Waiwayen Harkokin Wasanni A Shekarar 2013: NFF ta dage kungiyoyin kwallon da suka hada baki aka tashi 67-0 da 79-0 a shiyyar Bauchi

A karshen makon jiya ne aka samu labarin yadda wadansu kungiyoyin  kwallon kafa hudu suka hada baki da alkalan wasa aka tashi wasa da ci 67-0 da kuma 79-0 a shiyyar Bauchi a gasar rukuni-rukunin ’yan dagaji (Amateur).Su dai wasannin an yi su ne a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Bubayero FC da ke Gombe […]

Waiwayen Harkokin Wasanni A Shekarar 2013: NFF ta dage kungiyoyin kwallon da suka hada baki aka tashi 67-0 da 79-0 a shiyyar Bauchi

Alhaji Aminu Maigari, Shugaban Hukumar NFFA karshen makon jiya ne aka samu labarin yadda wadansu kungiyoyin  kwallon kafa hudu suka hada baki da alkalan wasa aka tashi wasa da ci 67-0 da kuma 79-0 a shiyyar Bauchi a gasar rukuni-rukunin ’yan dagaji (Amateur).
Su dai wasannin an yi su ne a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Bubayero FC da ke Gombe da kuma ta Plateau FC Feeder Team da ke Jos, a yayin da kuma aka yi wasa na biyu a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Akurba United FC da ke Nasarawa da kuma Police Machine da ke Adamawa.  Wasannin sun gudana ne a shiyyar Bauchi.