kanka, shi ke nan kai duniyar ta yi ma tsaf, sai fankama da nuna isa da ganin ai ba wani sai kai, wannan shi ne jin dadin rayuwar?
Tambayoyin ba su taba karewa, domin kuwa abubuwan tsinkayar ba sa misaltuwa. Amma abin lura a koyaushe shi ne, ina amfanin irin wannan rayuwar tunda ba ta da tabbas! Mene ne amfanin rayuwar da ke da iyaka! Mene ne na nuna isa bisa ga abin da ba rawa mutum ya yi aka ba shi ba! Ina amfanin badi ba rai!
Na san wani zai iya cewa ai ba abin da ya fi komai dadi da more wa rayuwa irin ka kasance ba matsala a rayuwa. Komai ya ji! Komai ya zauna! Sai dai ka wanke goma ka tsoma biyar a dukkan lamurra! To amma hakan gaskiya ne? Tarin dukiya ko iyali ko wani kyale-kyalen yau da gobe shi ne samun kwanciyar hankali da jin dadin duniya? Ko kadan ba haka ba ne! Tarin dukiya a lokuta da dama tarin wahala ne!
Wasu kuma ba abin da suke gani a matsayin isa da samun kwanciyar hankali irin ka samu mulki ka rike, ka yi dumu-dumu cikin masu-fada-a-ji, ya kasance kana cikin masu karyawa ko ba kan gaba ba. In kuma ba ka da iko a hannunka to ka kasance daga masu biye da masu ikon, abin nan da ake cewa ana yi da kai ya fi, ba a yi da kai. Ke nan mulki da mulka suna daga cikin jin dadin rayuwa, wanda kuma bai da su ko bai kusance su ba, bai da alamun jin dadin rayuwa ke nan? Wannan ma tsinkaya ce a karkace, domin hawa bisa karagar mulki, ba shi ne jin dadi ba. Kamawa da karywa bisa tafarkin isa da nuna isa ba shi ne burgewar rayuwa ba. Mulkin da kurar mulkin da ba za su tabbata ba, duk feleke ne, ba inda za su kai mai neman su ko yake dambare tare da su, tunda ba a guzuri da su zuwa ga matabbata. Ke nan jin dadin rayuwa ba wai ya jingina ga marmaron da dadin baki ke ji ba ne! Haka kuma bai kasance daga burgewar masu burgewa ba, ko kuma daga karfin masu karfin mulki da isa ba!
Ashe ke nan jin dadin rayuwa holoko ne hadarin kaka! Jin dadin rayuwa birkita kwanci ne a kare da kwaso bara-gurbi! Jin dadin rayuwa ba komai ba ne sai ihu bayan hari! Wannan kuwa haka yake, domin in tarin dukiya ne jin dadin rayuwa to ina karuna a jiya, ina kuma karunan wannan zamani? In mulki da isa shi ne jin dadin rayuwa, to ina Fir’aunan da. Ina kuma na yanzu? In tarin ’ya’ya ke sa mutum ya ji ya fi kowa jin dadin rayuwa, ina wadanda aka haifa jiya, ina kuma ’ya’yan yau da na gobe? Wane gida ne komai kyawo da tsarinsa ba zai zama kushewa ba? Wace mata ce da Allah Ya yi wa kyau da ke tabbata a doron kasa da mijinta zai ji ba wata irinta a doron kasa da ba za ta tafi zuwa ga kushewa ba?
Ashe ke nan dadin rayuwa bai wuce mu rage dogon buri da yawan mantuwa ba, siffofin nan biyu da suka tabbata a tsakaninmu, jiya da yau da kuma gobe! Duk burin rayuwa bai wuce ta ji dadi da walwala, ta shere ta kuma sherar ba, amma ina ne wakafi da ayar irin wannan buri, shi ne kushewa, a koma yadda aka fito, daga kasa zuwa ga kasa! Wannan shi ne a’ala, shi ne kuma abin da ke jawo kason na biyu, yawan mantuwa. Dukkan irin tarin burin rayuwar yau, an jima kadai ake jira, za ta kare, ba sai an kai gobe ba, domin gobe, zango ce mai nisa, ga wanda ya kai gare ta, to kuwa in buri ya kare, a kuma daidai wannan lokaci, abubuwan da aka manta suke bankado kansu, su dawo zuwa ga wanda ya manta, farat daya, tamkar majigi. A nan kuma ake gane cewa dogon buri, dakinsa mantuwa, a lokacin da ake faman yin fargar jaji! Allah Ya kyauta!