Waiwaye: Yadda El-Rufa’i ya rika caccakar Jonathan kan sace ’yan matan Chibok

Ya soki Jonathan kan kin tattaunawa a ceto daliban Chiboki, amma yanzu ya ki tattaunawa don ceto daliban da aka sace sa Jiharsa.

Waiwaye: Yadda El-Rufa’i ya rika caccakar Jonathan kan sace ’yan matan Chibok

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya ce babu sulhu tsakaninsa da ’yan bindiga kuma hukuncin da ya fi dacewa da su shi ne kisa.

’Yan bindigar da a kwanakin baya suka sace dalibai 39 daga Kwalejin Gandun Daje da ke Afaka a Jihar na neman Naira miliyan 500 a matsayin kudin fansa, amma Gwamnan ya kekashe kasa, ya ce ko kwabo ba zai biya su ba.

10 daga cikin dalibai 39 da aka sace din sun kubuta bayan iyalansu sun biya kudin fansarsu ga ’yan bindigar.

Ko a makon jiya, wasu ’yan bindiga sun mamaye Jami’ar Greenfield da ke Jihar suka sace dalibai da dama, amma duk da haka El-Rufa’i ya ce har yanzu yana nan a kan bakarsa ta kin tattaunawa da su don a sako daliban.

Daga bisani ’yan bindigar sun hallaka biyar daga cikin daliban tare da alkawarin ci gaba da kashe su daya bayan daya matukar ba a biya Naira miliyan 800 a matsayin kudin fansarsu ba.

A shekarar 2014, bayan kungiyar Boko Haram ta sace dalibai sama da 200 a Makarantar Sakandiren Gwamnati ta ’Yan Mata da ke Chibok a Jihar Borno, El-Rufa’i na daga cikin wadanda suka fito da babbar murya suna caccakar tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan kan lamarin.

A wancan lokacin, El-Rufai ya ce, “Idan da akwai ’yar Jonathan a cikin daliban da tuni abin ya zama tarihi. Dalilin da kwai ya sa har yanzu ba a kubutar da su ba shi ne saboda ba ’ya’yan wasu ba ne, mun san komai.

“Idan an ce muna siyasantar da lamarin rashin tsaro to me zai hana a je a ceto wadannan ’yan matan sai mu daina siyasantarwar?” inji shi.

Da aka tambaye shi ko yana goyon bayan tattaunawa da ’yan Boko Haram domin kubutar da su sai ya ce, “Ina goyon baya 100 bisa 100.

“Idan rayuwar mutane na cikin hatsari, to kamata ya yi shugaba ya yi dukkan abin da ya kamata ya ceto su. Ya kamata ya saurare su ya ji koke-kokensu.”

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos