Waiwaye Kan Abubuwan Al’ajabi A Shekarar 2013: Ana ta tafka shari’ar wata ’yar Sudan kan rashin lullube kanta
Wata ’yar Sudan za ta fuskanci hukuncin bulala a kotu, bayan da ake ta tafka shari’a kan keta dokar sutura ta kamala da Gwamnatin Sudan ta kafa tun a shekarar 1989, bayan da aka sameta da laifin rashin lullube kanta. Tun a cikin watan Satumbar bana aka fara shari’ar Amira Osman Hamid, inda lauyyanta ya […]
Wata ’yar Sudan za ta fuskanci hukuncin bulala a kotu, bayan da ake ta tafka shari’a kan keta
dokar sutura ta kamala da Gwamnatin Sudan ta kafa tun a shekarar 1989, bayan da aka sameta da
laifin rashin lullube kanta. Tun a cikin watan Satumbar bana aka fara shari’ar Amira Osman
Hamid, inda lauyyanta ya bukaci a janye tuhumar, amma tunda an gurfanar da ita a gaban kotu,
ana auna yadda ya kamata a ci gaba da wannan shari’a, kamar yadda lauyan Amira suka bayyana a
Jebel Aulia da ke wajen birnin Khartoum.