Wai shin me ke damunmu ne?

Wannan tambaya ce da na dade ina yi wa kaina, sa’annan jama’a da dama sun sha yi man makamanciyar irin wannan tambaya. An sha tsare ni ko dai fuska-da-fuska ko ta waya ko sakon imel ko Facebook domin fayyace amsoshin irin wadannan tambayoyi. Wani zai tambaya wai me ke damun tattalin arzikin kasar nan? Wasu […]

Wai shin me ke damunmu ne?
Wai shin me ke damunmu ne?

Wannan tambaya ce da na dade ina yi wa kaina, sa’annan jama’a da dama sun sha yi man makamanciyar irin wannan tambaya. An sha tsare ni ko dai fuska-da-fuska ko ta waya ko sakon imel ko Facebook domin fayyace amsoshin irin wadannan tambayoyi. Wani zai tambaya wai me ke damun tattalin arzikin kasar nan? Wasu kuma su ce me ke damun’yan siyasar kasar nan?A wani bangaren kuma ka ji ana tambayar me ke damun shugabannin kasar nan? Ba nan ne kadai aka tsaya ba, na sha jin jama’a na tambayar wai me ke damun malamai da shugabannin mujami’un kasar nan? Ko kuwa me ke damun talakawa ko matasan kasar nan? Haka na sha jin tambayar da ke cewa me ke damun ’yan kwangilar kasar nan ko kuwa ma’aikatan kasar baki daya. Wasu ma na ji suna tambayar wai me ke damun kasarmu Najeriya?
A duk lokacin da na ji ana yin irin wadannan tambayoyi, nakan so na amsa, amma sai na fahimci cewa ai kila ba ni ya kamata in amsa irin wadannan tambayoyi ba, ganin cewa yawancin abubuwan da ake son sanin amsarsu, ba ni suka shafa ba, to, amma da yake ina daga cikin daidaikun mutane a cikin kasar nan da ba su ganin zare sai sun tsinka ko kuma wadanda ba su ganin jariri a bayan uwarsa sai sun tambayi wane ne mahaifinsa, ya jawo ake mani irin wadannan tambayoyi ko kuma ni kaina nake dandakar kaina da su. Ina jin tambayar da zan iya amsawa ba ta wuce ta karshe ba, wai me ke damun kasarmu Najeriya? Amsar kuma ba ta wuce ba abin da ke damun Najeriya ba. kasarmu, Najeriya garau take, ba ta ciwon kai ko masassara ko wani jin jiki, na ba gaira, ba dalili.
Wani zai iya cewa anya kuwa Najeriya kalau take, duba ga irin matsalolin da ke jibge a cikin kasar? Talauci, yunwa, tashin-tashina, fashi da makami, fyade, sata, ta sarari da ta boye, cin hanci, rashawa, karuwanci, yake-yake da ludu da madigo, kai ga dai abubuwa nan bilahaddin da ke dambare a cikin kasarmu Najeriya. Dukkan wadannan matsaloli ba Najeriya suke damu ba, mu suke damu ’yan Najeriya, domin mu, mutanen da ke cikinta suke wa tarnaki da ci wa dudduge wajen gudanar da lamurran rayuwa ta yau da kullum, ba Najeriya. Ke nan tambayar da ta dace mu nemi amsar ta ita ce wai me ke damun mu ’yan Najeriya?
Abubuwa da dama ke damun ’yan Najeriya a halin yanzu, sai dai bisa ga dukkan alamu ’yan Najeriyar ma ba su san inda damuwar take ba, kila saboda tsananin damuwa da rashin sanin makama. Mu soma da matsalar shugabancin kasar nan, da yawa daga cikinmu za ka ji suna fadar ai al’amurran kasar nan sun rincabe, shugabanninmu barayi ne, ’yan siyasa, ’yan tsiya ne. Haka za ka ji ana ta fada cewa ai kansila ba wanda ya kai shi rainin wayo, da ka zabe shi ba ka kara jin duriyarsa, sai wani zaben ya zo. Haka ciyaman ko dan majalisar jiha ko ta tarayya ko gwamna ko minista ko shugaban kasa, babu na kwarai daga ciki. Ba abin da muke yi sai Allah-wadai da Allah-tsine, kai ka dauka da zarar mun samu damar da za mu kori wadannan ’yan tsirarun shugabanni za mu yi amfani da ita yadda ta dace, amma, ina! Da zarar aka samu musayar Murtala ko uwa-uba Mai Bornu da Isong, duk sai rawar ta canja. Mu ne kuma za ka ga muna biye da lalatattun shugabannin nan da kullum muke zagi da tsinewa. A yanzu, ba wasu da suka fi su, domin suna ba mu Naira da za mu yi cefane, idan sun kwana biyu ba su ce mana uffan ba, sai kuma mu dawo gare su da wasu bace-bacen da ba su taba jin irinsu ba. A cikin irin wannan yanayi, dole mu tambayi kanmu, shin wai me ke damunmu ne da ba mu iya maganin irin wadannan azzaluman shugabanni? Me ke sa mu kasance tamkar rakumi da akala a hannun wadannan tatattun, bijirarrun shugabanni da muke kyama?
Wasu za su iya ce da ni ai duk inda talauci ya yi katutu a cikin zukatan al’umma, to, shugabannin sun samu damar da za su rika daka talakawa a cikin turmi suna kirbewa, kamar sakwara, ba abin da wani zai iya yi! Wa ya ce haka? A wane Hadisin ko ayar Alkur’ani aka tabbatar da haka? Wa ya sa wa talakawa talaucin da har yau ba su iya gane gabas, bare su yi Sallah? Ina ce su dai shugabannin nan ne da muke bautawa a kullum rana su ne ummulhaba’isin halin da talakawan ke ciki! Su ne suke shake da dukiyar al’umma, ta koma tasu ba ta al’umma ba! Su ne ke sa a yi, ko a bari, ba tare da bin ka’idoji ba a yawancin lokuta, kuma a irin wadannan yanayi, matsaloli ba sa shafarsu ko shafar na kusa da su, sai dai su wadannan da ke cikin tasku a kullum rana ta Allah, wato talakawan nasu! Nan kuma laifin na wane ne, na shugabannin ne ko na talakawan da ba su iya bambance barcin makaho? Me ke damun talakawan Najeriya ne da kiri-kiri suna ganin alamun shedana tare da shugabanninsu, amma su yi ta masu maraba, ga annabawa sun bayyana? Me ke damun talakawan Najeriya ne ta yadda da zarar sun sami na shan koko, sai su bar shugabannin kasar su sace dukkan dukiyar da za a yi musu ayyukan ci da ita gaba ko sa ’ya’yansu makaranta ko gyara tattalin arzikin kasa? Me ke damun talakan Najeriya ne, ko dai hauka ne ya yi musu katutu?
Hauka mana, domin kuwa ba yadda zan zabi mutum zuwa ga mukamin da zai wakilce ni da sauran al’umma, amma ya yi kemadagas ya haye ruwan dukiyar da tawa ce da sauran al’umma, in yi shiru, ba katabus! Wane irin hauka ne wannan?
 
Za mu ci gaba