Wai shin me ke damunmu ne (2)?
Idan muka dage da cewa talakawa ne kadai ke da wannan irin hauka ko kuma su ne ke cikin kogin irin wannan sansamin hauka, to, ba mu yi wa kanmu adalci ba. Ba wani abu ya sa na fadi haka ba sai ganin cewa, ai su kansu shugabannin da masu dukiyar kasar tamu da kuma […]
Idan muka dage da cewa talakawa ne kadai ke da wannan irin hauka ko kuma su ne ke cikin kogin irin wannan sansamin hauka, to, ba mu yi wa kanmu adalci ba. Ba wani abu ya sa na fadi haka ba sai ganin cewa, ai su kansu shugabannin da masu dukiyar kasar tamu da kuma su kansu ’yan boko da malamanmu na kowane irin bangare na rayuwa, su ma dai mahaukatan ne ko kuma masu kama da su.
Wannan ikirari ba ya bukatar dogon nazari ko bin diddidgi, domin kuwa ga shi nan muna gani karara a cikin rayuwarmu ta yau da kullum. Wasu za su iya cewa ai an kwashi batun da fadi, idan har muka ce akwai mahaukata masu yawan gaske haka a cikin kasar nan, kama daga cikin mahukunta ko shugabanni ko tajirai ko ’yan boko da malamanmu, to, an mayar da kasar jamhuriyar mahaukata ne. Idan muka hada wadannan mahaukatan da kuma mahaukatan talakawan da muka yi bayani kansu a baya, za mu iya cewa ina amfanin badi ba rai, me ya bambanta hasashen da abin da ke wanzuwa a zahiri? Abin da kurum ya rage shi ne a kara bincike da kuma nazari. Wannan tattaunawa da muke yi, na daya daga cikin fagen nazarin.
Idan ba mu manta ba, a wasu shekaru da suka wuce nan baya kadan, Farida Waziri, jami’ar da ta rike kujerar shugabancin Hukumar EFCC ta taba irin wannan zance, amma yawancin mutane sun dauka cewa ba ta san abin da take yi ba ne shi ya sa, musamman da ta yi nuni da cewa yawancin masu satar dukiyar kasar nan, a kowane bangare na rayuwar yau da kullum, ba su da isassa a cikin kwalwarsu, ko kuma a takaice mahaukata ne, suna bukatar ganin likita, don a duba su. Ta kuma kara da cewa idan da so samu ne, kafin a nada mutane bisa kujerun shugabanci, ya dace likitan mahaukata ya duba lafiyarsu, ya tabbatar da wadatuwar kwakwalwarsu, kafin su hau kujerun shugabancin.
A nan ba wai satar ce ke da ciwo ba kamar yadda Farida Waziri ta nuna, a’a, yadda satar take kere tunanin mutane da kuma yadda take kara tabbatar da cewa ba masu hankali ke yin ta ba. Alal misali, ina hankali ga wanda ya sace dukiyar karamar hukumarsa, a matsayin Ciyaman ya je wani gari ko wata kasa ya gina gidajen haya ko sayen filaye da ba abin da zai yi da su, sai dai a ce shi ma ya haye? Irin wannan Ciyaman shi ne zai shigo cikin kasarsa, yana tokabo da tinkaho, ana kada masa begila da ganguna da hura masa sarewa da yi masa kirari, ya kuma zauna lafiya da mutanen karamar hukumarsa. Wane ne ke da hankali cikin su biyun Ciyaman ko talakan?
A cikin kasar nan mun ga yadda dan talaka ke tashi cikin kuncin talauci da damuwa, a nada shi kwamishina ko wani mukami irin wannan, ya zama hamshakin mai tarin dukiya, shi ne da shiga jifa-jifai na gani da fada, alhali gidansu da makwabta da wasu na kusa da shi suna rayuwar hannu- baka-hannu-kwarya, shi ba abin da ya dame shi, in dai ya hau tudun ‘mun tsira.’ Wane irin hankali ke ga irin wadannan mutane?
Haka za ka ga irin wannan fasalin rayuwa a tsakanin gwamnoni da ministoci da wasu mukarrabansu, ba abin da suke yi sai sata da facaka da abin da suka sata, ba tsoro ba wata fargaba. Amma abin tayar da hankali shi ne, me ake da dukiyar da aka sata? Me take kara wa wanda ya yi satar, ko za ta iya kara wa wanda ya yi satar? Wane irin tunani ke tattare da irin wadannan masu tekun dukiya da suka kwaso daga baitulmalin al’umma? Nan ne rashin hankali ke fitowa fili, karara!
Bincike ya tabbatar da cewa yawancin masu sayen gidaje da filayen kawa da ji da fada a Amurka ko Turai ko Dubai ko Afirka ta Kudu ’yan Najeriya ne, kuma daga cikin wadanda suke wandaka da dukiyar al’umma. Su din ne ake cewa mun zaba domin su mulke mu ko su wakilce mu, amma sun zare dukiyar, sun gina kansu. Mukarraban fadar Shugaban kasa ko na kusa da Shugaban kasar ko ministoci ko gwamnoni na da, da na yanzu da wasu na kusa da su da suka saci dukiyar al’umma su ne ke sayen gidaje 10 zuwa 20 a irin wadannan wurare. Su ne da sayen manya-manyan otel-otel a sassan duniya daban-daban. Su ne da sayen filaye domin gina fadoji na fada-a-ji a biranen Amurka da Turai da Dubai da Afirka ta Kudu. Su ne da manyan jiragen sama na shiga da yawace-yawace a sassan duniya. Su ne da kamfanonin motocin shiga da iyalansu. Su ne da hannun jari masu tsoka a yawancin kamfanoni da bankunan ciki da wajen Najeriya. Su ne ko’ina da ina! Idan ka tsaya lissafa irin tarin dukiyar da suka turmushe sai ka buga littattafai masu yawa, amma hankalin irin wadannan mutane ba ya tare da su, domin ba su san inda rana ke fitowa ko faduwa ba.
A irin wannan yanayi da kuma ganin irin wadannan mutunen da suka kai shekara 60 zuwa 70 ko 80 a doron kasa, ga shi kuma sun tada kai da bilyoyin Daloli ko tiriliyoyin Nairori, sai abin ya cunkushe maka tunani. Nan take za ka fara tambayar kanka, me irin wadannan mutane suke nema a rayuwa da ba za su iya taimaka wa wadanda suka gaza ba daga tarin dukiyar da suka tara ko sato? Me ke damunsu ne da sadaka ko taimakon gajiyayyu ba ya tare da su, sai handama da babakere? Me ke damun irin wadannan mutane da suke kusa da kabari, amma kullum rana ta Allah, tunaninsu na inda za su samu kwabo ko za su kara samun mulki da danne hakkokin jama’a? Me ke damun irin wadannan mutane ne in ba hauka ba?
Daga karshe nake karewa da cewa, wai shin me ke damunmu, mu kuma da ke biye da su muna maula da roko da sake biye musu a kullum su ci gaba da taushe mu da wahalar da mu ko ci gaba da sace kudade da arzikin kasa, ba ma komai sai murmushi da dariya da yake…..muna ta faman Allah na nan?