Wajibi ne mu yi hakurin zama da juna lafiya – Sheikh karibullah
Shugaban darikar kadiriyya ta Afirka Sheikh karibullah Nasiru Kabara ya nemi al’ummar kasar nan su yi hakuri da juna sa zauna lafiya, musamman a wannan lokaci da kasar ta shiga halin ni’ya-su.Sheikh karibullah ya bayyana haka ne lokacin da yake aza harsashin ginin makarantar Islamiyya ta tunawa da marigayi Sheikh Mu’azu Umar a Sabon Garin […]

Shugaban darikar kadiriyya ta Afirka Sheikh karibullah Nasiru Kabara ya nemi al’ummar kasar nan su yi hakuri da juna sa zauna lafiya, musamman a wannan lokaci da kasar ta shiga halin ni’ya-su.
Sheikh karibullah ya bayyana haka ne lokacin da yake aza harsashin ginin makarantar Islamiyya ta tunawa da marigayi Sheikh Mu’azu Umar a Sabon Garin Narabi da ke karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi a ranar Asabar din da ta gabata. Makarantar dai fitaccen malamin addinin Musuluncin nan makaho da ke Jos, Sheikh Abdulkadir Mu’azu Umar ne ya kudiri aniyar ginawa.
Sheikh karibullah wanda Alhaji Rabi’u Akawu Namata ya wakilnta ya ce, “Dole ne mu yi hakuri da junanmu, mu zauna lafiya, ganin halin da kasar nan ta shiga, dole mu yi wa kanmu fada mu zauna lafiya.”
Daga nan sai ya ce babu abin da yake sama da ilimi a rayuwa. Domin idan da ilimi abubuwa da dama za su zo da sauki a fahimci mene ne rayuwa, a fahimci juna kuma a zauna lafiya.
Sheikh karibullah ya ce yunkurin da malamin ya yi don gina makarantar babban abin alheri ne, sai ya yi godiya gare shi da dukkan wadanda suka taimaka wajen ganin an fara ginini makarantar.
A jawabin Babban Limamin Jos, Sheikh Balarabe Dawud ya yaba wa malamin kan wannan kokari da ya yi. Ya ce malamin duk da cewa Allah Ya yi shi makaho amma Allah Ya ba shi ilimi da kishin ilimin, wajen yada shi zuwa ga al’umma ta hanyar wa’azin da yake gabatarwa. Ya ce ya rubuta littattafa da dama don ilimantar da al’umma, kuma ga shi zai gina makarantar Islamiyya da masallaci. “Wannan ya nuna cewa Allah Ya yi wa wannan bawan Allah babbar baiwa duk da cewa makaho ne,” inji shi.
A jawabin wani malami a Jami’ar Jos, Dokta Abdurrahaman Lawal ya ce addinin Musulunci, addini ne na ilimi da karatu. Ya ce malamai masu hikima suna cewa duk wani abu da aka ce karatu ne ginshikinsa to wannan abin zai kai ga nasara. Ya yi kira ga al’ummar garin su tashi tsaye wajen ganin aikin ya tabbata don sun amfana da shi.
Dokta Abdurrahaman Lawal wanda Alaramma danjuma Usman Gwani ya wakilta ya ce rashin irin wadannan makarantu ya sa aka tafi aka bar al’ummar Musulmi a baya.
Tun farko a jawabin Sheikh Abdulkadir Mu’azu Umar ya ce dalilin gina makarantar shi ne domin ya cika burin mahaifinsa na gina makaranta tun yana raye don inganta rayuwar al’umma. Ya ce akalla an kiyasta za a kashe Naira miliyan 10 wajen gina makarantar, kuma ya mata sunan mahaifinsu wato makarantar Sheikh Malam Mu’azu Umar.
Sheikh Abdulkadir ya ce makarantar za ta kunshi ajujuwa 10 da ofishi da dakin karatu da na na’urar kwanfuta da masallaci. Ya ce Alhaji Rabi’u Akawu Namata ya ba da gudunmawar buhun siminti 50 da bulo 1,000 da yashi tifa 13.