Wajibi ne a hukunta sojojin da suka yi kisan gilla a Borno da Yobe – Ustaz dandada

Ustaz Abubakar dandada shi ne Shugaban Jam’iyyar NDP a Jihar Bauchi wanda rahoton da kungiyar Amnesty International ta fitar kan kashe kusan mutum dubu a jihohin Borno da Yobe a cikin wata shida, ya daga wa hankali, a tattaunawarsa da Aminiya ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta kama sojojin da suka yi wannan danyen aiki ta […]

Wajibi ne a hukunta sojojin da suka yi kisan gilla a Borno da Yobe – Ustaz dandada

Ustaz Abubakar DandadaUstaz Abubakar dandada shi ne Shugaban Jam’iyyar NDP a Jihar Bauchi wanda rahoton da kungiyar Amnesty International ta fitar kan kashe kusan mutum dubu a jihohin Borno da Yobe a cikin wata shida, ya daga wa hankali, a tattaunawarsa da Aminiya ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta kama sojojin da suka yi wannan danyen aiki ta kai su kotu don su fuskanci hukunci:

Aminiya: Me za ka ce kan rahoton kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Duniya (Amnesty International) kan kisan gilla da sojoji suka yi ga mutanen da suke tsare da su a Maiduguri da Yobe?
Ustaz dandada: Wannan kisan gilla abin kunya ce ga gwamnati da duk masu rike da mukamai, a ce irin wannan abu ya faru amma sai wani da ke nesa ne zai fito fili ya nuna kishi da tausayi tare da bukatar a bincika don hukunta wadanda suka aikata laifin domin a kiyaye gaba.  Shugabanni suna nuna halin ko oho da rayuwar mutanensu a kasar nan, saboda yadda suke barin na kasa da su suna yin abin da ransu yake so wajen cin zarafin al’umma, lamarin da idan aka ci gaba da haka za a iya haifar da rashin zaman lafiya saboda wata kabilar za ta ga kamar an turo sojojin ne don su rika yi mata kisan gilla da gangan, kamar yadda ya faru a kasashe irin su Rwanda da Burundi da Bosniya.
Aminiya: Yaya kake kallon lamarin ta gefen addini da siyasa?
Ustaz dandada:  Babu wani addini Musulunci ko Kiristanci ko wata dokar kasa ko ta duniya da ta yarda da zalunci. An yarda duk wanda ya aikata laifi a yi bincike a yi masa hukunci, amma ba a kama mutane a tsare su ba ci ba sha ba. Zalunci a wurin tsare mutane na soja abu ne mummuna a al’adance ko a addinance, don haka ya zamo wajibi gwamnati ta tabbatar an diddigin rahoton kungiyar Amnesty. Kuma a zauna tare wajen ganin an hukunta duk masu hannu cikin lamarin. Haka a bincika dukkan gidajen yari da wuraren tsare mutane na soja da ’yan sanda duk wanda aka kama ba tare da laifi ba, a sake shi a ba shi hakuri, idan ta kama na biyan diyya a biya shi, wadanda suka tsare shi kuma a hukumta su, tunda akwai takardar da ake rubuta sunayen wadanda aka kama da wadanda suka kamo su da rana da kuma lokacin da aka sake su ko aka kashe su duk a bi daftarin bayanan don a tabbatar da adalci. Ina son mahukunta kowa ya san irin hakkin da ya rataya a wuyansa, musamman wannan abu da ke faruwa, rashin imani ne da rashin tunani ga kowane mabiyin addini, ya ga ana kashe mutane ana kaiwa a watsar ko ana fita da mutane ana harbewa amma ya ki nuna damuwa, ko domin kada fushin Allah ya rutsa da dukkansu a dauki mataki. Kuma Musulunci ya koyar da idan ka ga ana aikata laifi ka yi hani da karfinka ko da bakinka amma Musulmin da suke aiki a irin wadannan wurare sun yi shiru sai Bature ne zai zo ya nuna ana cutar da mutanensu, wannan abin takaici ne.
Aminiya: A ganinka me ke jawo irin wannan matsalar ta rashin martaban ran dan Najeriya?
Ustaz dandada: Ba komai ke jawo haka ba sai rashin tsoron Allah da tawakkali, saboda kullum suna ganin idan ba su tare da wannan kaki na soja ko dan sanda kamar ba za su rayu ba ne. Don haka ya kamata kowa ya fito idan ya ga kuskure ya bayyana don a gan shi da mutunci, idan ba haka ba mutane suna nan suna addu’a wacce ba makawa da sannu za ta kama duk wanda ya aikata kisan gilla ga Musulmi ko ba Musulmi ba. Kuma hakan ke sa mutum ya gama aiki ya yi ritaya ya lalace, ko yana cikin aikin ya yi mutuwar wulakanci, haka ya faru ya fi a kirga. Don haka ya kamata mutane su rika daukar darasi su daina ganin idan sun shiga aikin soja ko dan sanda ko wani aiki na doka kamar an yafe su ne, tun daga duniya Allah ke hukunci ga azzalumai kafin su je Lahira su shiga mummunar makoma.
Abin da muke dauka ana wannan kashe-kashe ne don a rage yawan mutanen Arewa da nakasa walwala da dukiyar mutanen Arewa da gangan ba don rashin sani ba. Saboda Gwamnatin Tarayya ta san duk wani cin zarafi da ake yi ga mutumin Arewa ta hanyar canje-canjen wuraren aiki da wulakanci da ake yi. Don haka ’yan Arewa kowa ya fito idan an cuce shi ya yi magana, kuma ya yi aiki da karfinsa da dukiyarsa da matsayinsa don kare yankinsa da kasar nan da mutanen cikinta. Musulmi da wadanda ba Musulmi ba su sani cewa; dukkan abin da ake yi ga Arewa mutum ko a ina yake a Najeriya yana shafarsa, musamman ganin duk abin da ke faruwa a jihohin Arewa ba wanda yake zaune lafiya idan fitina ta tashi a inda yake. Kuma kowane dan Arewa na da bukata a Kudu haka kowane dan Kudu yana da bukata a Arewa kowa ya san haka. Don haka Najeriya wurin zaman kowa ne haka kuma mutum bai isa ya hana wani zama a doron kasa ba, ko ya hana mai shiga wuta zuwa wuta ko ya hana mai zuwa Aljanna zuwa Aljannar ba, sai idan mutum ya dauki cewa zai iya rigima da Ubangijinsa ne kurum.
Don haka nasihata ga ’yan Arewa wadanda ba Musulmi ba, su sani ba su da inda ya wuce Arewa, kuma ko raba kasar aka yi suna nan zaune da abokan zamansu Musulmin Arewa, haka su ma Musulmin ba wanda ya isa hana wani wanda ba Musulmi ba zama a Arewa duk irin halin da aka shiga. Domin haka dukkanmu gatar juna ne ya kamata kowa ya gyara tunaninsa ya nemi zaman lafiya, ya tashi ya nemi abin da zai lura da kansa da iyalansa cikin salama.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50