Wai shin ina mafita ga Arewa? (2)
A makon jiya muka kawo kashi na daya na wannan tsokaci daga MALAMA A’ISHA USMAN LIMAN (09093467171). A wannan makon kuma za mu karkare da kashi na biyu, kamar haka:Arewa ta samu daukaka kwarai, har shi ya sa a lokacin ake ganin ragamar shugabancin kasar nan bai dace da kowa ba sai dan Arewa saboda […]
A makon jiya muka kawo kashi na daya na wannan tsokaci daga MALAMA A’ISHA USMAN LIMAN (09093467171). A wannan makon kuma za mu karkare da kashi na biyu, kamar haka:
Arewa ta samu daukaka kwarai, har shi ya sa a lokacin ake ganin ragamar shugabancin kasar nan bai dace da kowa ba sai dan Arewa saboda kwarjini da kima da yankin yake da shi.
Idan da za mu zauna mu kirga yawan shuwagabannin kasar nan, in sha Allahu za mu ga sun kai 14 amma tara 9 daga cikinsu sun zo ne daga yankin Arewa. Alhamdu lillahi, dukansu sun yi kokari, sai dai ’yan kura-kurai da ba za a rasa ba saboda yanayin zamani da canzawar al’amura, amma dukansu sun yi riko da akidar da su baba SARDAUNA suka bar mu da ita.
Kwanaki na tafiya lokaci na shudewa har Allah Ya kawo mu 1998, inda Arewa da kasarmu Najeriya muka yi babban rashi, Allah Ya yi wa shugaban kasarmu, marigayi Sani Abacha rasuwa. Mu dai muna ganin tun daga wannan babban rashi Arewa ta kama hanyar rudani da daburcewa da rashin makama har zuwa yau, domin tun daga lokacin aka samu rashin alkibla mai saiti ga kasar nan. An rasa madogara mai kwari, Arewa ta shiga rudani. Ana cikin wannan kame-kame har aka koma turbar siyasa.
Arewa da zuciya daya ta karbi manhajar siyasar, domin ita ta dauka irin siyasar can baya ce. Kafin mu ankara sai muka ga ashe al’amura sun canza zane. A fakaice sai ga zamba cikin aminci na ta bayyana, kan ka ce kwabo duk hassadar da aka yi wa Arewa shekara da shekaru sai ga ta ta bayyana. Da aka ga an fara mike kafa sai aka fara tunanin ta yaya za a karya Arewa, a durkusar da ita, a maida ita baya; a yi mata illar da duk duniya sai an tsane ta. Shi ne sai aka ga ba yadda za a yi galaba a kanta cikin sauri, sai dai idan an gwara kan ’ya’yanta, an haddasa musu fada da juna ta fuskar siyasa da addini. Shi ke nan sai aka cusa wa ’yan Arewa muguwar akidar siyasa har ta kai ga dan Arewa ya fi son jam’iyyar siyasa a kan yankinsa, koda kuwa mukamin da yake a kai daga gida aka zabe shi. Aka kuma cusa wa yankin bambance-banbancen addini da na kabilanci a cikin kowace hulda da zamantakewar su, musamman a cikin siyasa.
A takaice dai yanzu duk mai hankali da lura da sanin ya kamata a kasar nan ko a waje, ya san Arewa tana cikin wani hali na neman mafita da gaggawa, domin duk wani arziki na ci gaba da take tinkaho da shi yanzu ya rushe, duk wata masana’anta da ke kowane sako na Arewa, komai girmanta, komai kankantarta ta durkushe, koma in ce ta mutu. Noma da kiwon da muka fi iyawa kuma Allah Ya hore mana kasa da yanayi mai kyau don shi, shi ma ya gagare mu (ba isasshen taki, ga shi mun kara yawa, ba wani tsayayyen tallafi daga hukuma. Shi kuwa kiwo kullum sai ka ji makiyaya na gida, da na jeji suna fada da manoma saboda rashin burtali ga barayi sun sa su a a gaba). Ga arzikin kasa da aka saba rabawa daidai, yanzu an tsiri wata tsirfa, wai da yanki mai arziki da yankin ci-ma-zaune ba daya ba. Wai Arewa ce ci-ma-zaune, an manta da cewa kafin mai arzikin ya yi arziki, Arewa ce gatansa da gadararsa da bugun gabansa.
