Waiwayen Harkokin Wasanni A Shekarar 2013: Gwamnatin Tarayya ta yi wa ‘yan kwallon Super Eagles ruwan Naira

A ranar Talatar nan da ta wuce ne Shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan tare da mukarrabansa suka tarbi ’yan kwallon Najeriya Super Eagles wadanda suka samu nasarar lashe gasar cin kofin Afirka karo na 29 da aka yi a Afirka ta Kudu.Su dai ’yan wasan sun samu nasara ne a wasan karshe bayan sun doke […]

Waiwayen Harkokin Wasanni A Shekarar 2013: Gwamnatin Tarayya ta yi wa ‘yan kwallon Super Eagles ruwan Naira

 Shugaba Goodluck Jonathan rike da kofin Afirka da kungiyar Super Eagles ta lashe a Afirka ta KuduA ranar Talatar nan da ta wuce ne Shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan tare da mukarrabansa suka tarbi ’yan kwallon Najeriya Super Eagles wadanda suka samu nasarar lashe gasar cin kofin Afirka karo na 29 da aka yi a Afirka ta Kudu.
Su dai ’yan wasan sun samu nasara ne a wasan karshe bayan sun doke Burkina Faso da ci 1-0 da hakan ya sa Najeriya ta lashe kofin sau uku bayan shekara 19 rabonsu da daukarsa.
Tun farko Ministan Abuja Sanata Bala Muhammad ne ya tarbi ’yan wasan a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin karfe 1 na rana daga bisani aka zarce da ’yan wasan da jami’ansu fadar gwmanati da ke Abuja inda aka yi musu liyafar karramawa.
Gwamnati ta ba koci Stephen Keshi zunzurutun Naira miliyan 10 sannan ta ba mataimakansa Naira miliyan bibbiyu yayin da daukacin ’yan wasan za su karbi kyautar Naira miliyan biyar-biyar.