Wajibcin girmama Makka da Madina ga mahajjata (2)

Fassara Abubakar Hamza Ibn Kayyim (Allah Ya yi masa rahama), ya ce: “Yin mummunan laifi a Harami da kasar Harami (Makka) da kuma a kan shimfidar Allah (Masallaci) ya fi girman muni a kan aikata laifi a wani bangare na daban na duniya.” Kuma ya ce, a cikin littafin Madalibu Ulin Nuha: “Kuma ana ninka […]

Wajibcin girmama Makka da Madina ga mahajjata (2)

Masallacin Annabi (SAW) da ke Madina

Fassara Abubakar Hamza

Ibn Kayyim (Allah Ya yi masa rahama), ya ce: “Yin mummunan laifi a Harami da kasar Harami (Makka) da kuma a kan shimfidar Allah (Masallaci) ya fi girman muni a kan aikata laifi a wani bangare na daban na duniya.”

Kuma ya ce, a cikin littafin Madalibu Ulin Nuha: “Kuma ana ninka kyawawan ayyuka da munana idan aka yi su a wuri mai daraja, kamar Makka da Madina da Baitul Makdis da kuma a cikin masallatai. Haka kuma idan aka yi su a wani zamani mai falala, kamar ranar Juma’a da watanni hudu masu alfarma da kuma a kwanakin watan azumi.”

Shehun Malami Mar’iy bn Yusuf Alkarmiy ya ce: “Lallai an sani daga shari’a mai haske da addini mikakke, cewa zunubi yana ninkuwa a wurare masu daraja da halaye madaukaka, to haka lamarin yake a wurare masu daraja.” Sa’annan ya ce: “Kowane wuri, ko zamani wanda ya fi daraja, to sabon Allah a cikinsa ya fi muni, domin bakar tawada ta fi bayyana ga farin abu.”

Imam Annawawi (Allah Ya yi masa rahama), ya ce: “Zababbiyar magana ita ce, lallai yin makwabtaka da Dakin Allah da kuma Masallacin Manzon Allah (SAW) a Makkah da Madina mustahabbi ne, sai ga wanda zato ya rinjaya masa cewa, zai auka cikin lamura ababen zargi, ko sashensu. Kuma hakika halittun da ba za a kididdige su ba, daga magabatan al’umma da wadanda suke a bayansu, daga cikin wadanda ake koyi da su, sun aikata mujawara  (makwabtaka a Makka da Madina).”

Imam Kurdabi (Allah Ya yi masa rahama), ya ce: “Haka kuma, shari’a a wurare da yawa ta bayyana cewa, lallai duk lokacin da alfarma ta ninka, sai aka keta ta, to ukubar ita ma sai ta ninka.”

Shaihul Islam Ibn Taimiyya (Allah Ya yi masa rahama), ya ce: “Yin sabo a kwanakin da ake girmamawa da wuraren da ake girmamawa, zunubinsu da ukubarsu yana yin kauri, gwargwadon falalar zamanin da wurin.”

Sannan Imam Kurdabi (Allah Ta’ala Ya yi masa rahama), ya ce: “Kuma idan Allah Madaukaki Ya girmama abu ta bangare guda, to sai ya zama yana da alfarma guda daya, idan kuma ya girmama shi ta bangarori biyu, ko bangarori da yawa, sai alfarmarsa ta kasance mai yawa, to sai a ninninka ukuba a kansa idan aka yi mummunan aiki, kamar yadda ake ninka lada idan aka yi aiki kyakkyawa; domin wanda ya yi biyayya ga Allah a cikin wata Mai alfarma a kuma gari Mai alfarma, to, ladansa ba kamar na mutumin da ya yi masa biyayya a watannin da ba su da alfarma, ko a garin da ba Harami ba ne. Haka wanda ya yi maSa biyayya a watan da ba ya da alfarma, amma a gari Mai alfarma, ba ya zama daidai da wanda ya yi maSa biyayya a watan da ba ya da alfarma, a kuma garin da ba ya da alfarma.”

Ya ku  Musulmi! Ku girmama ababen da Allah Ya ba su alfarma a cikin halin haraminku da wajensa, kada kuma ku ketare iyakokinSa, kada ku halatta wurare masu alfarma, Allah Ta’ala Ya ce: “Wannan kuma, saboda wanda ya girmama hukunce-hukuncen Allah , to shi ne mafifici a gare shi a wurin UbangijinSa.” (Hajji:30).

Alfarmomin kuma su ne: Girmama Mash’arul Haram (wuraren Hajji) da Daki Mai alfarma da Masallaci Mai alfarma da Gari Mai alfarma, wadannan su ne alfarmomin.

Kuma ku girmama abin da Allah Ya umarce ku da girmama shi, kuma ku gabatar da abin da Allah Ya umarci ku gabatar, kuma ku nisanci abin da Allah Ya hukunta haramcinsa, don ku samu falalarSa da ladarSa da ni’imarSa.

Ina fadan abin da kuke ji, ina neman gafarar Allah gare ni da ku, sai ku nemi gafararSa, lallai Shi Ya kasance ga masu mayar da lamuransu gare Shi Mai yawan gafara ne.

Huduba ta Biyu

Ya ku Musulmi! Sunnah ta tabbata kan ninka ladar Sallah a Masallaci Mai alfarma da Masallacin Annabi (SAW), wato ninkawa ta fuskar adadi ga farilla da nafila bisa maganar da ta fi inganci daga cikin maganganun malamai biyu.

An ruwaito daga Jabir  (Allah Ya kara yarda a gare shi) ya ce: “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Yin Sallah a Masallacina wannan, ya fi salloli dubu a waninsa falala; in ban da Masallaci Mai alfarma (Ka’aba). Sallah kuma a Masallaci Mai alfarma ta fi salloli dubu dari, a masallacin da ba shi ba.” Ahmad ya ruwaito shi, (14694 da 15271) da Ibn Majah.

Sai dai babu wani dalili ingantacce da ya nuna cewa, kyakkyawan aikin da aka aiwatar a garin Makka ana ninka ladarsa zuwa lada dubu dari. Ko yake cewa ana ninka ladar azumin Ramadan idan aka yi shi a garin Makka ko a Madina zuwa ladar azumin wata dubu dari, ko a ba da ladar Ramadan guda saba’in. Dukkan wadannan babu Sunnar da ta tabbatar da su, kuma babu wani dalili a kan haka. Kuma hadisan da suke dauke da wannan ma’anar ko dai da’ifai ne, ko yasassun hadisai na karya. Magana ingantacciya ita ce, lallai kyawawan ayyukan da aka yi a lokaci mai daraja da wuri mai daraja ana ninka ladarsu, ninkawa ta fuskar girma, ba ta fuskar adadi ba, sai abin da dalili (ingantacce) ya yi nuni a kansa. Kuma su ma munanan ayyukan da aka zartar da su a wurare ko lokuta masu daraja zunubinsu yana bunkasa ta fuskar girma, ba ninkuwa ta fuskar adadi ba.

Ya ku mahajjata da masu Umara da ziyara! Ku ribaci lokacin zamanku a garin Makka da Madina, ta hanyar yin kwazo ga aikata kyawawan ayyuka da yawaita aikata su, kuma ku yawaita tuba da neman gafara, kuma ku bayyanar da rusunawarku da kankan-da-kai da nadama da nuna bukatuwarku ga Ubangijnku da bayyanar da lalura; domin kuna wurin saukowar rahama, kuma wuraren karbar ayyuka da fagagen da ake zaton amsa addu’o’i da gafara da ’yanta bayi daga fadawa cikin wuta. Ku rika tuna girman wuraren da falalar lokutan.

Allah Ya hada addu’o’inku da amsawa, neman gafararku kuma da yarda, ayyukan da kuke yi kuma Ya karba.

Sheikh Salah Albudair ya gabatar da wannan Huduba ce a ranar Juma’ar da ta gabata (16 ga Zul-Kida, 1440 BH, 19 ga Yuli, 2019 Mildaiyya. Kuma mun samo ta ce daga shafin fecbook na Ustaz Aliyu Sa’id Gamawa

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos