‘Wajibi ne a kare asibitoci a inda ake yaki’
Kwamitin Tsaro na Majalisar dinkin Duniya ya gabatar da wani kuduri da ke neman a bai wa manya da kananan asibitoci da kuma ma’aikatan lafiya kariya a yankunan da ake fama da yaki.Wannan kuduri na zuwa ne kasa da mako guda da kai wasu hare-haren sama kan wani asibiti a Siriya wanda ya yi sanadiyyar […]
Kwamitin Tsaro na Majalisar dinkin Duniya ya gabatar da wani kuduri da ke neman a bai wa manya da kananan asibitoci da kuma ma’aikatan lafiya kariya a yankunan da ake fama da yaki.
Wannan kuduri na zuwa ne kasa da mako guda da kai wasu hare-haren sama kan wani asibiti a Siriya wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 30.
Shugaban Majalisar dinkin Duniya, Ban Ki-moon, ya bukaci kowacce kasa da ta kara kaimi wajen ganin an dakile kai irin wadannan hare-hare, ba wai yin Allah-wadai da shi kawai ba.
Ya kara da cewa, yakamata a yi wa duk wanda aka kama da hannu a irin wannan aika-aika hukunci.
Kwanakin baya ne, kungiyar likitoci ta Medecins Sans Frontieres, ta nuna rashin jin dadinta kan matakin da rundunar sojin Amurka ta dauka cewa ba za a kaddamar da tuhumar aikata mugun laifi kan wani mummunan harin sama da aka kai wani asibiti a Afghanistan ba a bara.