Waiwaye: Ko za mu yi ta zama karkashin barayi?

  Hukumar ‘EFCC’ ta fito ta gaya wa duniya cewa, shugabannin ikananan hukumomi 774 na Najeriya da gwamnonin jihohi 36 na da, da na yanzu, da mataimakin shugaban kasa da tsohon shugaban mulkin soja duk tana zarginsu da laifin wawushe baitalmalin gwamnati. Shugaban kasa da mataimakinsa suna zargin junan su da laifin wawashe baitilmalin gwamnati. […]

Waiwaye: Ko za mu yi ta zama karkashin barayi?
Waiwaye: Ko za mu yi ta zama karkashin barayi?

 

Hukumar ‘EFCC’ ta fito ta gaya wa duniya cewa, shugabannin ikananan hukumomi 774 na Najeriya da gwamnonin jihohi 36 na da, da na yanzu, da mataimakin shugaban kasa da tsohon shugaban mulkin soja duk tana zarginsu da laifin wawushe baitalmalin gwamnati.

Shugaban kasa da mataimakinsa suna zargin junan su da laifin wawashe baitilmalin gwamnati. Amma ko da zanga-zangar lumana babu wadanda suka nemi a yi domin nuna kyama ga masu irin wannan magun hali. Hatta kungiyoyin kwadago ba ta yi komai ba. Tamkar dukkan ‘yan Najeriya barayi ne sun yarda da mulkin barayi! To, mu, ‘yan jam’iyyar ‘Alliance For Democracy’ (A.D.) muna kira ga duk wadanda ba barayi ba, su zo mu hadu mu kawar da duk wadanda suka tabbata barayi ne daga mulki, a zaben 2007.

Wannan muhimmmiyar kasa tamu, da duk albarkatun da Allah ya ajiye cikinta mallakar dukkanmu ce, ba ta tsirarin barayi da ke cikinmu ba. Ofishin gwamnati, wurare ne na kula da amanar jama’a, ba na sata ba. Ba za mu harde hannuwanmu, mu da ido, a yi ta tsiyata mu ba. Daga rikon amana, su wawushe baitulmalin gwamnati karkaf.  Tilas mu warware hannayenmu, mu tsaya, tsayin daka sai mun kwato amanarmu da ke a hannun duk wanda ya sata. Ni, ban yarda dukkanmu barayi ne,  da za mu yi ta bin barayi a matsayin shugabannin mu ba. Saboda haka muke kira ga duk wadanda ba barayi ba, su shigo A.D. mu hadu mu tsarkake Najeriya. ga wani ya ce shi ne ya bata, shi ne zai gyara, ya yi kirari shi mai laifi ne, sai hukunci. Maraba da ‘EFCC’ a Najeriya!

Duk wanda ya isa a kasar nan an kashe shi babu abin da aka yi, ballantana rusa darajar Naira, babu maganar kwabo an rusa komai an rusa kowa sun kasa cewa komai, saboda su suka fara, aka ci gaba daga inda suka tsaya kafin tasu ta same su. Sune suka gabatar da gicciye (Cross) a katin zama dan kasa a 1989. Karanta Guardian ta ranar Juma’a 4 ga watan Augusta, 1989 da Triumph ta ranar Lahadi 17-9-1989, inda za a ga Babangida ya makala nasa katin mai gicciyen (Cross) sai da Musulmi suka yi masa ca, katin da ba a yi ba ke nan sai a wannan lokacin na Obasanjo shi ma kafin a yi shi sai da aka mayar da gicciyen (Cross) din katin PDP, wannan karon Musulmi suka yi ta rububin sai an ba su, har da rigima da tashin hankali maimakon su yi rigima a cire gicciyen (cross) din. Wa’iyazu Billahi. Allah maganin mai magani, duk sun gama halaka, sun kare a cikin (burma) ta kamun gafiya, ranar fitowa, ranar yankawa. Waye ya ga tantal-ba-tete?

Mun kori ‘yan Afenifere daga A.D. sun koma PDP wurin dan uwansu Obasanjo don su kwashi ganima, har sun yi agar, sun murde zaben dan Arewa sannan suka kori ‘yan Arewa daga PDP. babu makoma ‘yan Arewa ko Are-wawaye? babu makoma daga ACD sai AC, kafin A, sannan O. (Zero) ko hakkin ‘ya’yan talakawa da suka jefa cikin halakar shaye-shayen miyagun ababen sa maye suna ba su makamai da ‘yan kudin kashe kishirwa don su kare su daga abokan hamayya ta ishe su, kuma wata rana su za su afkawa, tunda suna ji ‘EFCC’ tana fallasa su, ballantana ga wadanda aka jefa a halakar da ta fi tasu, suna tare manyan hanyoyi da rantsatsun makamai suna yi wa kowa fashi saboda an hana su hakkinsu na ‘yan kasa?

Ga ‘yan ‘OPC’ can, da ‘Area Boys’, nan ga ‘MASSOB’ da Niger-Dalta duk suna jin abin da ‘EFCC’ take cewa shugabannin kananan hukumomi da gwamnonin jihohi da ‘yan majalisun da tsohon shugaban mulkin soja IBB. Da abin da shugaban kasa da mataimakan sa suke fada wa junansu.

Shi ne muka ga lokacinmu ne ya yi na mu shigo al’amarin tun bai kai ga bacin da ba zai gyaru ba, mu yi maza mu gyara, wanda duk ya daka ta mayaudara munafukai shi ne zai halaka, tare da su. Idan ba munafunci da yaudara ba duk masu yin kuka da mulkin Obasanjo su hadu su roki Allah ya rusa shi, tare wadanda suka kawo shi, da wadanda suka zabe shi, har da wadanda suka zabi Olufalae ma! kowa ya ji cewar dukkan ciyamomi na kasar nan hukumomi barayi ne, gwamnonin jihohi barayi.

Shugaban kasa da mataimakansa sun la’anci junansu da yin sata. Amma a ce ko da zanga-zangar lumana ba a yi ba a kasar, sai ka ce dukkanmu barayi ne? 

Bai kamata a ce dukkanmu, mun yarda da shugabancin barayi ba. Kuma mu fa suke yi wa satar! Hatta kafofin watsa labarai sun fi jirgewa gare su, saboda mulkin, da abin duniya. Talaka ya shiga uku. Duk wadanda suka shirya su fito ga mu, mun hada kai mu gyara a jam’iyyar Alliance For Democracy (A.D.) mai tauraro irin na NEPU, ta lokacin Malam Aminu Kano. Tun da yake sauran jam’iyyun ba za su iya ba, sun kasa saboda rashin shugabanci. Kada ma wani ya yaudari kansa, gyara ba ya yin kansa, sai dai a taru a yi shi, kamar yadda barnar ma ba ita ce ta yi kanta ba, wasu ne suka taru suka yi ta. Haka kuma babu wani abu na gaskiya da adalci, da amana da zai yiwu har sai mutane a kan kansu sun yarda su kiyaye amana, su zamanto adalai, masu gaskiya a tsakanin junansu. Ta haka ne kurum shugabancin da ake bukata zai samu. Kowa ya samu hakkinsa.