‘Wajibi ne Musulmi su hada kansu’

Shugaban kungiyar Fityanul Islam na kananan hukumomin yankin Kudancin Kaduna Malam Aminu kasim ne ya bukaci al’ummar Musulmi su manta da sabanin da ke tsakaninsu na kungiya ko mazhaba, su hada kai su kasance tsintsiya madaurinki daya, domin yi wa addinin Allah hidima da kuma samun karfintunkarar kalubale da Musulunci da Musulmi ke fuskanta a […]

‘Wajibi ne Musulmi su hada kansu’
‘Wajibi ne Musulmi su hada kansu’

Shugaban kungiyar Fityanul Islam na kananan hukumomin yankin Kudancin Kaduna Malam Aminu kasim ne ya bukaci al’ummar Musulmi su manta da sabanin da ke tsakaninsu na kungiya ko mazhaba, su hada kai su kasance tsintsiya madaurinki daya, domin yi wa addinin Allah hidima da kuma samun karfin
tunkarar kalubale da Musulunci da Musulmi ke fuskanta a duniya.
Malam Aminu kassim, ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyin wakilin Aminiya a ofishinsa da ke makarantar Markaz Abul kasim Al-Islamiy a garin Kafanchan. “Babu abin da zai taimaki al’umma ta karshe face abin da ya taimaki ta farko har suka cimma nasarar kai addinin Musulunci inda ya kai, wato hadin kai da kaunar juna,” inji Malamin.
Sai ya shawarci malamai cewa bai kamata don wani malami ya ji wata magana da a ganinsa ba daidai ba ne daga bakin wani malami ko wanda suke da sabanin fahimta da shi, ya je wurin almajiransa ya kafa musu wa’azi yana sukarsa. Ya ce hakan ke raunana ’yan uwantakar addini da haifar da hassada a tsakanin malamai, ta yadda kowa ke son girma, har a wayigari ba mai fadi a ji kamarsa alhali dukkansu manufarsu guda ce, ita ce ci gaban addini.
Da ya juya kan matasa wadanda ya ce su ne kashin bayan al’umma, Malam Aminu kasim ya hore su da neman ilimin addini da na zamani tare da lissafa lokacinsu suna amfani da shi, domin a cewarsa, lokaci kamar kibiya ne in ya fita, ya fita ya wuce ke nan ba zai maimaita kansa ba, “Don haka lokaci na da matukar muhimmanci musamman ga matasa domin su ne kashin bayan al’umma. Bai kamata su tozarta lokacinsu da damarsu da rayuwarsu gaba daya wajen shaye-shayen kayan maye ba, ta yadda mutum zai kasa tsinana wa kansa komai ballantana al’ummarsa ko addininsa,” inji shi.

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe

Iran da Amurka sun daidaita tattaunawar sulhu a Switzerland