Wainar da aka toya a manyan wasannin Firimiyar Ingila

Ramsey ya mayar da martani, inda bayan hutun rabin lokaci ya lafta wa United kwallo a raga.

Wainar da aka toya a manyan wasannin Firimiyar Ingila

A ranakun Asabar da Lahadi ne manyan kungiyoyin kafar Ingila suka fafata a wasannin mako na 14 na gasar Firimiyar Ingila ta bana.

Arsenal ta koma saman teburin gasar Firimiyar Ingila bayan da ta doke Chelsea da ci daya mai ban haushi a Stamford Bridge a ranar Lahadi.

A cikin minti na 63 ne Gabriel ya saka kwallo a raga bayan da Chelsea mai masaukin baki ta gaza tare kwallon da Bukayo Saka ya kawo daga bugun kusurwa.

Arsenal dai ta samu damammakin cin kwallaye a zubin farko na wasan, inda Martinelli da Gabriel Jesus suka barar da su.

Chelsea, wanda tsohon dan wasan Arsenal da ta sayo, Pierre-Emerick Aubameyang ya gaza tabuka abin kirki a wasan na ranar Lahadi, inda sau takwas kawai ya taba kwallo har aka tafi hutun rabin lokaci.

’Yan wasan Chelsea sun yi ta kokari abin ya ci tura, kuma yanzu haka wasanni 4 na gasar Firimiya kenan suka buga a jere ba tare da nasara ba.

Manchester City da Fulham

A ranar Asabar ce Arsenal ta rasa matsayinta na jan ragamar teburin gasar Firimiya, bayan da Manchester City da ta karkare wasanta da mutane 10 ta samu nasarar doke Fulham da ci 2-1.

Tun a minti na 16 Julian Alvarez ya jefa wa City kwallonta ta farko, daga bisani kuma murna ta koma ciki bayan Fulham ta farke a minti na 28 ta hannun Andreas Pereira.

Ana zuwa minti na 26 aka daga wa Joao Cancelo jan kati, wanda ya sanya City ta rika lallabawa har aka kai mintin karshe.

Saura kiris a tashi wasan ne Erling Halaand ya kalatowa City martaba bayan kungiyar ta samu bugun daga kai sai mai tsaron raga, kuma bai yi wata-wata ba ya yi amfani da damarsa.

Manchester United da Aston Villa

Unai Emery ya fara horar da Aston Villa da kafar dama, inda ’yan wasansa suka lallasa Manchester United da ci 3-1 a Villa Park.

Masu masaukin bakin ba su taba doke Manchester United a gidansu ba a gasar Lig tun bayan shekarar 1995, amma sai gashi a wannan wasa sun ci kwallaye 2, United babu ko daya, bayan mintuna 11 da soma wasan da karsashi.

Leon Bailey ne ya fara cin kwallo a minti na 7 da fara wasa inda da ya fasa bayan United kafin ya antaya wa mai tsaron raga, David de Gea ita a raga.

Lammura sun dada yi wa Villa kyau bayan mintuna 3 kacal, a yayin da Lucas Digne ya saka wata kwallo ta bugun tazara daga yadi na 25.

Manchester United sun yunkuro, inda Luke Shaw ya samu ya ci musu kwallo daya, bayan da ta daki jikin Jacob Ramsey.

Amma Ramsey ya mayar da martani, inda bayan hutun rabin lokaci ya lafta wa United kwallo a raga, kuma a haka aka tashi wasa 3-1.

Liverpool da Tottenham

’Yan kallo 62,008 ne suka halarci wasan da Tottenham ta karbi bakuncin Liverpool a ranar Lahadi.

Andrew Madley ne ya yi alkalancin wasan da Liverpool ta lallasa mai masaukin bakin da ci biyu da daya.

A minti na 11 da kuma na 40 ne Mohammed Salah ya jefa kwallaye biyu da ya ci wa Liverpool a wasan, sai dai Harry Kane ya farke kwallo daya a minti na 70.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno