Waka ta fi noma wahala- Mawakiya Ummi Nagarta
Ummi Muhammad wacce aka fi sani da Ummi Nagarta ta shafe shekaru a harkar waka, ta yi bayanin yadda ta fara waka da kuma matsalolin da suke ci mata tuwo a kwarya a harkar. Ta ce wahalar waka ta fi ta noma. TarihinkiAssalamu alakium, sunana Umma Muhammad Baba, amma an fi kira na da Ummi […]

Ummi Muhammad wacce aka fi sani da Ummi Nagarta ta shafe shekaru a harkar waka, ta yi bayanin yadda ta fara waka da kuma matsalolin da suke ci mata tuwo a kwarya a harkar. Ta ce wahalar waka ta fi ta noma.
Tarihinki
Assalamu alakium, sunana Umma Muhammad Baba, amma an fi kira na da Ummi Nagarta. An haife ni a karamar Hukumar Tarauni, Jihar Kano, a ranar 25 ga watan Agusta, 1988. Mahaifiyata daga kasar Sudan take, mahaifina kuma dan Katsina ne. Mahaifana sun shafe fiye da shekara 50 a Kano. Na yi makarantar share fagen shiga firamare da kuma makarantar firamare daga 1992 zuwa 1999. Na yi karamar sakandare a dan Zabuwa a Kano, inda na yi sakandare a Shekara duk a cikin Kano, daga nan sai na yi Difloma a kan Na’aurar Kwamfuta.
Yadda na fara waka
Na fara waka a shekarar 2006. Kodayake tun ina karama nake da sha’awar waka, musamman ma komai na gani sai na fara rera masa waka.
Wakokin da na yi
Wakar da ta fi fito da ni a duniya ita ce wadda na yi da Sadi Sidi Sharifai mai suna ‘Ibro Bakon Agadas’ a shekarar 2011 da kuma wakar ‘Ibro Nama Inna’ a shekarar 2014. Kafin wannan lokacin ana kira na da Ummi Shaba Mai Uwargida saboda tare muke waka, inda a shekarar 2010 sai na fara rera waka da Habibu Lafazi, wanda shi ya yi mini lakabin ‘Ummi Nagarta’. Na yi wakoki masu yawa.
Mawakan da nake koyi da su
Sadi Sidi Sharafai da kuma Maryam Muhammad Sale Fantimoti, sun ba ni gudunmuwa mai yawa a harkar wakata.
Rubutun waka
Ni nake rubuta wakokina.
Mayar da hankali kan wakar sarauta
Wakar sarauta da siyasa sun fi kawo kudi. Ina wakokin fim amma ba ni nake rubutawa ba. Wakokin sarauta da siyasa ni nake rubutawa.
Wakokin fina-finan da na yi
Wakar ‘Ibro Bakon Agadas’ da wakar ‘Gida daya’ da “Ibro Nama Inna’ da “Marainiya’ da ‘Yankan Baya’ da ‘kaddara da ‘Basaja’ da sauransu.
Burina
Burina shi ne sakon da nake isarwa ya amfanar da masu saurare na.
kalubale a harkar waka
Eh to, akwai ranar da na rubuta waka an yi mini kida amma lokacin da na shiga dakin rera waka (boice room) sai na manta sai bayan kwana biyu na yi wakar. Daga bangaren al’umma kuma idan an ji ke mawakiya ce sai ka ga suna yi mini wani irin kallo. Suna daukar mawaka kamar masu aikata wani zunubi, to ni kuma abin yana ba ni haushi domin waka baiwa ce, ta fi noma wahala.
Babbar kyauta ta hanyar waka
Na samu kyaututtuka ta dalilin waka, sirri ne a wajena, amma ko motar da nake hawa na same ta ne dalilin waka.