Wainar da aka toya a bikin karrama ’yan fim a Kano

A ranar Asabar da ta gabata ne aka gudanar da bikin karrama ‘yan fim wanda Kamfanin sadarwa na MTN ya dauki nauyi. Aminiya ta kawo muku wainar da aka toya a wurin bikin. A sha karatu lafiya. dakin taro na Afficient da ke lamba 42 a titin Sultan a Nasarawa GRA, Jihar Kano ya yi […]

Wainar da aka toya a bikin karrama ’yan fim a Kano

A ranar Asabar da ta gabata ne aka gudanar da bikin karrama ‘yan fim wanda Kamfanin sadarwa na MTN ya dauki nauyi. Aminiya ta kawo muku wainar da aka toya a wurin bikin. A sha karatu lafiya.

dakin taro na Afficient da ke lamba 42 a titin Sultan a Nasarawa GRA, Jihar Kano ya yi cikar farin dango da ‘yan fim da masu ruwa da tsaki a harkar fim da kuma masoya harkar a ranar Asabar da ta gabata.
Ali Nuhu ne Gwarzon jarumi da fim din ‘Matan Gida’, sai Nafisa Abdullahi Gwarzuwar Jaruma da fim din ‘Ahlil Kitab’. Aminu Saira shi ne Gwarzon Darakta da fim din ‘Wata Hudu’, inda fim din ‘Wani Gari’ ya lashe kyautar Gwarzon Fim.
Fara taro ba tare da addu’a ba
Zaharaddeen Sani yake karvar kyautar Mai Tallafa wa Gwarzon Ado Ahmad Gidan Dabino yake mika wa Ali Nuhu kyautar Gwarzon Jarumi Aminu Saira yake karbar kyautar Gwarzon DaraktaAn fara gudanar da taron ne da karfe takwas da rabi na dare inda jarumi kuma mawaki Abbas Sadik ya fara nishadantar da taron da wakarsa mai suna ‘Abbasi’. Yadda jama’a suka rika amshi ne ya tabbatar da wakar ta ratsa su. Bayan ya kammala ne aka gayyato mawaki Muddansiru Kassim ya nishadantar da mahalarta taron da wakar ‘Baiwa’ da kuma ‘A Sha Rubutu’. Bayan ya sauka ne sai Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Mukhtar Nafisa Abdullahi take karbar kyautar Gwarzuwar JarumaRamalan Yero ya ja hankalin Shehu Hasan Kano daya daga cikin masu gabatar da taron cewa, an fara taro ba tare da an yi addu’a ba. Hakan ya sanya aka kira Shugaban kungiyar ‘yan fim ta Arewa Film Makers Association of Nigeria, Alhaji Isma’il Na’abba AfakAllah ya bude taro da addu’a.
Harbe-harben da sojoji suka yi  
Kilomita biyu kafin a isa dakin taron ta kowace kusurwa babu abin da ake gani sai jami’an tsaro suna muzarai. Hakan ya sanya ba zato bare tsammani bayan an kammala addu’a sai aka rika jin harbe-harbe na tashi, hankali jama’a ya tashi. Bayan wakilinmu ya bincika ne sai ya gano cewa mahalarta taron ne suka rika gogoriyo har suka fasa kofar da jami’an tsaro suke. Jama’a da yawa sun samu raunuka. Aliyu dalhatu wakilin gidan rediyon BRC da ke Jama’are wanda a lokacin da yake kofar shigowa al’amarin ya faru, ya shaida wa wakilinmu cewa bai san lokacin da ya rika tafiya da gwiwa ba saboda razana har ya yayyaga wandonsa ba. Wata majiya ta ce jami’an tsaro sun yi wa fitaccen mawakin nan Rara wanda ya yi wakar ‘Ba Da Ni Ta bare Ba’ bulala, wakilinmu ya nemi jin ta bakinsa amma abin ya ci tura, duk da haka lokaci jami’an tsaro suka shawo kan al’amarin.
Bikin Arewa ne ba na Kannywood ba
Bayan komai ya natsa ne sai Dokta Ahmed Sarari wanda shi ne kodinetan bikin karramawar ya yi jawabin maraba da baki inda ya ce biki ne na Arewa ba wai na ‘yan fim kawai  ba.
Ya ce: “Wannan biki ne da aka tsara shi don ci gaba masana’antar fim ta Kannywood. Kannywood ta fi kowace masana’anta a Arewa samar da aikin yi. Wannan biki ba nawa ko na AfakAllah ko Iyantama ko Alkanawy ba ne, biki ne na ‘yan Kannywood, don haka yana fata kowane dan Kannywood zai kasance cikin farin ciki marar misaltuwa. Kodayake biki ne na Arewa.”
Ya ce, wannan gasar kamar kwallon kafa ne dole a yi nasara ko a fadi, wanda ya yi nasara sai ya yi murna, wanda ya fadi kuma ya yi hakuri, wannan bikin yanzu aka fara domin za a ci gaba da yi kowace shekara.  A karshe ya yaba wa kamfanin MTN bisa daukar nauyin bikin.
korafin Gwamnan Kaduna
Bayan nan ne sai aka lissafo wadanda suka raini masana’antar hade da ba ta babbar gudunmuwa. Wadannan mutanen sun hada da Ibrahim Mandawari da Bashir Mudi Yakasai da marigayi Tijjani Ibrahim da Ishak Sidi Ishak da Hajiya Balaraba Ramat da Ado Ahmad Gidan Dabino da Bala Anas Babinlata da dan Azumi Baba da Auwal Muhammad Sabo da Abdullahi Sani Abdullahi (Baba karami) da sauransu.
Ana cikin haka sai Gwamnan Kaduna Mukhtar Yero ya ce ba a kyauta ba, domin ya ji an ambaci wadanda suka ba da gudunmawa amma a ciki babu ‘yan Kaduna.
Kamfanin MTN zai ci gaba da daukar nauyin bikin
Daga nan sai Babbar Manajar Kasuwanci ta Kamfanin MTN ta Arewacin Najeriya, Hajiya Amina Usman ta gabatar da jawabi, inda ta ce ta yi farin ciki da ta halarci wannan biki mai matukar tarihi, domin yadda ta dauki Kannywood ashe abin ya wuce haka, domin yadda ta ga dakin taron babu masaka tsinke.
“Ta yi farin ciki da kamfanin sadarwa na MTN ya zama kamfani na farko a tarihi da ya dauki nauyin gudanar da wannan biki. Tun kafin zuwan Turawa Arewa tana da kashi 60 cikin 100 na yawan ‘yan Najeriya, kuma suna da al’adu kyawawa masu daukar hankali. Harkar fim a Arewa ta bunkasa ta kai wani matsayi da yanzu za a iya cim ma kowane buri a harkar. MTN za ta ci gaba da daukar nauyin bikin.” Inji ta.
Nishadi
Masu iya magana sun ce taba kidi taba karatu. Bayan Hajiya Amina ta kammala jawabinta ne sai aka kira Ali Nuhu da Rahma Sadau (Priyanka) suka nihadantar da taro da wakokin Umar M. Shariff masu suna ‘Jinin Jikina’ da kuma ‘Madubin Dubawa’.              Karramawa
An karrama Gwamnan Kaduna Mukhtar Ramalan Yero da kyautar zaman lafiya. Haka an karrama Gwamnan Kano da mataimakinsa.
Nishadi
Daga nan aka kira jarumi Sani Danja ya nishadantar da taro da wakar ‘dan Zaki’. Hakan ne ya sanya wuri ya hargitse, jama’a suka rika takawa hade da bin wakar.