Wajibi ne mu hadu don ceto Najeriya
A shekarar 2007 mun yi babban taron Jam’iyyar AD a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano a ranar 10/02/2007 a matsayina na Shugaban Jam’iyyar AD na kasa, inda muka yi kira ga ’yan takara uku: Janar Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar da Attahiru dalhatu Bafarawa a kan su hada kai su bar wa […]
A shekarar 2007 mun yi babban taron Jam’iyyar AD a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano a ranar 10/02/2007 a matsayina na Shugaban Jam’iyyar AD na kasa, inda muka yi kira ga ’yan takara uku: Janar Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar da Attahiru dalhatu Bafarawa a kan su hada kai su bar wa daya daga cikinsu, duk wanda suka bar wa shi ne dan takararmu (AD), shi za mu yi wa yakin neman zabe, sai inda karfinmu ya kare. Duk su ukun na je na samu kowannensu daya bayan daya, na fara da Attahiru Bafarawa a Abuja (Sokoto State House) da magariba har 11:00 na dare muna tare, na ba shi takardar da muka tsara da su Malam Muhammadu Inuwa Dutse da sauran jiga-jigan Jam’iyyar AD na kowane bangare da suka halarci babban taron, na yi masa cikakken bayani. Daga nan na je na samu Janar Muhammadu Buhari a Hilton Hotel na ba shi tasa takardar na yi masa cikakken bayani. Zan iya tunawa muna ganawa da shi ne Hajiya Naja’atu ta leko, Janar Buhari ya ce ta yi hakuri. Haka Alhaji Sule Yahaya Hamma shi ma Buhari ya ce da shi ya yi hakuri. Sai da muka kai kusan karfe 2:00 na dare tare. Muna cin abinci da shi Janar din sai ga Alhaji Sule Yahaya Hamma ya dawo tare da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Sani Yariman Bakura bayan mun gaisa da su, na yi sallama da su na tafi. Washegari da karfe 7:00 na safe awa biyar tsakani na je Fadar Shugaban kasa gidan Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar yana fitowa muka shiga wurin karya kumallo, ni da shi da wasu abokansa, muna gamawa ya ba abokansa hakuri cewa ni kadai zai iya gani, saboda jirgi yana jiransa zai yi tafiya. Muka shiga wani karamin ofis a gidansa, na ba shi tasa takardar, na yi masa bayani a kan hadarin rarrabuwar kansu, bayan dukkansu suna yakar Jam’iyyar PDP ne. Ni kadai na san lafazin da kowannensu ya yi min.
To alhamdulillahi yanzu an samu irin wannan dama ta hada kan ’yan adawa domin kawo gyarar da ake bukata. Sai dai abin takaici wasu saboda dalilai na kashin kai ko dai saboda sun fadi a zaben fidda-gwani ko abin da suke gani an yi musu magudi ko an kada yaransu ko an yi wa yaransu magudi, sun fara cewa sama APC kasa wat jam’iyyar.
A fahimtata, wannan gagarumin aiki na kawar da mugun mulki na PDP da ya gaza yin amfani da dama da dukiyar da Allah Ya ba kasar nan, wajen bunkasa kasar da ci gaban rayuwar jama’a ta yadda hatta wutar lantarki ta ka sa inganta, bai kamata mu lura da bukatun kanmu ba. Tilas a siyasa a bata wa wani a kuma kyautata wa wani, bai kamata wanda aka bata masa yau ya fusata ya yanke irin wannan danyen hukunci na ungulu da kan zabo ba.
Wannan ce dama ta karshe da insha Allah za mu kawo wannan sauyi ta wajen zaben Janar Muhammadu Buhari, kuma Buhari yana bukatar mataimaka wadanda wajibi ne su fito daga jam’iyyarsa idan har ana bukatar ya samu nasarar kawo gyaran da ake bukata. Idan wani ya ce, a zabi APC a sama, a zabi PDP ko APGA ko PDM a kasa, to ba masoyin Buhari ba ne, ba masoyin kawo gyara ba ne, masoyin kansa ne kawai.
