Wajibi ne kowa ya ba da gudunmawa ga gyara matsalolin tsaro

Masallacin Halliru Abdu, Birnin Kebbi Hudubu ta Farko Dukan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai mulki, Mai tsarki, Aminci, Mai amintarwa, Mai tsarewa, Mabuwayi, Mai gafara. Ya Allah! Kai ne Aminci kuma aminci daga gare Ka yake zuwa; Ka raya mu a cikin aminci. Ka tsarkaka ya Ma’abucin daukaka da buwaya! Ya Allah! […]

Wajibi ne kowa ya ba da gudunmawa ga gyara matsalolin tsaro

Masallacin Great Mosque na Dining China

Masallacin Halliru Abdu, Birnin Kebbi

Hudubu ta Farko

Dukan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Mai mulki, Mai tsarki, Aminci, Mai amintarwa, Mai tsarewa, Mabuwayi, Mai gafara. Ya Allah! Kai ne Aminci kuma aminci daga gare Ka yake zuwa; Ka raya mu a cikin aminci. Ka tsarkaka ya Ma’abucin daukaka da buwaya! Ya Allah! Ka yi salati ga Shugabanmu Annabi Muhammadu, BawanKa, AnnabinKa kuma ManzonKa. Annabin da bai koyi karatu ko rubutu daga wani mutum ba; da jama’ar gidansa da sahabbansa baki daya.

Bayan haka, ya ’yan uwa na imani! Ba boye yake ba a gare ku cewa wannan kasa tamu an sake jarraba ta da wasu masifun da muke neman agajin Allah, muke labewa zuwa gare Shi, muna masu kankan da kanmu gare Shi, muna rokonSa Ya dauke mana su domin rahamarSa.

Daga cikin mafi bayyanar wadannan masifun, kamar yadda amintattun labarai da ganau suka fada, akwai kashe-kashen ta’addanci da cin zarafin mata da hallaka amfanin gona da kame mutane a nemi kudin fansa da sauransu, musamman a Jihar Zamfara da wasu jihohi a Arewacin kasar nan! Sai mu ce “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!” Ya Allah, Ka kubutar da wannan al’umma daga wadannan masifu, kuma Ka maye mata da abin da ya fi su zama alheri, domin rahamarKa, ya Mafi jinkan masu jinkai!

Ya ku ’yan uwa! Wajibi ne mu jaddada imaninmu da Allah, mu sakankance (mu hakikance) cewa fa komai yana HannunSa ne, kuma Shi ne Mai rahama Mai jinkai, Mai tausayin bayinSa, Mai tausasa musu. Don haka, mu koma maSa, mu tuba zuwa gare Shi, mu nemi tunkudewar masifa daga gare Shi. Mu yi kankan da kai zuwa gare Shi, mu roke Shi! Ya fadi a cikin Alkur’aninSa Mai girma cewa: “To don me a lokacin da tsananinMu ya je musu ba su yi tawali’u ba? …(An’am: 43). Kun ga an zargi wadancan mutanen da rashin tawali’u ga Allah da rashin addu’a alhali suna cikin wani yanayi. Da wannan za mu fahimci cewa ashe idan aka yi kankan da kai ga Allah aka roke Shi, ana fatar yayewar kowane tsanani. Ya Allah ga mu muna kankan da kai gare Ka, muna rokonKa, Ka dauke mana wadannan bala’o’i, kuma Ka musanya mana su da aminci da kwanciyar hankali da zama lafiya domin rahamarKa!

Bayan haka, ya ku ’yan uwa! Mu fa fahimci cewa kokarin warware wadannan matsaloli ba a kan shugabanni kawai yake ba. A’a, dole ne kowanenmu ya yi aikin da ya wajaba a kansa domin abubuwa su gyaru. Manzon Allah (Mai tsira da Amincin Allah ya ce:

“Kowannenku makiyayi ne, kuma kowanenku abin tambaya ne a kan abin da aka ba shi kiwo” (Bukhari da Muslim suka ruwaito).

A kan haka, kowanenmu sai ya fara da kansa. Hanyar gyaran kai kuwa (kamar yadda wadansu malamai suka yi bincike suka tsara), ita ce ka zama:

Mai lafiyayyar akidar Musulunci

Mai kiyaye ibada ingantacciya

Mai wayayyen tunani (ya san addinisa, ya san zamaninsa)

Mai kyawawan dabi’u

Mai kakkarfan jiki (wato zama jarumi, ba rago ba)

Mai iya neman na kansa (ba cima-zaune ba)

Ba mai bata lokacinsa ba (ga abin da ba zai amfane shi duniya ko Lahira ba)

Mai tsari ga al’amuransa

Mai yakar rayuwarsa a kan ta tsayu a kan hanyar Allah, kuma

Mai amfanar da waninsa.

Na yi imani cewa idan kowanenmu ya tsare wadannan ka’i’doji, za mu zama mutanen kirki, kuma za mu zama abin koyi ga wadansu insha Allah.

Ya Allah! Ka taimake mu mu kiyaye wadannan ka’i’doji, Ka kama mana ambatonKa da gode maKa da kuma kyautata ibadarKa, ya Mafi jinkan masu jinkai! Tsira da Amincin Allah su tabbata ga Shugabanmu, Annabi Muhammad (SAW) da jama’ar gidansa da sahabbansa baki daya.

Huduba ta Biyu

Dukan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin talikai. Tsira da Amincin Allah su tabbata ga Annabinmu Muhammad (SAW) mai halin girma.

