Wainar da aka toya a bikin …

Alkawarin taimaka wa KannywoodDaga nan Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abdullahi Ganduje wanda ya wakilci gwamnan Kano ya gabatar da jawabi, inda ya yi alkawarin gwamnatinsu za ta ci gaba da ba harkar fim gudunmuwa don ta ci gaba da tsayawa da kafafunta.Ya ce: “Gwamnatin Jihar Kano ta yi alkawarin taimaka wa harkar fim don […]

Wainar da aka toya a bikin …

????????????????????????????????????

Alkawarin taimaka wa Kannywood
Daga nan Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abdullahi Ganduje wanda ya wakilci gwamnan Kano ya gabatar da jawabi, inda ya yi alkawarin gwamnatinsu za ta ci gaba da ba harkar fim gudunmuwa don ta ci gaba da tsayawa da kafafunta.
Ya ce: “Gwamnatin Jihar Kano ta yi alkawarin taimaka wa harkar fim don ta ci gaba da tsayawa da kafafunta. A cikin shirin gwamnatin Jihar Kano na bunkasa harkar fim ne ya sanya ta kirkiro da kauyen daukar fim, ta kuma samar da kayan ayyukan da ake bukata. Gwamnatin jihar ta yi odar kayan aikin fim daga Indiya.”
Fina-finan gyara tarbiyya
Bayan nan sai Gwamnan Jihar Kaduna Mukhtar Ramalan Yero ya gabatar da jawabi inda ya nemi ‘yan fim su karkata akalarsu kan fina-finan gyara tarbiyya.
“Za mu yi bakin kokarinmu wurin taimaka wa harkar fim, ina fata ‘yan fim za su rika girmamam junansu, su kuma zauna lafiya, sannan ina fata za ku karkata akalarku kan fina-finan gyara tarbiyya, a karshe ina fata matasa za su daina shaye-shaye domin babu inda hakan zai kai mutum sai halaka.” Inji Gwamnan.
Nishadi
Daga nan sai aka gayyaci jaruma Nafisa da tawagarta inda suka nishadantar da taron da wakar ‘Basaja’ da Personally’.
An karrama tsofaffi a harkar fim
Bayan nan sai aka karrama mutanen da suka samu nasarori a harkar fim wadanda suka hada da Umar Pategi (Samanja) da Ibrahim Mandawari da Hamisu Lamido Iyan-tama da Sani Mu’azu Jos da Abdulkareem Muhammad da kasimu Yero da kuma Abdu Kano (Karkuzu).
Daga nan aka rika karrama ‘yan fim da suka samu nasara a matakai daban-daban.
korafe-korafe
An ji masoya mawaki Nura M Inuwa suna tayar da jijiyar wuya cewa babu mawakin da ya yi ruwan wakoki masu ma’ana da fadakarwa da nishadantarwa da kuma ilimantarwa kamar mawakinsu, amma a ce bai samu kyauta ba. Sai dai mawakin ya ce haka Allah Ya kaddara.
Wata majiya ta bayyana wa wakilinmu bai kamata a shiga gasar da fim din ‘Kicimilli’ ba, tun da kotun tafi da gidanka ta hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano ta ci tarar furodusan fim din kan fitar da fim din ba tare da an tace ba, sai dai daya daga cikin alkalan gasar ya ce ai jarumin fim din aka zaba ba wai fim din ko furodusan ba.
Wata majiya ta ce a duk rukunan da aka kawo babu na gwarzon furodusa.
Da yawa daga cikin wadanda suka halarci bikin sun ce dakin  taron da aka gudanar da bikin ya yi kadan, sannan kudin shigar da aka sanya Naira dubu daya ya yi kadan. Wani ya ce kamata ya yi a yi taron a dakin taro na Sport Indoor.
Shugaban kwamitin gudanar da taron Alhaji Hamisu Lamido Iyantama ya ce dan Adam  tara yake bai cika goma, kuma wannan ne karo na farko da suka gudanar da irin wannan bikin. A karshe ya yi alkawarin za a samu canji a nan gaba.
An kammala taron da karfe 2:32 na dare.

Ado Ahmad da Rabilu Musa Ibro a wurin bikin

Ali Nuhu da abokinsa dan Indiya Nilesh Nipane ma’aikacin Kamfanin Media Trust masu buga jaridar Daily Trust da Weekly Trust da Sunday Trust da kuma Aminiya da kuma Lawan Ahmad a wurin bikinSahura da Baban Chinedu da Maryam Pantimoti da Maryam Sangandali a wurin bikin	Jerin sunayen ‘yan fim da fina-finan da suka samu nasara:

Gwarzon jarumi:             Ali Nuhu da fim din ‘Matan Gida’

Mai tallafa Gwarzon Jarumi:         Zaharaddeen Sani da fim din ‘Fulani’

 Gwarzuwar Jaruma:             Nafisa Abdullahi da fim din ‘Ahlil Kitabi’

Mai Tallafa wa Gwarzuwar Jaruma:     Ladi Muhammad (Mutu-Ka-Raba) da fim din                             ‘Kicimilli’

Gwarzuwar Jaruma mai Tasowa:         A’isha Tsamiya da fim din ‘Matan Gida’

 Gwarzon Jarumin Barkwanci:         Rabi’u Ibrahim (Daushe) da fim din ‘Aliya’

Gwarzon Darakta:             Aminu Saira da fim din ‘Wata Hudu’

Gwarzon Jarumi mai tasowa:         Adamu Ushere da fim din ‘Gidan Dadi Duniya’

Labari:                 Ilyasu Abdulmumini da fim din ‘Daga Allah Ne’

Tsara Labari:                 Yakubu M Kumo da fim din ‘Daga Allah Ne’

Tsara wurin daukar fim:         Sayyadi Garba da fim din ‘dan Marayan Zaki’

Siddabaru:                 Aliyu Musa Danjalo da fim din ‘Ta’addanci’

 Murya:                 Kabir A Zango da fim din ‘Jarumin Maza’

Tufafi:                 Aminu One Eye da fim din ‘Wani Gari’

Hoto:                     Yassin Auwal da fim din ‘Wani Gari’

daukar fim:                 danlami Ali da Isma’il M Isma’il da fim din ‘Ta’addanci’

Mugunta:                 Tanimu Akawu da fim din ‘Jarumin Maza’

Gwarzon Edita:                 Saddam M Koli da Adam A Zango da fim din                             ‘Ta’addanci’

 Kida:                     Adam Zango da fim din ‘Basaja’

Rubuta Waka:                 Sadi Sidi Sharifai da fim din ‘Daga Allah Ne’

Gwarzon Mawaki:             Yakubu Mohammed da wakar fim din ‘Gani-Gaka’

Gwarzuwar Mawakiya:             Zuwaira Isma’il da wakar fim din ‘Wata Hudu’