Wajibi ne ’yan Najeriya su fito su zabi shugabanni nagari – Sheikh Jingir
Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, ya bukaci al’ummar Najeriya su fito su zabi shugabanni nagari da za su ceto kasar nan daga mawuyacin halin da take ciki. Sheikh Sani Yahya Jingir ya yi wannan kira ne a wa’azin kasa da kungiyar ta […]
Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, ya bukaci al’ummar Najeriya su fito su zabi shugabanni nagari da za su ceto kasar nan daga mawuyacin halin da take ciki.
Sheikh Sani Yahya Jingir ya yi wannan kira ne a wa’azin kasa da kungiyar ta shirya a garin
Kebbe da ke Jihar Sakkwato a ranar Asabar da Lahadin nan.
Ya ce “Ya zama wajibi mu fito a lokacin zaben nan mai zuwa, domin mu zabi shugabanni nagari masu tsoron Allah wadanda za su ceto kasar nan daga mawuyacin halin da muke ciki. Mu guji kwadayi, mu lura da halayen mutum na kwarai a wajen wannan zabe da za a yi.”
Sheikh Jingir ya roki Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta yi gaskiya a lokacin zaben. Kuma ya yi kira ga jami’an tsaro su yi gaskiya, kada su bari a yi amfani da su, a yi magudi ko zaluntar wani.
Sheikh Jingir ya nuna takaici kan irin mawuyacin halin da al’ummar Musulmi suke ciki. Ya ce a gaskiya Musulmi suna jin jiki a Najeriya da duniya baki daya saboda hargitsewar al’amura. Ya yi kira ga Musulmin kan su koma ga Allah.