Bayan haka, ya ku bayin Allah! Daga cikin matakan warware wadannan matsaloli (na lalecewar tsaro) a kasar nan akwai:

Dole ne IYAYE su tsayu ga tarbiyyar ’ya’yansu (wato su kula da ita kamar yadda Allah Ya aza musu). Ku tuna fa ya ku iyaye! Cewa a shari’ar Musulunci (ga abin da muka sani), haihuwar ’ya’yan ba tilas ba ne, amma tarbiyyantar da su dole ne (farlu ainin), wanda idan ba ka yi ba, ka yi laifi.

Su kuma MALAMAI, lallai ne su zama abin koyi a wajen tsoron Allah da kaffa-kaffa da duniya. Manzon Allah (SAW) ya ce: “Babu wasu kyarkeci guda biyu mayunwata da aka sake su a cikin tumaki da za su iya yin barna a cikinsu fiye da barna da kwadayin mutum a kan dukiya da mulki (ko suna ko daukaka…) za su yi masa ga addininsa” (Imam Tirmizi ne da sauransu suka ruwaito, kuma ya ce Hadisi ne mai kyau, ingantattace).

Su kuma MAWADATA kada su zama marowata (su rika fitar da zakkar dukiyarsu kamar yadda Allah Ya ce. Kuma su buda hanyoyin samar da ayukkan yi ga marasa shi da kuma samari). Allah ba Ya son dukiya ta zama tana yawo a tsakanin mawadata kawai.

Su kuma SAMARI su daure, su himmatu wajen neman ilimi mai amfani da kuma sana’o’i. Su sani cewa zaman mutum mai bayarwa shi ne daukaka, ba zama mai karba daga wani ba.

Su kuma SHUGABANNI, wajibi ne su ji tsoron Allah game da talakawansu. Daga cikin aikin da Allah Ya dora musu akwai toshe duk wata hanyar da makiya al’ummarsu za su iya kai musu hari ko su yi musu ta’addanci.

A cikin littafin “Diya’ul-Hukkam” na Sheikh Abdullahi dan Fodiyo, game da abin da ya wajaba a kan shugaba, ya ce: “Lallai ne shugaba ya san halaye da yanayin makiya ta hanyar amfani da masu leken asiri amintattu a kowane lokaci – ko a yanayin hargitsi, ko a yanayin kwanciyar hankali, ta yadda ba abin da zai boyu gare shi na kai-komonsu a kowane lokaci. Domin duk abin da ka jahilta, to, ka zama makahonsa, alhali mai gani daya yana iya rinjayar makafi dubu!” A nan, dole ne a yaba wa duk Gwamnan da ya tsayu bil-hakki, ya nuna kulawa ga jama’arsa a lokutan damuwa (irin yadda muka sani Gwamna Kashim Shattima na Borno da Gwamna Nasir El-Rufa’i na Kaduna suka yi. Allah Ya saka musu da alheri; sabanin Gwamnan da rahotanni suka ce ana ta kashe jama’arsa, shi kuma ya tafi wani wuri abinsa, ya yi zamansa). Ya Allah Ka ba mu lafiya da zama lafiya.

GABA DAYA dai, dole ne mu damu da halin da ’yan uwanmu na Jihar Zamfara da ire-irenta suke ciki. Mu yi duk kokarin da muke iyawa wajen yaye bakin cikinsu. Mu yi musu addu’o’i da Kunuti a salloli. Mu tuna Hadisi ko hadisan Annabi (SAW) da ya kwatanta soyayya da tausayawar mumminai ga junansu cewa kamar gangar jiki daya ne; duk abin da ya samu wata gaba, to sauran gabobi za su karba da rashin barci da zazzabi.

Ku tuna ya ’yan uwa! Cewa fa muna da makiya ga addininmu da kasarmu. Kuma (su makiyan namu) ba su takaitawa wajen yi mana barna, kuma abin da duk zai wahalar da mu shi suke buri (suke so). (Dubi Surar Ali-Imran, Aya ta 118). Makiyanmu a yau suna iya tayar da ’yan ta’adda ko ’yan tawaye a cikinmu, ko su karfafa su, su yi ta yi mkna barnar da su makiyan namu ba sai sun zo da kansu sun yi mana ba! Fatar wadansu makiyanmu fa ita ce wargajewar kasar nan kamar yadda wasu kasashe suka wargaje. Kada Allah Ya sa!

Lallai ne mu farka; mu kare addininmu da kasarmu, domin shi ma jihadi ne. (Dubi Fikhus Sunna mujalladi na 3, Babin Jihadi). Mu yawaita addu’a ga kawunanmu da ’yan uwanmu da ke cikin matsaloli (a ko’ina suke) da Shugaban Kasarmu  Muhammad Buhari, wanda aka shaidi gaskiyarsa da hakurinsa da rikon amanarsa; da sauran jagororinmu da jami’an tsaronmu – wadanda muke barci, su kuma idanunsu suna bude saboda mu; mu kwana a gidajenmu, su kuma su kwana a daji saboda mu! Mu kuma ci gaba da addu’a ga kasarmu da dukan kasashen Musulmi.

Ya Allah! Ka ba mu abu mai kyau a duniya, kuma Ka ba mu mai kyau a Lahira, kuma Ka kare mu daga azabar Wuta. Ya Allah! Ka yi salati da sallama ga Shugabanmu, Annabinmu Muhammad (SAW) da jama’ar gidansa da sahabbansa baki daya.

Wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Za a iya samun Imam Injiniya Isma’il M. Cindo Gotomo (MNSE, MNIAE)  ta +2348036049452 da ismailgotomo@yahoo.com.