Don haka ina kiran dukkan wadanda suke jin an saba ko an bata musu su fahimci cewa ba batu ne na daidaikunmu ba, batu ne na ceto kasa daga mugun mulkin da muke fama da shi, mulkin da ya gaza kare rayuka da dukiyoyinmu, mulkin da satar dukiyar gwamnati ba laifi ba ne! Na yi imani kusan kowa a Najeriya yana tafiya a kan titi ne ba tare da tabbacin zai iya komawa gida ba, yana fitowa ne daga gidansa yana tunanin ko zai koma ko ba zai koma ba, saboda gwamnati ta gaza kare rayuwarsa. Mutane da dama a yanzu abin da suke so a samu zaman lafiya, wanda wannan gwamnati ta nuna ba za ta samar da shi ba. Ta nuna wa duniya matsalar tsaro ta fi karfinta.
Wata sabuwa, a yayin da muka hango hasken cewa canjin da muke nema yana dab da samuwa, sai kuma alamu na nuna cewa ana yunkurin dakile gudanar da zaben na bana. Akwai bayanan da ke cewa gwamnati ba ta ba hukumar zabe (INEC) isassun kudi don gudanar da zaben mai zuwa ba. Sannan a gefe akwai wadanda suka fara kiraye-kirayen a kafa gwamnatin rikon kwarya, kuma wani abu takaici shi ne suna son wai a kafa wannan gwamnati a karkashin Shugaba Jonathan sannnan wai shugabancin ya rika zagayawa har na tsawon wasu shekaru.
A gaskiya ba za mu amince da wannan gurguwar shawara ba, ko da wannan gwamnati za ta gaza gudanar da zaben na bana, hakika ba za mu yarda a kara mata ko da kwana daya ba. Kuma ina kira ga ’yan Majalisar Tarayya su hanzarta gyara kundin tsarin mulki yadda zai bayar da damar kafa gwamnatin rikon kwarya a karkashin Babban Jojin Najeriya, kuma gwamnatin ta kunshi mutane masu mutunci da ba su da sha’awa ta tsayawa takarar siyasa daga kowane bangare, sannan su dauki akalla shekara biyu ta yadda za su samu damar tsarkake duk kazantar da Najeriya take ciki a halin yanzu.
Bayan haka sai a aiwatar da wadannan abubuwan kamar haka:
1) A kwato dukkan kudi da kadarori da rijiyoyin mai da azzaluman shugabanni suka wawashe suka rabe a tsakaninsu.
2) A kafa hukuma ta musamman da za ta kula da dukkan ’yan Najeriya marasa aiki ko sana’a, ta rika ba su abin da suke bukata na rayuwa har sai lokacin da gwamnati ta samar da ayyukan yi da sana’o’i a wadace yadda kowa zai samu abin da zai yi, ya dogara da kansa.
3) A inganta wutar lantarki da ruwan famfo da jiragen sama da na kasa da na ruwa da na karkashin kasa, mallakar gwamnatin Najeriya.
4) Ilimi da kiwon lafiya a bayar da su kyauta.
5) A rika biyan diyyar rayuka da na dukiya a duk yayin da suka salwanta saboda sakacin gwamnati. Wato dai a inganta sha’anin tsaro.
6) A janye kariyar da ake ba masu mulki (immunity) wadda take ba su dama su rika yin duk barnar da suka ga dama ba a hukunta su.
7) Sannan a bude sabon babi na kafa sababbin jam’iyyu da sabuwar hukumar zabe, har ila yau kuma a hukunta dun wadanda suka taba yin kowane irin laifi a baya, kowa ya gani. A kashe na kashewa, a daure na daurewa, sannan a kwato duk abin da suka mallaka ba bisa ka’ida ba a mayar asusun gwamnati don yi wa jama’a aiki.
Abdulkarim dayyabu
Shugaban Rundunar Adalci ta Najeriya,
Kano.
08023106666, 08060116666,
Imel:[email protected]