Wainar da ake toyawa a yakin Rasha da Ukraine

Kwana 13 da fara rikicin, farashin danyen mai ya haura Dala 130 a kasuwar duniya

Wainar da ake toyawa a yakin Rasha da Ukraine

Wasu dakarun Rasha a Ukraine

Yakin Rasha da Ukraine, wanda shi ne mafi muni a nahiyar Turai tun bayan Yakin Duniya na biyu ya yi sanadin tserewar mutum sama da miliyan biyu daga Ukraine.

A cikin kwana 13 da fara rikicin, farashin gangar danyen mai ya haura Dala 130 a kasuwar duniya a yayin da aka samu rabuwar kai tsakanin kasashen Yammacin Duniya kan kaurace wa sayen makamashi daga Rasha.

Ga karin wainar da ake toyawa a kwana 13 bayan fara yakin a Ukraine:

– Aikin jinkai a Ukraine –

Rasha ta sake bude kofar ayyukan jinkai don ba wa fararen hula damar ficewa daga yankunan da sojojinta suka mamaye a Ukraine.

Ukraine da kawayenta sun yi watsi da tayin Rasha na kwashe fararen hular Ukarine zuwa kasarta, suna masu cewa kinibibin siyasa ne; Suna zargin sojojin Rasha da tarwatsa hanyoyin fita daga Ukraine.

Dubban fararen hula sun fice daga Kyiv, babban birnin Ukraine da kewaye, a kafa, ta wata gadar wucin gadi, dauke da kananayan yara da tsofaffi masu rauni a kan tabarmi.

– ’Yan gudun hijira miliyan biyu –

Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ce sama da mutum miliyan biyu ne suka yi gudun hijira daga Ukraine a cikin kwana 13 da Rasha ta far wa kasar. Ta bayyana cewa wannan shi ne lokacin da aka samu karuwar masu gudun hijira da ba a taba gani ba tun bayan Yakin Duniya na Biyu.

Hukumar Kula da Masu Gudun Hijira ta MDD ta ce daga ranar 24 ga Fabrairu, 2022  da aka fara yakin zuwa yanzu mutum 2,011,312 ne suka tsere daga Ukraine zuwa kasashe makwabta — kasar Poland kadai ta karbi mutum miliyan 1.2 daga cikinsu.

– An kashe mutum 21 a Sumy –

Rasha ta tsananta kai hari a birnin Kharkiv da ke kusa da Kyiv, a Gabashin Ukraine. 

Ta kuma yi luguden wuta a Sumy da ke Arewa Maso Gabas da kuma Chernihiv da ke Arewa, sai kuma Mykolayiv a yankin Kudu Maso Yammacin kasar.

Hukumomi sun ce an kashe mutum 21, ciki har da kananan yara da mata a harin sama a Sumy.

Dubban mutane na rige-rige tserewa daga ta jirgin kasa daga Odessa, garin da ke da babbar tashar jirgin ruwa a Ukraine, wanda Rasha ke far wa da yaki.

– Zelensky ya soki Kasashen Yamma kan saba alkawari –

Shugaban Volodymyr Zelensky na Ukraine ya soki abin da ya kira rashin cika alkawarin da Kasashen Yammacin Duniya suka yi na kare Ukrraine daga hare-haren Rasha.

“Kwana 13 ke nan sai alkawura ake ta yi ji cewa za a taimaka mana ta sararin samaniya da jiragen yaki yankin,” inji Zelensky a sakon da ya tura ta Telegram.

“Alhaki da na wuyan wadanda suka ki yanke hukunci a tsawon kwana 13 a Yammacin Duniya, da ba su kare sararin samaniyan Ukraine daga ’yan ina-da-kisan Rasha.”

– Rasha na daukar ‘Sojojin haya da Siriya’ –

Ma’aikatar Tsaro ta Amurka (Pentagon) ta ce akwai kwararan hujjoji da ke nuna Rasha na daukar sojojin haya daga Siriya, kasar da Rashar ta taimaka wa a 2015 domin kare gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad.

Wani kakakin Pentagon ya ce, “Mun yi amannar akwai kamshin gaskiya a cikin hakan.”

Amma Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin, ya ce ‘kwararrun sojoji’ kasarsa za ta tura zuwa bakin daga.

– Luguden wuta a tashar nukiliya –

Hukumar Kula da Nukiliya ta Duniya (IAEA) ta ce ta samu rahoton cewa makaman atilare sun yi barna a wata cibiyar binciken makamashin nukiliya a Kharkiv, birni na biyu da Rasha ta mamaye a Ukraine.

Sai dai kuma hukumar ta bayyana cewa hakan bai haifar da wata illa ba.

– Baraka kan makamashin Rasha –

Fadar White House ta Amurka ta ce an samu baraka tsakanin kawayenta na Turai kan su kaurace wa sayen danyen mai da iskar gas daga Rasha.

Rasha na barazanar katse iskar gas din da take sayar wa kasashen Turai ta bututunta na Nord Stream 1 a matsayin ramuwar gayya ga takunkumin da Kasashen Yamma suka sanya mata.

– Faransa ta soke taron dan Rasha –

Faransa ta soke wani biki da aka shirya wa wani mai zayyana dan kasar Rasha, Valentin Yudashkin, wanda shi ne ya tsara kakin sojojin kasarsa, saboda a cewar Faransa, bai la’anci yakin kasarsa a Ukraine ba.

– Bankin Duniya zai ba Ukraine kudade –

Bankin Duniya ya ware karin Dala mliyan 489 domin tallafa wa Ukraine nan take.

– Hasashen taurin kan Rasha –

Kamfanin Morgan Stanley na Amurka ya yi hasashen Rasha za ta nuna taurin kai, inda za ta yi amfani da tsarin ‘coupon’ a kan takardun lamunin da za ta bayar a watan Afrilu.

 – Ficewar ’yan kwallo daga Rasha –

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta ba wa ’yan kwallo da masu horas da su ’yan kasashen waje izinin jingine kwantaraginsu a Rasha, su koma wasu kasashen zuwa wani lokaci.

Hukumomin kwallon kafa na duniya sun sanya wa Rasha takunkumi saboda mamayar da ta yi wa Ukraine.