Wai shin ina mafita ga Arewa?
Ba tare da raba daya biyu ba, kowa ya san halin da Arewa take ciki na kaka-ni-kayi. Al’amura sun sakwarkwace, Arewa ta zama kashin baya a dukkan al’amura. Shin ina mafita daga wannan waskataccen yanayi? MALAMA A’ISHA USMAN LIMAN (09093467171), mai sharhi kan al’amuran yau da kullum ta dauki alkalami domin nemo wa Arewa mafiya. […]
Ba tare da raba daya biyu ba, kowa ya san halin da Arewa take ciki na kaka-ni-kayi. Al’amura sun sakwarkwace, Arewa ta zama kashin baya a dukkan al’amura. Shin ina mafita daga wannan waskataccen yanayi? MALAMA A’ISHA USMAN LIMAN (09093467171), mai sharhi kan al’amuran yau da kullum ta dauki alkalami domin nemo wa Arewa mafiya. Ta yaya? Ga abin da take cewa:
Arewa ita ce yanki babba mafi girma daga cikin yankunan kasarmu Najeriya. Yanki ne mafi yawan al’umma da fadin kasa. Allah Ya wadata Arewa da arzikin kasar noma da arzikin albarkatun karkashin kasa iri-iri, ga ilimin addinin Musulinci tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka, ga tsarin masarautu da mukamai iri-iri cikin kowace jiha ko karamar hukuma ko gunduma.
Allah Ya albarkanci yankin da haihuwar ’ya’yaye masu albarka da kwazo da kishin zuci da kishin mahaifa, wanda shi ya yi musabbabin kai ta ga yin fice da daukaka, aka ji ta gabas da yamma, kudu da arewa na nahiyar Afirika da ma duniya baki daya tun ma kafin zuwan Turawa.
Arewa ta yi fice wurin noma da kiwo da kasuwanci da duk wata hulda ta kawo ci gaban al’umma. Ta yi suna wajen samar da hanyoyin zaman lafiya da kwanciyar hankali ga al’ummarta da kasa, da ma duniya baki daya.
Al’ummar Arewa mutane ne masu son zumunci da so da kauna da kulawa a tsakaninsu, kai har ma ga makwabtansu. Allah Ya hore musu tarbiyya mai kyau da al’adu tsarkaka, ga biyayyar da talakawa ke wa manya da shuwagabanninsu. Wadannan su ne halaye da dabi’un al’ummar Arewa tun ma kafin zuwan Turawa. Da dabi’un suka same su kuma da su suka bar su.
Wadannan kyawawan halaye, su suka sa Turawan mulki suka samu saukin hada kan lardunan nan guda uku wuri daya a 1914, suka kira su da suna Najeriya.
Koda Turawan mulki suka zo, Arewa ce lardin da suka fi samun saukin gudanarwa ta fuskar mulki da kasuwanci da zamantakewa, a dalilin kyawawan tsare-tsare da suka samu al’ummar yankin da su.
Tun bayan da Turawan mulki suka samu nasarar samar da kasa Najeriya, Arewa ce lardin da ya fi kowane lardi kwazo da habaka cikin sauri. A dalilin dace da shuwagabannin kirki da yankin ya yi, nan da nan ya yi zarra har sai da Arewa ta kai ita ce uwa maba da mama a kasar nan, domin duk wani abinci da nama, ita ce take ci da kasar nan da su, kai har ma da makwabtanta. Ba ma abinci kadai ba, har ma da kudin zartarwa na tafiyar da mulki da gudanarwar kasar nan, duk a Arewa ake tatsa daga arzikinta, saboda albarkar da Allah Ya yi mata.
