Waka fitila ce da ke haskaka rayuwar al’umma – Mawakiya Balhat

Wata matashiya mai rera wakokin Hausa a Jihar Legas mai suna Balhat Nuhu  ta ce waka fitila ce da ke haskaka rayuwar al’umma. Mawakiyar  ’yar shekara 20 a duniya ta kuma ce burinta ta rika kirkiro wakokin yabon Manzon Allah (SAW) a maimakon rera wakokin da wasu suka tsara.Ta ce:  ‘Gaskiya ba ni nake tsara […]

Waka fitila ce da ke haskaka rayuwar al’umma – Mawakiya Balhat

Wata matashiya mai rera wakokin Hausa a Jihar Legas mai suna Balhat Nuhu  ta ce waka fitila ce da ke haskaka rayuwar al’umma.
Mawakiyar  ’yar shekara 20 a duniya ta kuma ce burinta ta rika kirkiro wakokin yabon Manzon Allah (SAW) a maimakon rera wakokin da wasu suka tsara.
Ta ce:  ‘Gaskiya ba ni nake tsara wakokin ba sai dai wasu su tsara ni kuma na rera. Ban taba kirkiro waka ta kaina ba, amma ina da burin na rika yin wadanda za su samu karbuwa a wurin jama’a. Shi ya sa tun yanzu na fara yunkurin tsara wata waka ta yabon Manzon Allah (SAW) wacce nake burin za ta samu karbuwa a wurin jama’a’.
Ta kara cewa: “Waka wata fitila ce da ke haskaka rayuwar al’umma, hakan ne ya sanya tsara waka da kuma rerawa sai mai baiwa. Wani Allah Ya hada masa duka biyun wani kuma daya Ya ba shi,  amma ni Allah Ya hada mini duka biyun, shi ya sa nake yi masa godiya da baiwar da Ya yi mini.”
Balhat wacce ta shafe shekaru fiye da biyu tana rera waka, ta ce sha’awar waka ce ta sa ta tsunduma cikin harkar waka.
Ta bayyana cewa ta hadu da mutane iri-iri kuma ta karu da ilimomi daban-daban sakamakon rera wakokin da take yi.
“Gaskiya na karu da ilimi da yawa saboda rera wakokin jama’a da nake yi. Ni da ma tun ina karama nake sha’awar waka saboda haka ne ma na shiga rera wakoki tun ina karama a makarantar Islamiyya, inda malamaina suka zabe ni na zama tamkar zabiyar makarantarmu.” Inji ta.
 Tana karbar Naira dubu hudu a kowane amshin waka, idan kuwa za ta rera baitoci ne takan karbi fiye da haka.
Amma duk da haka Balhat ta bayyana cewa babbar matsalar da take ci mata tuwo a kwarya ita ce rera karin waka.
“Karin waka yana da wahala. Wani lokaci idan aka ba ka sabuwar waka aka ce ka rera a karon farko za ka rika gamuwa da kalubale, amma daga bisani idan ka maimaita sau da yawa sai ka ga ka iya.” Inji ta.
Ta ce wakar da ta rera mai suna ‘Salamun Alaika’ ita ce ta fi shiga ranta saboda yabo ce ga Manzon Allah (SAW).