Ba ma wanan ne abin haushin ba, yanzu duk wani tallafi daga Gwamnati Tarayya ko daga Bankin Duniya ga Arewa, a wulakance ake ba ta shi. Mu yanzu ma abun damuwarmu shi ne, a maimakon a bar mu da bakin talaucin da aka cinna mana, a’a sai kuma aka bi mu da kisan mummuke. Wasu yankunan ma na Arewa kamar ba a kasar nan suke ba saboda rashin ga ta. Misali, jihohin Arewa ta gabas, su yanzu ma sun durkushe har kasa, an karya arzikinsu; ba wani kasuwanci da ake yi a wurin. An hana yaransu zuwa makaranta, an yi musu dabaibayi da jahilci da talauci, an kashe makomarsu, domin duk yankin da aka kashe matasa, mata da yara irin Arewa maso gabas ai kuwa illar da zai haifar a gaba sai dai wanda ya gani.
Kuma wannan kudiri na tagayyara Arewa, ta wannan hanya bai tsaya a yankin gabashi ba kadai, a’a, so ake a fantsama shi a dukkan yankunan Arewa, a ga dai yankin ya lalace, ya rasa mafita. Wai ma don rainin da aka yi wa yankin, har ikirarin rabuwa da shi ake yi (wai za a raba kasa). Ai dai kowa ya san dan tawaye kullum burinsa a raba, ba a hada ba.
Lallai kam Arewa tana neman mafita cikin gaggawa amma kuma mu muna ganin za ta samu nan ba da dadewa ba. Domin har yanzu yankin na da sauran gata, tun da har yanzu duk ’ya’yan da take haihuwa masu albarka ne kuma ana damawa da su. Alal misali, yanzu haka cikin wannan shekara, akwai mukamai masu girma da ’ya’yanta ke rike da su kamar haka: Mataimakin Shugaban kasa, Shugaban Majalisar Dattijai kuma ’yan Arewa ne suka fi yawa a majalisar. Shugaban Majalisar Tarayya dan Arewa ne kuma ’yan yankin su suka fi yawa. Sauran sun hada da Babban Jojin Najeriya, Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya, Shugaban Hukumar Kwastan, Ministan Tsaro da Mai ba Shugaban kasa Shawara kan tsaro. Akwai Shugaban Ma’aikatan Najeriya, Shugaban Kotunan Najeriya, Shugaba Hukumar Hana Zamba da Almundahana, Shugaban Hukumar Zabe ta kasa, ga gwamnoni 19 ’yan Arewa ne. Wadannan duk kadan ke nan muka ambata.
To, in dai yanzu Arewa tana da irin wannan gata, to me ya ja mata irin wannan halin na wahala da rashin mafita? Me ya sa ake yi mata bi-ta-da-kulli a bayyane muna ji muna gani? Me ya sa aka maida yankin Arewa bora wasu yankunan mowa, duk a idonmu? Me ya sa aka kasa tsare mana yankinmu, ake ta kasha mu, kowa na ji na gani? Me ya sa tattalin arzikinmu sai rushewa yake yi kullum? Tambayoyin nan ba su da iyaka. Amma magana ta gaskiya ga talakawa da shuwagabannin Arewa, mu sani cewa Arewa na cikin hali na halaka, talauci, yunwa, jahilci, zaman banza, rashin tsaro, duk sun mamaye yankin.
Gaskiya shuwagabanninmu ya kamata ku juyo ku dubi gida, ku tuna irin wahalar da su Sardauna suka sha wajen gina yankin nan, to shi ne ku za ku bari bakin wuta ya mutu a hannunku? In kuwa kuka bari hakan ta faru, wallahi tarihi ba zai taba yafe muku ba.
Muna yi muku tuni da maganar Malam Aminu Kano da ya ce: “kasa daya al’umma daya amma in dare ya yi kowa ya san gidan ubansa.” Gaskiya yanzu kam dare ya yi, ya kamata ku dawo gida ko ma kwana muna shawara, mu ga ta yaya za mu sama wa yankinmu na Arewa mafita kafin yaki ya ci mu.