Shuwagabanin Arewa na wancan lokacin, mutane ne masu gaskiya da rikon amana, ga kaunar talakawa da tausayawa, ga su da fatan alheri da burin ganin Arewa da kasar nan ta habaka, ta kamo duk wata kasa da ke tinkahon ta ci gaba. Su dai kullum burinsu da tunaninsu, me za su yi da zai kawo ci gaba cikin sauri a yankin da kasarmu baki daya. Suna da hangen nesa kwarai da gaske kuma ba su yarda da duk wani tunani da zai janyo koma baya ga yankin da ma kasar ba. Shi ya sa suka yi tsaye, suka dage a kan kowane kai-kawo na tafiyar da yankin da ma kasa baki daya, har sai da suka tabbatar da yankin da kasar sun tsayu da kafafunsu, ba abin da zai iya girgiza hadin kan kasar. Suka samar da soyayya da kaunar juna, suka wanzar da yarda da amana ga ’yan kasa, har sai da ta kai kowane dan kasa, in dai mai cikkaken kishin kasa ne, yana fatan alheri ga kowane yanki, kamar yadda yake yi wa nasa yankin.
Irin wannan halayyar ce ta sa kowane al’amari suka tashi yi na tafiyar da kasar nan, yakan zo musu cikin sauki da kwanciyar hankali. Ba wata fitina ko rashin jituwa, balle ma ya kai su ga tashin hankali ko bita-da-kulli ko zamba cikin aminci wa juna. Su dai fatansu a kullum kasa daya al’umma daya.
Tarihi ya nuna mana cewa tun daga lokacin da aka samu nasarar hada kan lardunan Najeriya, har zuwa lokacin da ta samu ’yancin kai, zuwa lokacin juyin mulki na farko a 1966, duk al’amuran mulkin kasar nan yana tafiya cikin fahimtar juna. Komaii ana yin sa cikin jituwa da hadin kai, ba abin da ke cikin zukatan wadannan shugabanni namu illa yaya za su ciyar da kasar nan gaba. Su dai kullum tunanin su gaba daya Najeriyaa, sai dai gasar ci gaban larduna da suka sa wa kansu, domin ana su tunanin, ta haka ne kawai za a samu ci gaba cikin hanzari. Amma kar ku manta fa, duk wani mabubbugar arzikin kasar nan Arewa ce, domin duk wani kudi na tafiyar da al’amura irin su kasafin kudin kasa da rabon arzikin kasa, da duk wani aikin ci gaban kasa,tun daga na tarayya har na jahohi daga Arewa ake samun su. Arewa ce mai arzikin da za a sayar a biya ma’aikatan kasar nan kaf albashi. Duk a Arewa kudin zartarwar suke fitowa. Haka duk wani lardi da yake son ya gwada binciken arzikinsa, Arewa ce za ta tallafa masa da kudin binciken har sai ya samu, kuma ba bashi, ba tsangwama ba gori, kai har masarautar Ingila ma Arewa tana taimaka mata da wani kaso na kudinta. Ba ma Ingila kadai ba, har masarautar Saudiyya ta amfana kwarai da arzikin Arewa. Akwai kasashen Asiya da dama, irin su Malaysia da Bangaledash da sauran su, duk sun tsotsa daga arzikin da Allah Ya yi wa Arewa amma fa duk a karkashin dace da shuwagabannin kwarai da yankin ya yi.
Domin su ba ruwansu da handama da babakere, ba ruwansu da hadama da ha’inci. Ba ruwansu da rashin gaskiya da zalunci, ba ruwansu da zamba cikin aminci. Ba ruwansu da son kai ko nuna fifiko, su dai fatansu da burinsu kullum; rayuwarsu ta amfani al’ummarsu, adalcinsu ya zama ’yanci ga jama’arsu, gaskiyarsu ta zama abin tinkaho ga talakawansu, amanarsu ta zama yardarsu ga mutanensu. Kuma hakan shi ya kai su ga cikar burinsu, har Arewa ta kai yadda suke mafarki, domin ba wanda bai yi alfahari da zamansa dan Arewa ba saboda a lokacin ko talakan Arewa yana alfahari da zamansa talaka daga Arewa, domin girmama shi da ake yi, don mahimmanci da kima da yankinsa yake da su a idon duniya.
Za mu ci gaba