Waiwaye kan yadda aka dage zaben 2011 da 2015 kafin na 2019

A ranar Juma’ar da ta gaba ce Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta dage babban zaben kasar nan sa’o’i kadan kafin a fara kada kuri’’a wanda hakan ya janyo mutane suka yi ta bayyana ra’ayoyinsu kan lamarin. Hukumar INEC ta bayar da hujjar cewa rashin isar kayan zabe a kan lokaci zuwa wasu wuraren ne […]

Waiwaye kan yadda aka dage zaben 2011 da 2015 kafin na 2019

zaben 2011 da 2015 kafin na 2019

A ranar Juma’ar da ta gaba ce Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta dage babban zaben kasar nan sa’o’i kadan kafin a fara kada kuri’’a wanda hakan ya janyo mutane suka yi ta bayyana ra’ayoyinsu kan lamarin.

Hukumar INEC ta bayar da hujjar cewa rashin isar kayan zabe a kan lokaci zuwa wasu wuraren ne ya sa ta dage zaben.

Wannan ne karo na uku da aka taba dage zabe a Najeriya. Gidan Rediyon BBC ya yi waiwaye kan wannan batu inda muka rairayo tare da  karin bayani:

Zaben 2011: Rashin isar kayin aiki da sauri

A shekarar 2011, Hukumar INEC ta dage zaben Majalisar Dokoki bayan an riga an fara kada kuri’a a wasu jihohi.

Lamarin ya faru ne a ranar 2 ga Afrilun shekarar 2011, ranar da ’yan Najeriya za su zabi ’yan majalisa.

Bayan an fara tantance masu zabe a wasu wuraren, wasu wuraren kuma an fara kada kuri’a, sai kwatsam Shugaban Hukumar a wancan lokacin Farefesa Attahiru Jega ya fito ya bayyana cewa zaben ba zai yiwu ba, saboda kayayyakin zaben ba su isa wasu sassan kasar ba.

A wancan lokacin, Hukumar INEC ta bayar da uzurin cewa, “Wasu abubuwa da ba mu yi tsammani ba wadanda suka hada da kai kayayyakin zabe a makare zuwa wasu sassan kasa, kuma kasancewar har da takardar rubuta sakamakon zabe, wanda kuma shi ne kan gaba wajen tabbatar da ingancin zabe. Wannan lamarin ya sanya dole mu dage zabubbukan Majalisar Tarayya zuwa ranar Litinin, 4 ga Afrilu domin mu kara shiri.”

Daga baya kuma sai aka dage zaben zuwa ranar Asabar, 9 ga  Afrilun 2011, sannan aka dage na Shugaban Kasa zuwa ranar 16 ga Afrilu, sai kuma na Gwamna da ’yan majalisun jihohi ya koma 23 ga watan Afrilu.

2015: Matsalolin tsaro suka sa aka dage zaben

A ranar 8 ga watan Fabrairun shekarar 2015 ne Shugaban Hukumar INEC na wancan lokacin Farfesa Attahiru Jega ya sanar da dage manyan zabubbukan kasar nan, lokacin da ya rage saura kwana shida a gudanar da shi inda ya mayar da zaben ranar 28 ga watan Maris, wanda ya kama karin mako shida ke nan.

Farfesa Jega ya ce ya yi hakan ne saboda matsalar tsaro da ake fuskanta a wancan lokacin.

A wancan lokacin ana tsaka da matsalar rikicin Boko Haram a Arewa maso Gabas, don haka ne hukumomin tsaron kasar nan suka ce rashin isassun dakarun da za su kare masu kada kuri’a a wancan yanki, na daga cikin dalilan dage zaben kamar yadda BBC ya yi waiwaye a kan lamarin.

A wancan lokacin, Shugaba Goodluck Jonathan ya nuna goyon bayansa ga Shugaban Hukumar INEC din.

A hirar da ya yi da sashen Ingilishi na BBC, Shugaba Jonathan ya yi bayani a kan cece-kucen da ya biyo bayan dage zaben inda ya ce duk da yake bai ji dadin abin da ya faru ba, amma yana da kwarin gwiwar cewa Farfesa Jega zai iya sauke nauyin da ke kansa na shirya zabe ingantacce a kasar nan.

Kuma Shugaba Jonathan ya bukaci jama’a su ci gaba da nuna hakuri da juriya, su kuma fito domin yin zaben a sabuwar ranar da aka sanya.

’Yan Najeriya dai a lokacin sun harzuka matuka kan wannan al’amari, inda wadansu suke tunanin kawai wata manakisa aka shirya domin a lokacin da yawa daga cikin mutane suna zargin kawai akwai yiwuwar Jonathan ya shirya magudi ne, don haka yake neman hada baki da Jega da jami’an tsaro.

Zaben 2019: Jinkirin kai kayan zabe

Haka ma a wannan karo, a ranar Juma’ar da ta gabata lokacin da bai wuce saura kimanin sa’a biyar ba a fara kada kuri’a, sai Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar da cewa an dage zaben da mako guda.

Farfesa Mahmood Yakubu ya bayar da sanarwar ce cikin dare da misalin karfe biyu da rabi, lokacin da mutane da dama suke barci da shirin washegari za su tafi layin zabe.

Kwatsam sai da safe mutane suka tashi da labarin cewa an dage zaben, wanda hakan ya sa suke ganin abin kamar almara, wadansu kuma suke ganin abin kamar mafarki

A yanzu dai gobe  23 ga Fabrairu ne za a fafata zaben na bana.

Da yake bayani a kan dalilin hukumar na dage zaben, Farfesa Yakubu ya ce an dage zaben ne saboda “Wasu matsaloli da suka taso dangane da shirye-shiryen zaben, musamman jigilar kayan zabe ta hanyar da za a bude rumfunan zabe a kasar baki daya a tare daga karfe takwas na safe ranar Asabar. Bisa wannan dalili ne hukumar zabe ta yi taro, inda ta dage zaben zuwa 23 ga watan Fabrairu,” inji shi.

Wannan karon dai dage zaben ya fi tayar da kura, domin an yi ta musayar yawu tsakanin bangarori da dama.

Shi kansa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fito fili ya bayyana rashin jin dadinsa kan dage zaben, inda ye ce “Ina shawartar ’yan Najeriya da su guje wa tashin hankali kuma su zama ’yan kasa nagari domin kada su kawo wa dimokuradiyyar Najeriya nakasu,” kamar yadda BBC ya rawaito Shugaba Buhari yana fada.

Haka ma dan takarar Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya nuna rashin dadinsa a kan lamarin.